Daga Ahmad Sani
Duk lokacin da wani mummunan abu ya faru a wannan ƙasar tamu a ɗan tsakanin nan za ka ji mutane na cewa ai taliya ce sanadi. Mutanen da ke wannan furucin ba suna yi ne don alhini ko jin tausayi kan abun da ya faru ba ne bare waɗanda ya faru da su, kaɗai suna faɗin hakan ne don huce haushi, da fatan hakan ya ci gaba da faruwa don kowa ya ji a jikinsa ko don ba ɗan takararsu ne ya lashe zaɓe ba.
Babbar matsalata da irin waɗannan mutanen ita ce suna ganin cewa ai mutane sun karɓi taliya ne suka zaɓi ruɓaɓɓun shuwagabanni don haka yanzu lokaci ne na girbin abun da aka shuka. Ta wata fuskar suna da gaskiya, amma bari mu kalli abun ta ɗaya fuskar.
A watan Mayun shekarar 2022 kamar yadda da yawan jaridun Ƙasar nan suka buga, “delegates” na jam’iyyar PDP sun samu abun da ya kai $35,000 a wajen zaɓen fidda gwani da aka yi. Ba iya jam’iyyar PDP ba kaɗai, shi kansa shugaban ƙasa na yanzu a lokacin an rawaito wasu jihohin ya ba kowanne mai zaɓen fidda gwani $25,000, wasu kuma $10,000.
Wannan ba fa shi ne karo na farko da haka ke faruwa ba, kaɗai na kawo shi ne a matsayin misali. Babban abun da nake son nunawa shi ne kowane mutum akwai farashinsa. Wani ba zai karɓi taliya ba, amma zai karɓi daloli, wani muƙami, wani atamfa, wani kwangila, wani abun hawa, wani maggi, wani kuɗin shan wiwi.
To idan har ya zama dukkanmu ba mu fi ƙarfin a ba mu wani abu mu canja ra’ayinmu a siyasa ba meyasa abu kaɗan sai a ce taliya ce sanadi? Amsar ita ce ba mu gaji da yaudarar kanmu ba kan gyara a Najeriya, yawancin masu ɓaɓatu dama ce ba su samu ba, daga sun samu dama kuma tunaninsu da irin aikinsu yake canjawa saboda dalilai da yawa. Wasu a musu barazana, wasu a musu bi-ta-da-ƙulli, wasu kuwa daga sun ɗanɗana sun ji sai su gane ashe da wahala suke, yanzu ne damarsu ta zo.
Rayuwarmu ta yau da gobe tana fassara da yawa ba mu shirya gyara ba, a zahiri ma ba kowa ke son gyaran ba, domin in an yi shi ana tsoron za a iya rasa ci ko sha. Wannan tunanin ci ko sha ɗin shi ne yake kai talakawa da yawa karɓar taliya su yi zaɓe. Idan yunwa ba ta taɓa gigita mutum ba, ba shi da hurumin ganin laifin wanda ya kwana bai ci ba don an ba shi ya karɓa don ba kowa ke da haƙuri da juriya ba.
Wani zai ce to ai talakan ne bai san kansa ba, gwara a ce masa Allah ya ƙara domin shi ya ja wa kansa. Wataƙila mai wannan tunanin ya zamto yana da gaskiya, domin dama ai an gina tsarin zaɓe ne don kowa ya fita ya zaɓi wanda yake so. Amma fa mu sani, ba dukkanmu ne muke zaɓar abun da muke so ba, da yawa muna zaɓar ɗan takarar da kafofin sada zumunta da abokai suka sayar mana ne. Sau nawa ka taɓa jin mutum ya ce wane ya cancanta amma ba zai ci ba? Wasu kuwa dama ba su da ra’ayin, iya sakin hannun jam’iyya iya yadda za su yi rububin ɗan takararta.
Daga ƙarshe ina kira ga duk mai tunanin cewa taliya ce sanadi ya yi karatun ta nutsu, ya gane asali yana yi ne don talaka shi ne bishiya mai sauƙin hawa. Wannan fushin da ƙunar damuke ji, da za mu juyar da akalarsa wajen kawo ci gaba daidai iyawarmu a inda muke da wataran za mu wayi gari ba ma buƙatar mu hana talaka karɓar taliya, domin shi ma ya san me ya kamace shi.
Talauci ba hauka ba ne, ba kuma wanda yake son ya gan shi a hakan, jarrabawa ce da dukkaninmu ba mu fi ƙarfinta ba. Abun da za mu iya yi wa talakawa ƴan’unmu da muke ganin kansu bai waye ba shi ne mu taimake su, mu nuna musu ƙauna, mu wayar musu da kai, mu ilmantar da su, mu nuna musu irin ikon da damammaki da dokokin ƙasa suka ba su. In ba mu yi haka ba kuwa tabbas za su ci gaba da zaɓa mana irin shuwagabannin da muke tunanin ba su dace da mu ba, a yayin da mu kuma za mu ci gaba da tofin alatsine gare su.
Jazakallahu khairan, Allah ya saka da alheri. Wannan gaskiya ne kullum mutanen mu da an shiga wata masifa sai su ce taliya ce sanadi; wannan maganar tana ci mun tuwo a ƙwarya.
Amin summa amin. Ai sai a hankali, abun ba daɗi.