Idan da za ka tara mutum 10 da rayuwarsu ba ta tafiya yadda yakamata, da wuya ace 7 ko 8 ba su ba ka uzuri irin wannan ba; gwamanti ta ƙi taimaka mana, ƴan siyasa sun lalata ƙasar, dangi ba sa taimako, ba wanda ya ba ni jari, ina da dabaru da yawa amma Ƙasar ce sai a hankali, a Najeriya shirme ne ya fi cin kasuwa, ƴan kudu ne suke hana mu samun damarmaki, Hausawa akwai hassada ba sa son wani nasu ya samu, da sauran ire-iren waɗannan uzurori.

Shakka babu yawancin waɗannan abubuwan da mutane suke hujja da su wajen kare gazawarsu gaskiya ne, waɗannan abubuwan suna taka rawa sosai wajen rugujewar rayuwar matasa da dama. Sai dai in da gizo ke saƙar shi ne, irin wannan ƙorafin ba ya taɓa taimakon mutum a rayuwa. Wanda yake zargin cewa talaucin iyayensa ne ya sa yake cikin matsi yanzu ta ina hakan zai taimake shi?

Shi ƙorafi ba ya canja komai, kuma shi ne hanya mafi sauƙi ta ruguza rayuwa. Idan misali an haife ka a gidan talauci, a tunaninka awa nawa za ka ɗauka kana kuka ko kana ƙorafi ko kana tattauna abun don Allah ya canja ma iyaye? A tunaninka awa nawa za ka yi kana zargin masu mulki don ka samu sauyi?

Kuka da ƙorafi ba su taɓa kawo mafita ga mutum ba, duk wanda yake son rayuwarsa ta canja sai ya yarda shi ne matsalar kansa, kuma shi zai magance wa kansa matsalarsa da kansa. Misali, wanda yake zana jarrabawar lissafi aka ce ya nemo “x”, yana tsayawa jiran wani ya zo ya nemo masa ko yana ɗaukar alhakin nemowa da kansa. Akwai abubuwa da yawa da muke yi don samawa kanmu mafita a lokacin da muka shiga wani hali, kuma tabbas ƙorafi ba ya ciki. Bari in ba ku misali.

Lokacin da wuta ta lalace, tsakani da Allah wuni muke muna zagin shuwagabannin arewa har wayoyinmu suka mutu muka ajje su gefe? Ko kuwa kai wayar wajen caji muke cike da takaicin halin da aka jefa mu? Na tabbata waɗanda ba su nemi wurin kai wayoyinsu caji ba su ne yan kaɗan, ke nan mun san cewa ba ƙorafin ba ne mafita, tashi mu yi abun da zai fisshe mu ni mafitarmu.

Lokacin da farashin man fetur yake ta ƙara hauhawa, a ina muka nemi mafita? Ƙorafi da zagin shuwagabanni? Ko kuwa mun haɗa da yin tafiya a ƙafa, ajje motocinmu, siyan ababen hawa masu amfani da caji da sanya solar a gidaje da shagunanmu? Tabbas a cikin tashi tsaye muka samu mafita.

Lokacin da ya bayyana gare mu lallai in shugaban ƙasa ya ci gaba da mulki a 2015 kowa zai iya zama ɗan gudun hijira a arewa, ƙorafi muka yi ta yi a dandali har Allah ya kawar da shi ko kuwa haɗa kai aka yi manyanmu da ƙanana don samar wa kai da mafita? Ko shakka babu tashi tsaye aka yi da gaske har sai da aka kai shi ƙasa da ikon Allah (Duk da dai da alama ba a samu abun da ake nema ba, amma ɓangaren aikin nake so a kalla). Haka muke tashi tsaye a wurare da dama don nemawa kanmu mafita a ɓangaren lafiya, ilimi, da sauransu. Akwai misalai da yawa amma zan dakata a nan.

Babban maƙasudin yin wannan rubutun shi ne don zaburar da kawunanmu kan neman mafita a duk halin da muka tsinci kanmu. Misali wanda ya gama makaranta bai samu aiki ba, zai dawwama yana ƙorafi kan bai san kowa ba ne ko an hana shi jari a gida? Ko kuwa zai tashi tsaye a inda yake ya duba abun da ya ga zai iya ya shiga ciki gadan-gadan. Wasu mutane saboda tunanin cewa tunda matsalar ba daga su ba ne, ba hakkinsu ba ne su nemi mafita ya sa har suna ganin cewa ɓata lokaci ne yin karatun, da sun sani ma sana’a suka runguma tun farko, hmmm da gaske?!!!

Ilimi asalinsa haske ne, amfaninsa ya haska ma hanya a inda ka sa gaba a rayuwa, ilimi arziƙi ne mai zaman kansa, ba shi da alaƙa da tara dukiya. Wanda yake son samun kuɗi bayan ya yi karatu abu biyu zai yi, ya nemi ilimin samun kuɗi, sannan ya yi aiki wurjanjan wajen samun kuɗin. Ilimi samun kuɗi kuwa ba kamar karatun aji ba ne, an fi samunsa a mu’amala ta yau da gobe, da gwadawa da yi kullum.

Idan mutum bai da abun yi, awannin da yake ɓatawa wajen zaman gulma da zagin shuwagabanni da zargin iyaye, yan’uwa da abokai, sun ishe shi ya koyi sana’ar hannu.

Idan ma’aikaci albashinsa ba ya wadatar da shi, ba ha’inci zai sa a cikin aikin ba, a’a lokutan da ake ɓatawa a hirar ofis, da zaman majalisa bayan an koma gida, zai yi amfani da su wajen gina wata harkar da za ta ba shi taro da sisi.

Idan matashi ya rasa jari, ba ƙorafi ba ne mafitarsa, mafitarsa tana cikin yin amfani da basirarsa wajen nemo jarin, ko kuma ya kama aikin hannun da ba ya buƙatar wani babban jari. Misali mutum ya koyi wani “digital skill online”, sai ya shiga cikin mutanen da suke samun kuɗi da abun don shi ma ya koyi yadda ake samun kuɗi da shi. In ba zai iya na online ba, ga sana’o’in hannu da yawa da zai iya zuwa ya maƙale a koya masa.

Akwai damarmaki da yawa, sai dai kaɗai wanda ya tashi haiƙan yana neman mafita ne yake ganinsu. Ƙorafi da furzar da ɓacin rai kamar shan kayan maye ne, a lokacin da ake yi ana samun sanyi-sanyi, amma illar da suke yi wa lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa ba sai an tona ba, za su bayyana.

Yadda da yawa suke tunanin babu mafita sai aiki, haka kuma wasu da yawa suke ganin damarmaki kaca-kaca a noma, sana’ar hannu, “digital skills”, kasuwancin yanar gizo da na zahiri, “entrepreneurship”, “crypto ko “blockchain technology”, dillanci, da buga-buga.

Idan ka yarda akwai mafita a wannan rubutun, to ga shawarar da zan ba ka, ka riƙe zikirorin samun mafita a halin ƙunci da gaske, Allah zai wanke maka zuciyarka da tunaninka, sannan zai taimake ka a lokacin da ka tashi tsaye kana neman mafita. Lokacin tsanani ba ya ɗorewa, amma mutane masu naci da dauriya suna iyawa in ji wani marubuci.