A da can duniya ta kasance ba kamar yadda muke ganinta a yanzu ba. Misali idan za ka tura saƙon gayyatar aure ko sanar da haihuwa ko rasuwa daga gari zuwa gari sai ka tanadi abun hawa, guzuri da kuma lokaci. Ko kuma in kana da hali ka tada manzo ya kai saƙon a rubuce a takarda.

Da bayyanar wayoyin hannu a shekarar 1973/1979 aka samu sauƙin wannan lamarin. Yanzu kowanne saƙo kake so ka aika da buga waya ɗaya bukatarka za ta biya. Ba wannan kaɗai ba ma, za ku iya hira da mutum kai tsaye yana kallonka kana kallonsa ba tare da kowannenku ya bar garin da yake ba.

Kowanne ci gaba da duniya ta samu ya kan zo da abubuwa da dama, wasu abubuwan suna sauƙaƙa mana rayuwa, wasu kuma suna mai da ita mai tsanani. Akwai abubuwan da kuma tsabar jin daɗinsu da muke ne ya sa suke mana illa ba tare da mun ankare ba.

Idan za ka tambayi ɗan shaye-shaye me yake ji a cikin kayen mayensa zai faɗa maka cewa damuwarsa tana yayewa, yana jinsa a sama, ya fi yin tunani da kyau, da sauransu. Amma bayan wani lokaci in za ka sake masa wannan tambayar zai ce da kai wannan jarrabawa ce, ya rasa yadda zai yi ya daina.

Kamar yadda kayan maye suke shiga rai (addiction), mutum ya zama ya kasa rabuwa da su duk yadda ya so sai an yi da gaske, duk da yana ji yana gani cutar da shi suke, haka wayoyin hannunmu suke, dan haka ma na ba wa rubutun wannan taken.

Ka da ka ɗauka wai haka kawai wayoyi suke da shiga rai, masana sun bayyana cewa dama an ƙirƙire su ne don su shiga rai. Ya abun yake?

Tristan Harris wani tsohon injiniya ne a kamfanin Google, a wata hira da aka yi da shi a shirin Real Time na HBO ya bayyana yadda ake ƙiƙirar sabuwar fasaha don mutane su shaƙu da ita inda ya ce:

“Akwai wata magana da ake cewa wai fasaha ba ta da tsagi (ba ta cutarwa ba ta amfanarwa) ya rage mu zaɓi yadda muke so mu yi amfani da ita. Wannan magana ba gaskiya ba ce… fasaha ba tsaka-tsaki ba ce, suna so (masu ƙirƙirar) mu yi amfani da ita ta wata hanya ne keɓantacciya na tsawon wani adadi na lokaci. Domin ta haka ne kaɗai suke samun kudi” Cal Newport ya kawo wannan a littafin Digital minimalism. Kuma wannan dalilin ya sa ake kiran masu ƙirƙirar sabbin fasahohi musamman na dandalin sada zumunta da sunan manoman taba a T-shirt.

Mu yi tunani a kan wannan, me muke buƙatar yi a dandalin sada zumunta? Bai wuce mu samu bayanai ba. To sai ya zama akwai damar in ka yi rubutu a danna “like”, akwai damar abokananka su dinga yaɗa yadda rayuwarsu take gudana, akwai damar yaɗa hotuna, akwai damar ka bayyana ra’ayinka kan abun da wani ya rubuta (duk wannan fa ba kuskure ba ne da manufar samar da waɗannan damammakin).

Masana suna cewa mutum ba zai iya rayuwa haka kawai ba, sai da mutane, don haka duk lokacin da ya samu damar sanin halin da abokanansa suke ciki bai san lokacin da yake manta kansa ba. Abun shi ne idan a misali ka hau shafin fesbuk don duba wani bayani, sai kaga hotunan abokanka sun ci kwalliya, ko suna wajen wani taro suna cin abinci, ko suna wajen wani shaƙatawa, ko suna cikin manyan mutane, ba ka san lokacin da za ka shagaltu da bin hotunan ɗaya bayan ɗaya ba kana dubawa. Kai da ka zo duba saƙon minti guda, sai ka shafe minti ashirin (20) ba ka ma sani ba tsakanin kallon hotuna da karanta rubutu da karanta tsokaci.

Wani zai ce har yanzu bai ga alaƙar wannan da shaye-shaye ba, ka bi ni a sannu-sannu za mu isa wurin.

A lokacin da ɗan shaye-shaye yake shan kayan mayensa, akwai wani sinadari da ake kira “dopamine” da yake sauƙa a cikin ƙwaƙwalwa, shi wannan sinadarin shi ne yake da alaƙa da farin ciki/nishaɗi. Ma’ana in ya sha karon farko wannan sinadarin zai sauƙa daga ƙwaƙwalwarsa don haka sai ya ji shi a sama, farin ciki marar misaltuwa ya baibaye shi. A ɗabi’a mutum ba ya son rabuwa da farin ciki don haka anjima daga ya ji yanayinsa ya sauya sai ya sake shan wancen abun da ya sha ɗin don dawo da wancen tsohon yanayin na farin ciki.

Ba iya shaye-shaye ba kaɗai, komai da muke yi da yake sa mu farin ciki yana iya sauƙar da wannan sinadarin, kuma shi wannan sinadarin da gwargwadon yadda yake yawan sauƙa, da gwargwadon yadda abin da ke sa shi sauƙan yake kasa masa. Misali, in taba sigari kara ɗaya ta sauke shi da safe, to da yamma zai buƙaci kara ɗaya da rabi kafin mashayin ya ji daidai, wannan ya sa shaƙuwa tsakanin mashayi da abun shansa yake zama na wuce hankali.

Idan ka yi rubutu ko ka ɗaura hoto a Fesbuk ko Instagram, iya adadin likes da tsokaci masu daɗi da aka yi iya adadin farin cikinka saboda dalilai biyu, na farko za ka ji daɗi mutane sun gamsu da abin da ka faɗa, na biyu za ka fara kallonka kanka a matsayin wani mutum na musamman da ya kai a idon tsarekunsa. Don haka gobe ma za ka so ka samu kanka a irin wannan yanayin. Ana nan ana nan sai ka shaƙu da aikata wannan aikin da yake kawo maka jin daɗin a shafin fesbuk (ya danganta da niyyar mutum fa, ba kowa ne yake rubutu ko ɗaura hoto dan likes ba). Wannan fa shi ne ke yin rubutun, me kake tunanin mai karatu zai kasance?

Idan kallon youtube ko netflix kake, ko labarin wasanni kake bibiya, ko labaran abubuwan da ke faruwa a ƙasa, ko ma kai ba ruwanka da internet fina-finai kake turawa ka yi ta kallo, ko “game” kake bugawa, duk matsalar dai guda ce, dole sai ka samu shaƙuwa da wannan aikin da kake yi saboda yadda yake sa ka ji a ranka wanda hakan zai iya mayar da kai tamkar ɗan shaye-shaye in tafiya ta yi tafiya. Za ka ji in ba ka yi wannan abun ba ka rasa sukuni kwata-kwata.

A wannan gaɓar zan so na yi wani ɗan tsokaci, ba kowanne irin amfani da waya ba ne ake ɗaukarsa a matsayin shaƙuwa mai haɗari. Masana suna bayyana wasu alamomi da mutum zai gane shaƙuwar da ke tsakaninsa da waya daidai yake da shaye-shaye ko kuwa.

A wani bincike da shafin pyschguides.com suka wallafa sun bayyana cewa kashi 67% na waɗanda suka mallaki wayar hannu, sun yarda cewa suna duba wayarsu su gani ko da wani sabon kira ko saƙo ba tare da wayar ta yi ƙara (ringing) ko vibration ba. Wannan suka ce yana daga cikin babbar alamar da take nuna akwai matsala. Daga nan kuma suka lissafo sauran alamomin kamar haka:

  •     Buƙatuwa zuwa ga amfani da wayar yana ƙaruwa kullum
  •     Duk yadda aka so a rage amfani da waya haƙar ba ta cimma ruwa
  •     Nutsewa a duniyar danna waya
  •     Komawa ga danna waya duk lokacin da aka shiga damuwa ko aka ji ba a jin daɗin komai
  •     Ba a gane yadda lokaci yake tafiya a yayin amfani da ita
  •     Buƙatuwa zuwa ga sabbin wayoyi ko sabbin apps kodayaushe
  •     Idan ba waya a kusa ko ba caji ko ba “network” ko “data” sai a tsinci kai a cikin fushi da ɓacin rai, damuwa, fargaba, matsi, tashin hankali da kasa zama wuri guda.

Ana alaƙanta shaƙuwa da wayoyin hannu da wasu abubuwa da na riga da na yi bayaninsu a baya. Abubuwan su ne:

  •     Tsoron ko jin cewa ana yi ba kai, ko wani abu zai wuce ka
  •     Son sanin abubuwa da yawa na ilimi ta hanyar bibiyar saƙonnin masu ilimin, ko labarai na wasanni ko na halin da duniya take ciki
  •     Kallace-kallen batsa, “games”, wasannin caca, da sauransu
  •     Ƙulla alaƙa ta soyayya a shafukan sada zumunta ko ma ƙullawa a zahiri amma hirar a kan yanar gizo

Ban so rubutun ya yi tsayi sosai ba, ina ganin ya kamata na samu gaɓar dakatawa. Kafin nan, idan mun lura da bayanan da suka gabata, shaƙuwa za mu iya cewa kala biyu ce akwai mai kyau akwai marar kyau. Wanda zuciyarsa take ta’allaƙe da masallaci alama ce ta shaƙuwa, amma kuma a bar so ce, don haka kafin ka yanke hukunci kan irin shaƙuwarka da wayar hannunka ka fara tambayar kanka me kake yi?

Idan ya bayyana gare ka shaƙuwarka ba ta kai ka inda kake son zuwa to ya kamata ka canza salonka. Idan ya bayyana gare ka shaƙuwarka da wayar hannu tana cutar da lafiyar jikinka da ta tunaninka ya kamata ka san na yi. Idan ya bayyana gare ka shaƙuwa da wayar hannu yana hana ka ƙulla alaƙa da mutane a zahiri ya kamata ka fara taka-tsantsan. Idan himmarka a wurin aiki ko a rayuwarka gaba ɗaya tana raguwa a dalilin shaƙuwa da wayar hannu ya kamata ka yi karatun ta nutsu.

Ko da ilimi kake samu, ko kuɗi, ko wani amfani na daban kake samu, ka dinga tambayar kanka, shin lokacin da nake ɓatawa dan na samu wannan abun ya cancanci abun? Ba zan iya samun abun a wani farashin lokaci mai sauƙi ba sama da wannan? Abun da ya sa yake da matuƙar muhimmanci a dinga duba farashi shi ne, mutum zai iya ruɗuwa da cewar ai abu mai amfani yake yi ba tare da la’akari da yadda lokacinsa yake wucewa ba a ɗan amfanin da bai taka-kara ya karya ba.

Akwai illoli da yawa na shaƙuwa ko da ban lissafo su ba ka dubi rayuwar ɗan shaye-shaye ka gani, illolin za su iya zama iri ɗaya, wataƙila in ma da bambanci bai wuce tsafta ba. Fargaba, damuwa, kasa bacci ko rasin samun sa a wadace, rasa sukuni, illa ga ido, kasa tsayar da hankali wuri guda, jin kaɗaici, rashin nutsuwa, rashin iya hassala komai, rashin sanin ina aka sa a gaba a rayuwa su ne illolin a dunƙule.

Ko akwai mafita? A duk abubuwan da ake lissafawa a matsayin mafita daga ƙarshe za ka ga sun tuƙe ne kan rage amfani da wayar. A gani na mutum ya duba ta ina ta sa cutar ta samo asali sai ya yi aiki a kan wannan ɓangaren. Idan likes da comments ne damuwarka za ka iya neman wani abu a zahiri da zai ba ka irin wannan jin daɗin, idan kallo ne ka gane cewa sana’a suke yi, kuɗi suke samu kai kuma asara kake yi, in soyayya ce ka tuna haɗarin da kake shiga ya fi na jin daɗin da kake samu, in neman ilimi ne ka gane cewa aiki da ilimin ya fi tara shi ba aiki muhimmanci, wanda yake wuni danna waya kuwa dole aikinsa zai zama kaɗan, idan kana tsoron abokanka za su yi wani abu ba kai, ka tuna haɗarin bibiyarsu da yadda hakan zai iya kai ka ga yi musu hassada ko kishi ko jin haushin su ko haushin kanka, idan labaran duniya ne suke ruɗarka ka tuna cewa yawancin labaran da ƴan jarida suke yaɗawa munanan labarai ne, ko su kaɗai aka bar ka da su sun isa su illata lafiyarka.

Wasu suna ba da shawarar ka samar da wani abu da zai dinga tursasaka ƙin yin amfani da wayar, misali ka cika lokacinka da abubuwan da ba za su bari ka samu rarar lokaci ba, ko ka sa wa kanka wani haraji duk lokacin da ka wuce iyaka a amfani da waya, za ka iya sa wa kanka tara ta kuɗi misali, ka samu wanda za ka ba wa kuɗin ku yi magana, in ka yi awa kaza a waya za ka ba shi kaza (hahahaha). Za ka iya gwadawa don kowa akwai kiwon da yake karɓarsa.

Ni kai na marubucin ba tsira na yi ba, domin nima mutum ne kamar kowa, a ƙoƙari na na ganin na yi rayuwa mai inganici ne ba tare da wayar hannuna ta hana ni rawar gaban hantsi ba na ci karo da waɗannan bayanan, dan haka in kun amfana sai ku haɗa da ni a cikin addu’o’inku. Nagode.