Abarba tana daga cikin ƴaƴan itacen da nake matuƙar jin daɗin tauna su, musamman idan na ci karo da mai zaƙi sosai. Ko jiya ma (a 2022 lokacin da na yi rubutun) da na zo wucewa ta kusa da wani mai abarba, sai da na tsaya ya yanka min wacce zan shiga gida da ita.
A lokacin da nake cin wannan ɗan itace mai matuƙar zaƙi da daɗi, abubuwa da dama ne ke yawo a raina, ɗaya daga cikin su shi ne da can, a ƙarni na 18, abarba alamace ta arziƙi, a ƙasashen turai musamman, farashin abarba an yi ƙiyasin yana kai $8000 a kuɗin yanzu (za mu iya cewa kimanin N12,000,000 a kuɗin Najeriya).
Masana tarihi sun ce har hayar ta ana iya ɗauka in za a yi wata hidima ta ƙasaita (party) in an gama kuma a ba wa wasu masu buƙatar ɗaukar haya, a haka har ta je hannun wanda zai iya siyanta ya ci. Ni kuwa gashi wacce aka yanka min ko $1 ba ta kai ba, kai ko rabin $1 ma.
Menene alaƙar labarin nan da taken rubutun?
An yi yawa
Meyasa abarba ta sauko haka da har kamata zai iya siya ya sha ba tare da wani taraddadi ba? Saboda ta yawaita ne, masana tattalin arziƙi na cewa duk abun da ya yi yawa, yana rasa darajarsa.
Abunda ya faru da samun aikin yi a dalilin karatun boko ke nan, shekarun baya ni ma na sani mutum yana gama sakandare zai samu aikin yi sai dai in ba ya so. Kafin wannan zamanin kuwa in kana da kwalin degree wani kallo ake maka na musamman, ku ne waɗanda ake ji da ku, babban albashi, gida da mota da direba, duk kuma gwamnati za ta kula maka da su.
Idan ana zancen aikin yi, mutane da dama suna ɗaukar cewa iya ƙasar nan ne matsalar, kuma saboda ƴan siyasa sun yi babakere ne akan komai, ba na musun hakan, amma batun aikin yi ya wuce ikon ƴan siyasa ko wasu masu riƙe da muƙaman gwamnati, matsala ce ta duniya gaba ɗaya.
Na taɓa jin Dr Ken Robinson yana cewa da can in ka gama makaranta sai dai in ba ka son yin aiki, saboda akwai aikin, yace amma yanzu masu masters suna gida suna buga video game. Wannan fa bature ne a ƙasar da muke ganin sun ci gaba (Amurka).
Me nake nufi da an yi yawa, ba wai mutanen duniya ne suka yi yawa ba, masu irin kwalin da kake da shi ne suka yawaita, irin ilimin da kake da shi ya yawaita, dabarar kasuwancin da ka iya ta zama ruwan dare, aikin hannu da ka iya da yawa sun koya sun ƙware, wannan shiyasa darajar komai take faɗuwa, dan haka kamar komai darajar masu kwali a hannu ta yi ƙasa warwas.
Mutanen Duniya sun nunnunku
Shekara 100 baya, ana ƙiyasin cewa mutanen duniya ba su haura biliyan biyu ba(2,000,000,000). Ba sai mun je da nisa ba, ka kwatanta ƴan Nijeriya a yanzu da ƙidayar da aka yi shekarar 2006, za ka ga yadda adadinmu ya ruɓanyu.
Ba wai yawan da mutanen suka yi ba ne matsalar kaɗai, duk mutanen hanya ɗaya suka ɗauka, ka je makaranta, ka gama da sakamako mai kyau, ka samu aikin yi da babban albashi. A shekarun baya wannan tunani ya kai ga nasara saboda kamfanunnuka da ma’aikatun da za su ba da aikin suna da yawan da suka wadaci mutanen.
Shi arziƙin Allah yana da faɗi, duk yawanmu ba mu isa mu ga ƙarshensa ba, amma in dukkanmu hankalinmu ya koma kan abu ɗaya dole za mu yi ta shan wahala, wasu su ci gaba da danne wasu. Tun mutane suna ganin aikin lauya da likitanci shi ne mafita, har sun haƙura sun fara cewa mai albarka suke nema.
Duniya ta sauya
A zamanin baya duk da akwai masana’antu masu yawa, za ka samu kuma masana’antun mutane suke buƙata wajen tafiyar da su. Shin wannan na nufin yanzu aljanu suke buƙata? Hahaha, ba lallai ba.
Abunda nake so na ce shi ne sauyawar zamani ya zo da abubuwa da dama, aikin da mutum 10 za su yi na’ura guda za ta yi. Mu ɗauki misalin banki, da kowa in yana buƙatar kuɗi sai ya shiga banki, ga waɗanda ke biya a zaune, sai ka bi layi ma wataƙila duk da yawansu. Amma yanzu da katin ATM ɗinka za ka tsaya ka yi uzurinka ba sai ka shiga bankin ba.
Duk da mu har yanzu da garma da fartanya muke noma, amma inda aka ci gaba akwai injinan duk da za su yi wannan aikin, mutum 1 ko 2 sun isa su sarrafasu. Akwai maganin da in ka fesa shi ma ba ka buƙatar a yi noman, yanzu abun ya kai matakin da har an fara noma a cikin ɗakin da bai kai ko rabin hekta ba.
Da sai ka tashi ka yi yawo ka tallata hajarka, daga ƙasa zuwa ƙasa, amma yanzu shafin facebook, ko whatsApp status zai kawo maka mai saye. Duk sauƙin da rayuwa ta ƙara yi sai wani ya rasa aikinsa.
Ko akwai mafita? A duk iya abubuwan da manazarta suke faɗa a matsayin mafita, ina ganin za a iya taƙaice su a kan abu 3. Neman sani kullum, tallata ƙwarewarka da kuma warware matsalolin mutane.
Kamar yadda na faɗa a baya, taskar Allah yawa gare ta, ba mu kaɗai ne a duniya ba, kuma duk ƙarƙashin ariziƙinSa muke, don haka munana zato ne gare Shi a yi tsammanin yawanmu zai sa wani ya rasa.
Tunda dai canji dole ne, to dole mu ma mu nemi sani kullum, sanin sabon abu kullum a fanninka zai kai ka duk inda ba ka yi tsammanin zuwa ba. Ba iya fanninka ba kaɗai, kana buƙatar ka san mutane da kuma abun da suke so da yadda suke so, don ka ba su abun da suke son a yadda suke so ɗin. Sai dai fa sani da ƙwarewa kaɗai ba sa isa, bayan an sani sai an nunawa mutane an sani, ta hanyar sanar da su, ko warware musu wata matsala tasu da wannan ilimin. Wannan ne kaɗai zai sa su ɗauki kuɗin da suka tara da guminsu su baka.
Wani abun ban sha’awa game da fasahar zamani shi ne a duk lokacin da wata hanya ta kulle a dalilin sabuwar fasaha sai ka ga wata ta buɗe. Ƙaramin misali shi ne yadda kasuwancin yanar gizo ya ke nema ya mamaye ko’ina, jama’a da yawa sun rasa aikinsu a dalilin zuwan yanar gizo, kamar yadda kuma zuwan nasa ya buɗe damarmaki ga mutanen da ba za su irgu ba, wasu ba don shi ba ma ba mamaki har su bar duniya ba za a san da zamansu ba.
Zan so na rufe wannan rubutun da wani abu guda ɗaya mai matuƙar muhimamanci, wato kaƙa (connection). Babu inda za ka je a duniya sai da ƙafa, idan na ce ƙafa ba na nufin kamar yadda yawancin mutane suke ɗaukarsa a matsayin ƙulla alaƙa da ƴan siyasa ko manya don a samu kwangila ko aikin yi, ba iya wannan ne connection ba, bai kuma kamata a taƙaita ma’anar a iya nan ba.
Ƙulla abota da abokan kirki waɗanda suka san ina suka dosa a rayuwa shi ne babbar ƙafa, kuma duk taimakon da mutum yake buƙata a duniya matuƙar ya samar wa kansa da ‘connections’ babu abun da ba zai samu ba, wani abokin ‘idea’ zai ba ka, wani jari zai sama maka, wani littafi zai ba ka ka karanta, wani wata matsalar zai warware maka, wani kasantuwarka a tare da shi zai ba ka ƙwarin gwiwa, da sauraran su. Don haka kada ka koma gefe ka yi ta ƙorafin rashin sanin manya ne yake daƙile ka, ka samar da naka manyan a kewaye da kai, kuma ka zage dantse ka zama babban da za a so a yi hulɗa da shi, sannan ka jure wurin rainon alaƙar.
Ko a nan na dakata ina sa ran mai karatu ya amfana sosai, idan haka ne kuwa me zai hana ka turawa koda mutum biyu ne cikin abokanka don suma su ƙaru. Mun gode.
Gaskiya na ƙaru sosai
Ma sha Allah, haka ake so
Allah ya kara basira
Amin summa amin, mun gode
Gaskiya mun ƙaru sosai, Allah ya saka da alkahairi
Madalla, amin summa amin
Masha Allah. Tunatarwa tana Amfanin Mimini.
Wannan Bayani Na Ilimine. Mungode
Madalla