“Ɗabi’a ce mai matuƙar kyau mu dinga lura da yadda mutane suke ɗaukarmu. Wannan ba wani abu ba ne a game da mutum. Muna son jin mu kusa da mutane kuma muna damuwa da halin da suke ciki, a bisa wannan dalilin muke lura da yadda suke tunani game da mu da kuma yadda alaƙarmu take da su”. Therapist Charlotte Howard
Lallai damuwa kan yadda mutane suke kallonmu yana da matuƙar muhimmanci. Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata gare shi ya faɗa a wani hadisi cewa “wanda ba ya jin kunyar mutane ya aikata duk abun da ya so” Haka nan a wani wurin ya ce “zunubi shi ne abun da ke kai kawo a zuci, kuma kake jin tsoron kar mutane su farga da abun da kake yi”. Sai dai wannan fa ba ya nuna mu canja rayuwarmu don mu saje da kowa.
A matsayinmu na mutane ko shakka babu muna buƙatar mu rayu da wasu mutanen, a saboda haka dole ne mu dinga ba da muhimmanci kan yadda suke kallonmu. Duk da cewa damuwa da yadda mutane suke kallonmu ba wani abu ba ne, yana zama haɗari a duk lokacin da hakan ya zama mana abun damuwa, zullumi da fargaba.
Da wuya ace har yanzu mutanen unguwarku suna iya tuna cewa shekaran jiya kayan da ka sa babu guga. Ba mamaki abokanka sun daɗe da manta cewa ɗazu ma sai da ka manta hularka a wurin da ka yi alwala. Duk da haka za ka samu mutum yana ci gaba da damuwa kan ire-iren waɗannan abubuwan da mutane sun daɗe da mantawa da su.
Babu riba a cikin yin watsi da mai mutane suke tunani a kanmu, ko dinga nuna halin ko in kula kamar ma ba mu san suna yi ba, alhalin wannan ba gaskiya ba ne, mun san suna yi. Amma akwai hanyoyin da za mu bi da za su rage mana yawan zullumin da muke shiga a dalilin tunanin me mutane suke tunani game da mu.
Alamomin da suke nuna mun damu sosai da yadda ake ganinmu
Waɗannan alamomin za su fayyace maka ko damuwa da mai mutane za su ce a kanka yana iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwarka ko kuma ba ya iya shafa
· Saurin canjawa daga an caccakeka, ko daga ina kushen yake, kuma ko ma waye ya yi shi yana sa ka ka sauƙa daga ra’ayinka.
· Ba ka iya cewa a’a, komai aka faɗa bi kake da “to” da “e”.
· Kwanciyar hankalinka ya ta’allaƙa da yadda sauran mutane suka karɓeka.
· Kana nacewa yin komai ɗari-bisa-ɗari.
· Ba ka jan layi a rayuwarka, kowacce shara kana maraba da ita.
· Kana ba wa mutane damar yanke maka yadda ya kamata ka yi da rayuwarka
· Ba wuya ka bayar da haƙuri ko da ba ka yi komai ba
· Idan ra’ayinka ya saɓa da na sauran, kana tsoron bayyana naka.
Ta ya za ka daina damuwa da yadda ake ɗaukarka?
Idan kana son daina damuwa da yadda mutane suke kallonka ga wasu abubuwa da ya kamata ka yi la’akari da su:
Ka tsammaci, kuma ka yarda cewa mutane za su samar da wani ra’ayi game da kai
Kada ka ɓatawa kanka lokaci wajen tunanin za ka iya tsira daga yadda mutane za su kalle ka ko su fassara ka. Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Duk yadda kake, duk yadda ka so, duk iya ƙoƙarinka dole ne yadda mutane suke kallonka ya sha bamban, kuma za su ɗauru a kan wani ra’ayi game da kai, gaskiya ne ko ƙarya ba ruwansu. Sani da tuna wannan zai taimake ka wajen daina damuwa da su.
Ka tuna cewa duk mutum tara yake
Tunda abu ne mayuwaci a cimma, tsammanin komai ɗari-bisa-ɗari ba shi da wani amfani. Ka gane cewa kowa yana kuskure, ba kanka farau ba. duk wanda ya tsangwameka kan wani kuskure naka to fa shi ma yana da nasa.
Kusakurai a rayuwa suna da matuƙar amfani ga mai ɗaukan izna da su, sukan zama wa mutum wani ilimi da zai yi amfani da shi a gaba don kaiwa gaci. Don haka ka ɗauki kura-kuranka a matsayin wani darasi, sannan ka sa a ranka wannan shi ne ya mayar da kai mutum.
Mahaifina ya taɓa ba ni wannan shawarar lokacin da ya lura ina ta faman damuwa kan ƙananan kusakuran da zan iya gyara su ko da ba cif-cif kamar yadda nake son yi ba.
Ka kewaye kanka da masu ƙaunar ci gabanka
Zama da mutanen da kullum suke yanke hukunci tare da munana zato ga abubuwan da kake yi yana da matuƙar cutarwa ga rayuwa ko da kuwa ƴan gidanku ne.
A ɗaya hannun kuwa kewaye kai da mutanen da suke ƙarfafa maka gwiwa, suke mara maka baya, suke ɗaura ka a kan hanya, suke taya ka murna, zai taimakeka wajen yin rayuwa mai kyau ba tare da wani zullumi ba. saboda haka sai ka nemi irin waɗannan mutanen ka ƙulla alaƙa da su.
Ka lura da inda maganar ta fito
Ba kowanne kare ne in ya yi haushi ake tsayawa waiwaye ba, balle har a kai ga an jefe shi. Idan iyaye ko malami ko wani shugabanka ya faɗi wani abu game da kai yana da kyau ka tsaya ka ba wa abun muhimmanci don ka gano kuskurenka ka gyara in akwai. Amma haka kawai don wani ɗan unguwa yace kana da girman kai ko ba ka murmushi ban ga dalilin da zai sa wannan ya dame ka ba.
Ka daina ƙoƙarin karanta tunanin mutane
Ba ma fa koyaushe ne mutane suke faɗan wani abu mummuna game da mutum ba. wani lokacin shi mutumin ne kawai yake ƙirƙirarwa kansa tunanin wane da wane kallo kaza suke min. Bincike ya bayyana cewa yawancin lokuta mune muke ɗaukar ana mana wani kallo, alhalin jama’ar su ma sha’anin gabansu ne ya dame su.
Ka fahimci kanka, kuma ka rayu da izza
Rashin sanin kai da ƙin karɓar kai a yadda aka halicci mutum ya kan jefa shi cikin haɗarin ƙin kansa. Wanda ba ya son kansa ba ya girmama kansa. Don haka komai aka faɗa game da shi sai ya ji ya dame shi.
Rayuwa cikin izza tana hana maƙiya taɓuka komai, duk yadda suka so su jefeka da wani abu da zai raunata maka tunani ba sa samun dama. Cikakkiyar izza kuwa tana samuwa ga wanda yake rayuwa a matsayin shi ba a matsayin waninsa ba. Sanin kai da abubuwan da ka yi imani da su da yadda kake so ka rayu zai iya ba ka wannan izzar.
Ka shaglatar da kanka
Yawancin mutanen da suka fi afkawa cikin damuwa da me ake cewa game da su su ne masu yawan samun rarar lokaci. Wanda ya shagaltar da kansa da wasu abubuwan ba lallai ma ya san me yake faruwa ba balle har ya damu.
Idan ka je aiki ko kasuwa ka dawo ba ka da wani abun yi, za ka iya zama ka yi karatu, ko shiga wani aikin sa kai a unguwa kamar koyar da yara. Ba iya wannan ba, zama da wanda taku ta zo ɗaya ma zai iya mantar da kai halin da sauran mutane suke ciki game da kai. Haka nan zama ka ƙarasa wani aiki da ka gagara ƙarasa shi, ko ma samarwa kanka da wani abu na nishaɗi da zai dinga shagaltar da kai, kamar wasanni, zane-zane, bincike, da sauransu.
Ka nisanci magulmata
Hanya ɗaya tilo mafi sauƙi kuma ta kaucewa a dinga yawan gulmarka shi ne ka nisanci zama da magulmata. Su irin waɗannan mutanen duk yadda suka so su nuna maka su masu ƙaunarka ne, ko su ba ruwansu, ƙarya suke, kullum ransu a ɓace yake, zuciyarsu cike take da ƙunci da mummunan fata ga jama’a. Ba za su taɓa jin daɗin rayuwarsu ba sai suna yaɗa gulma da jita-jita.
Wanda ba ya so a dinga yi da shi sai ya canja abokansa, ya samu mutanen da suke da inda suka nufa a rayuwa ya mayar da su abokanan hulɗarsa. Yin abota da magulmata ba ya taɓa haifar da ɗa mai ido, kuma yana da illa ga lafiyar tunani da ta jiki.
Wasu ƙarin shawarwari
· Ka daina haɗa kanka da kowa
· Ka mayar da hankali kan inganta rayuwarka
· Ka gane cewa ba ka da iko kan ra’ayinsu game da kai
· Waɗanda ba sa ƙaunarka ba za su taɓa baka goyon baya ba
· Ka gane bambancin girman kai da girmama kai
· Ka zama kana da ayyananniiyar manufa, tsari da dokokin da ba a keta maka
· Ka karɓi kanka a yadda kake
· Ka mayar da hankali kan irin baiwar da Allah ya maka da bai ba wa wasu ba.
Ina fatan ku samu amfani cikin wannan saƙon. Allah ya datar da mu.
Don ƙarin bayani:
https://www.wikihow.com/Deal-With-Gossip
https://psychcentral.com/blog/mental-shifts-to-stop-caring-what-people-think-of-you
Jazakallahu khairan, Allah ya ƙara ɗaukaka.
Amin summa amin