Ba kasafai nake iya tuna abubuwan da na yi a yarinta ba kamar sauran mutane, ko da yake da yawa ma ba sa iya tunawa, sai dai wasu sukan samu masu ba su labari, wanda ni ban samu hakan ba.

Yawancin abubuwan da nake iya tunawa su ne waɗanda suka faru bayan na haura shekara 10. Nakan tuna lokacin da nake yawan zama a wani ɗaki da ba kowa a ciki ina haɗa wasan afto da basawa suna faɗa har da su faɗan ƙarshe (hahaha!).

Nakan iya tuna yadda nake zane-zane, karance-karancen littafan Hausa, musamman na yaƙi da ƙagaggun labarai. Haka nan nakan yi rubutu jifa-jifa, har watarana na yi azama na rubuta wani littafi da na kira “Gwarazan Sadaukai” lokacin ina aji 6 na firamare.

Bayan na shiga JSS sai kuma na fara son darasin lissafi a dalilin wata malama da muka a yi a JSS 2. Daga ta yi abu a aji da wuri nake ganewa, in ma ban gane ba in na je gida na yi bita sai na gano, a haka ya zama min jiki duk wani abu mai sarƙaƙiya ko wahalar ganewa sai ka ga ina ƙoƙarin kashe kaina a wurin gano shi (Allah ya taimake ni ma ba ni da juriya, da wuri nake sarewa, da yanzu na zama ɗan boko).

Zuwa lokacin da na shiga SS na gane cewa ina yawan saɓawa da mutane, abun da suka ba shi muhimmanci ba kasafai nake ba shi ba, abun da ke sa da yawa nishaɗi sai in dinga ganinsa shirme ne kawai. A lokacin kuma na gane ina son gwada abubuwa in na samu dama, misali wani lokaci da na binne ɓera ya dagargaje don kawai na ga ƙasusuwansa yadda aka koyar da mu a Biology. Haka wani lokaci da na lanƙwasa wani ƙarfe don na samar da abun da za a dinga tashin ɗalibai sallah da shi da Asuba ba tare da an komaɗa ƙarfen gadon da ake bugu ba. Haka na taɓa gano wani salo na lissafin da ya shafi rabawa ta hanya mai sauƙi.

Da na zo Jami’a, na samu kaina a rashin ɗaukar komai da muhimmanci, a raina ina jin wai meyasa muke yin waɗannan abubuwan (kar ku fahimce ni a baibai, ina zama na koya in an koyar, har ma nakan iya koya wa wasu). A wannan lokacin na rasa abun da ake kira “Focus”, wata mayar ko tsayar da hankali kan abu. A haka dai na lallaɓa na gama makarantar, ina gamawa kuwa ciwon damuwa (depression) ya ce da wa Allah ya gama shi in ba da ni ba.

Ina yawan samun tambaya daga mutanen da suka karanta littafin “Ka San Kanka” kan yadda za su gano baiwarsu bayan sun san kansu. Wannan rubutun na irin waɗannan mutanen ne. Idan ba ka rigaya ka san kanka ba, za ka iya sauƙe littafin “Ka San Kanka” don farawa da shi kafin wannan ta hanyar dannan shuɗin rubutun da ke jikin sunan littafin.

Me kake yi a yarinta?

Na kira taken rubutun da yadda za ka gano baiwarka amma na ɓuge da ba ku wannan labarin mai gundura, ku ɗan yi min hanzari, ga inda nake son mu iso. Hanya mafi sauƙi ta gano baiwarka ita ce ka san me kake yi lokacin da kana yaro. Lokacin yarinta babu tunanin komai a kan mutum, ba nauyin kowa a kanka, ba tunanin neman kuɗi, ba tunanin me abokanka suke yi a dandalin sada zumunta, ba tunanin in ka faɗi jarrabawa akwai wata matsala, komai kana yinsa ne don ya dace da kai. Don haka akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin abun da kake kana yaro da irin zubin halittarka.

Ba iya abubuwan da ka yi a yarinta ba kaɗai, duk wani abu da kake yi da yake yi maka sauƙi, sauran mutane kuma yana ba su wahala za ka iya sa shi ƙarƙashin wannan tambayar, domin kuwa an huwace masa yin wasu abubuwa cikin sauƙi ko da abubuwan na da wahala.

Meyasa kake yi?

Abu na biyu, ba iya abun da kake yi za ka kalla ba, nau’in aikin za ka kalla. Abun da nake nufi da nau’in aiki shi ne, ba lallai abu ɗaya kake yi ba, amma za ka samu akwai alaƙa tsakaninsu. Misali ni da nake haɗa wasanni, zane da rubutu, ƙoƙarin warware matsala ko gano wani abu da ya shiga duhu, na gane alaƙar abubuwan shi ne baiwar ƙirƙira, idan da na samu horo sosai da wataƙila yanzu na ƙirƙiro muku injin hana jin sanyi (lol). To, ba lallai sai na haɗa wani babban abu ba ma fa, domin shi kansa rubutu samar da ma’ana ta hanyar amfani da haruffa, wanda shi ma ƙirƙira ne.

A ina kake yanzu?

Wani abu mai muhimmanci shi ne sanin a ina kake yanzu da kuma me kake yi. Abun da ya sa wannan yake da muhimmanci shi ne, ka riga da ka girma, wataƙila ma da iyali a kanka, matsawa kanka sai ka gano baiwarka ta yarinta don ka rayu da ita zai iya illata ka. Gwagwarmayar da ka yi a rayuwa tana da muhimmanci a wannan gaɓar, duk inda ka samu kanka akwai ta inda za ka ci moriyar baiwarka ko kai ba ka ci ba, wasu za su ci ta hanyar amfani da kai.

Akwai abun da nake yanke ban faɗa muku ba a labarina, shi ne koyarwa. Na yi koyarwa a Islamiyya da boko, sannan ina koyar da ɗalibai ƴan uwana idan na riga su koyon abu. Bayan na gama makaranta ma dai aikin koyarwa na samu. Don haka me zan yi da ya wuce koyarwa? Baiwawwakin da nake tunanin ina da su fa? Wasu na watsar, wasu kuma ina amfani da su har yanzu, yayin da wasu kuma yanzu nake horar da kaina don na ƙware a kansu, domin ko da ka gane baiwarka, sai ka yi haƙuri ka raine ta. Abun da na yi shi ne, na ci gaba da koyar da mutane a rubuce, sannan duk abun da zai ba ni damar samar ko gano wani abu ina yinsa gwargwadon buƙata, kai ma za ka iya hakan.

Ya zan yi da hidindimun yau da gobe?

Wani zai ce shi fa yanzu ba gano baiwarsa ba ce matsalarsa, ko da ya gano baiwar ba za ta ba shi abun masarufi ba, ina amfanin gano ta gare shi? Mai wannan tunanin yana da gaskiya duba da halin da yake ciki. Gano baiwa ba don a ci tuwo ba ne kaɗai, tunanin tuwo yana daga abun da yake hana mu ci gaba, za ka ga mutum mai himma da ƙwazo a wani wuri amma ya saki saboda neman na masara.

A ƙarshen labarina na ambaci ciwon damuwa, cikin hasashen da na yi yankewar alaƙa tsakanin abun da nake yi a lokacin, da wanda yakamata a ce nake yi, ya taka rawa, idan da karatun ya taimake ni wajen cin moriyar baiwata da wataƙila ban shiga halin ba (ba lallai kuma hasashen ya zama daidai ba, domin ina da abokin da shi kuma wannan yankewar alaƙar ne ya zaburar da shi ya koyi wasu abubuwan da yanzu yake cin gajiyarsu).

Za ka iya yin wata sana’a a gefe kuma kana neman hanyar gano baiwarka. Idan ka gano baiwar sai ka duba ta ina mutane suke cin abinci da baiwarsu, sai kai ma ka jarraba, idan Allah ya maka nasibi da wuri za ta haɓaka har ta zama ita ce ma sana’arka. Ku fahimce ni, ba ina nufin a gano baiwa don a ci abinci ba ne, sai dai ga wanda iya wannan baiwar ce zai ci abinci da ita ba laifi don ya mayar da ita sana’arsa, hakan zai kuma sauƙaƙa lamurra da yawa na rayuwa. Ko ni da ba ni da inda nake samun abun rufin asiri, da ba zan ba wannan aikin muhimmanci da nake ba shi yanzu ba, domin ina da iyalin da suka dogara da ni. Shiyasa yake da muhimmanci ka farka da wuri a rayuwa a matsayinka na matashi, don samun sauƙin cimma nasara.

Rubtun yana son yin tsayi sosai, na so a ce mun tattauna yadda za ka koma kan hanyar amfani da baiwarka bayan ka gano ta, amma zan ajje wannan sai wani lokacin. Kamar yadda na faɗa a farko, yana da kyau ka fara da littafin “Ka San Kanka” kafin wannan, domin shi sanin kan zai nuna maka kai wane ne, irin raunin da wataƙila kake da shi da zai iya ba ka cikas, da kuma ƙarfin da kake da shi da zai tallafi baiwar, ko ya sauƙaƙa maka wajen amfani da ita.

Zan so na ji ra’ayoyinku kan wannan batu kafin na yi na gabansa. Idan ba za ku iya tsokaci a nan ba, ga alamar Whatsapp a gefen dama na wannan shafin, ku danna shi don bar mana saƙo. Mun gode.