Wani “comment” da na taɓa karantawa shekarun baya tun kafin dambarwar degree da skill ta yawaita ya yi matuƙar tsuma ni, kuma na daɗe ina tunaninsa. Ba zan iya tuna inda zan same shi ba amma abun da mai tsokacin yake cewa shi ne “da kuna cewa ko tallen rake sai mai shaidar karatu… yanzu mai gari ya waya…?
A lokacin abun da na fahimta shi wannan yana jin daɗin kan yadda yanzu waɗanda suka yi karatu suke aiki suke shan wahalar ƙaramin albashi yayin da masu sana’a suke ta more rayuwarsu. Wannan tunanin ba fa iya shi kaɗai ba ne, da yawan mutanen da ba su samu damar yin boko ba, ko kuma sun yi amma ba sa gane karatu duk suna da irin wannan tunanin. Wasu su ce su 3rd class mai albarka suke nema, wasu su ce karatu kam yanzu duk ɗaya ne mai albarka ake nema. Abun da suke nufi da albarkar karatu ba ilimi ba ne, samun wurin maƙalewa mai tsoka. Idan har waɗanda ke karatun suna da wannan tunanin to tabbas bai kamata a ga laifin waɗanda ba su yi karatu ba don sun ce wani abu.
Ba fa iya mutanen gari ne ke da wannan tunanin ba, hatta da yawa daga malaman jami’o’i suna faɗi tashin ganin sun samu sauyin wurin aiki ko sun samu wani muƙami a gwamnati don samun abun da zai ishe su biyan buƙatun rayuwarsu. To idan malaminka ma yana gudun makaranta mene ne laifinka kai ma don ka yi yunƙurin hakan.
Kafin na yi tsokaci kan gundarin matsalar, bari mu yi waiwaye adon tafiya. A shekarun baya idan ka gama makaranta kai ba ƙaramin mutum ba ne, kowane irin karatu ka yi aiki ba zai maka wahalar samu ba, in ka ga ba ka samu aiki ba to ba ka so ne kawai. Wannan abun haka yake a ƙasashe da dama a duniya kamar yadda wani bature yake bayani a shekarar 2006 a taron Teds cewa “A da in ka gama makaranta in ka ga ba ka aiki sai dai in ba ka so ba, amma yanzu masu masters ma buga video game suke a ɗaki saboda ba aikin yi”. (Za a iya neman “Do schools kill creativity” a YouTube don ƙarin bayani)
Malamanmu Allah ya ƙara musu tsayuwa a kan gaskiya sun sha yin lakcoci kan karatu da wadda ya dace a yi. Manyan malamai irinsu Mal Muhammad Bn Usman sun sha jan hankali kan yin boko manufa a maimakon boko sana’a da boko addini. Daga lokacin da muka ɗauki boko hanyar cin abinci kaɗai to tun daga sannan mun kauce hanya. Mutane da yawa suna jayayya a wannan babin domin suna ganin to in dai ba don a gama a samu kuɗi ba ake yin karatun ina amfaninsa. Wannan tunanin kuma ya sa yanzu da ake ganin ba kuɗi a harkar ake son a zame mata.
Mu kalli abun ta wannan fuskar, da turawa suka zo ai duk muna da sana’o’inmu na gado irinsu kasuwanci, noma, ƙira, wanzanci, sassaƙa, saƙa, jima da sauransu. Waɗanda suka karɓi boko da yawa ba za su iya ci gaba da sana’ar gado ba, domin ko da ba su samu girman kai ba, ai bokon tana da cin lokaci, duk lokutan koyon abun ta cinye su. In ma ba ta cinye ba to mutum ya samu wani aikin da karatun da ya yi, ba zai samu lokacin zama ya yi sana’ar gado ba.
A ɗaya ɓangaren kuma ai dama da aka kawo mana boko ba a same mu kara zube ba ilimi ba, muna da iliminmu na addini, rayuwa da sana’a. Ke nan in ilimi kaɗai za a duba ba mu da buƙatar boko, tunda ba mu rasa komai ba. Wannan dalilin ya sa aka yi ta kiran mutane kan su shiga boko da manufa, manufofin kuma su zama na amfanar kai, addini da kuma al’umma. Ana sa ran in aka yi abun da manufa za mu juya shi ya amfane mu a addini da rayuwa a maimakon ya cutar da mu.
Ina magana kan skills da degrees na ɓuge da wasu bayanai, a ɗan yi min haƙuri mai karatu, ina son mu kalli abun ta fuskoki da dama kafin mu kai ga yanke hukunci. Asali tsarin karatun degree an gina shi don in an gama a zauna a office a kula da masu aikin hannu. Marubucin littafin “What Britain did to Nigeria” ya kawo wannan a matsayin dalilin da yasa Inyamurai da Yarbawa suka karɓi boko a hannun turawa, saboda tana ba su damar yin gogayya da Turawan a ofisoshi. Don haka dai a takaice gaba ɗaya an gina wannan tsarin karatun ne don mutum ya gama ya samu aiki.
Wanda aka horar da shi don ya gama ya samu aiki ya kula da ma’aikata a ƙarƙashinsa kuna ganin iya karatu da rubutu ne yake koya? Dole sai an koyar da shi “skills” domin in bai sani ba, ba zai iya kula da su ba. Wani ya taɓa samuna a “site” ina aiki, sai ya ce wato kai ka san shi a karance, su sun sani a aikace. Wannan tunanin shi ne a kan mutane da yawa musamman waɗanda ba su yi boko ba, ko waɗanda ba su tsaya sun yi ta da kyau ba. To amma ba laifinsu ba ne, karatun ya yi lalacewar da da yawa suna gama makarantar ba su koyi abun da suka je koya ba.
Tun kafin a kai ga yanzu, da aka lura cewa ba kowa yake gane karatu ba, wasu sun fi gane aikin hannu, sai aka ƙirƙiri makarantun koyon sana’o’i da aka fi sani da “Technical Colleges”. Waɗannan makarantu manufofinsu koyar da sana’o’i ne tare da fasaharsu. Ga kuma “Polytechnics” da “Montechnics” don duk dai a cike gurbin rashin masu aikin hannun da tsarin degree ka iya haifarwa. Mu fahimta, ba fa na nufin degree ba ya koyar da skills, yana koyar da skills ne irin nasa. Wanda ya yi degree a fannin malanta abun da za a koya masa skills ne na koyarwa, wanda ya yi degree a accounting skills na aikin zai koya, haka engineering, medicine, pharmacy, da sauransu. Ke nan don ba mu ga mutum ya zauna da hannunsa yana aikin ba, bai kamata mu ɗauka shaida ce kawai a hannunsa ba, bai san komai ba, domin shi karatunsa irin skills ɗin da yake koyarwa daban.
Asali wannan cece-kucen ma fa bai taso ba, lalacewar karatu, da son tara abun duniya, da canjawar duniya ne ya kawo hakan. In na ce canjawar duniya ina nufin “4th da 5th industrial revolution” da muke tunkara. A halin da ake ciki na’urori da yawa sun ƙwace ayyuka, ayyukan hannu da ayyukan masu degree, don haka wasu masu kamfanunnuka suke ganin to ai yanzu kawai wanda ya iya aikin hannun za su nema ba wai wanda degree ne da shi ba. Don haka rashin aikin yi yake ta ƙara tsananta, duk da cewa kowacce sabuwar fasaha tana zuwa da sabbin ayyuka, amma da yake har yanzu muna kan tsohon tsarin karatu, sai ka ga ba ma iya koyo da wuri balle har mu samu a tafi da mu a zamanance.
Yakamata mu fahimci cewa, duk yadda duniya za ta canja, wanda ya tsaya ya yi ilimi da kyau ba za a iya tafiya ba shi ba, sai dai in ba ya so. Mutane irinsu Kashifu Inuwa shugaban NITDA na yanzu sun ishe mu misali. Idan layin sana’a ka ɗauka, sai ka jajirce, in aikin hannu ne Allah ya maka baiwa sai ka dage, in layin karatu ka ɗauka shi ma haka, in kasuwa ce duk dai dagiya da fatan dacewa ake. Bai kamata a zauna ma ana yi wa juna izgili ba, don in da duk mun sa manufa mai kyau a harkokinmu da yanzu kai yana haɗe ana aiki kafaɗa da kafaɗa tsakanin masu karatu da masu sana’o’i.
Ba zan iya rufe wannan rubutun ban ba da shawara ga masu degree ba, ba iya degree kaɗai ba, har da su ND, HND, NCE da duk wata shaida, domin duk karatun yana narkewa zuwa burin mallakar kwalin kawai. Shawarata ita ce, in kana da kyau ka ƙara da wanka, in karatun da kake yi akwai skills da za a koya na musamman don samun gurbin aiki to ka zage ka koyi su a wajen waɗanda suka iya tun kafin ka gama makarantar, hakan zai sa ko ba ka samu aiki ba ka gama da sana’arka. Idan kuma ɓangaren admin ne wanda zaman office ne aka koya, to saboda tsaro ka samu wani skill ka koya da za ka ci abinci da shi, kar ka ƙare karatun ba ka samu aiki ba ka dawo kana cizon yatsa da zargin degree. Girman kai ba naku ba ne, in da hali ku fara koya ma tun kafin degreen ya samu.
Daga ƙarshe, entrepreneurs da suke zuga mutane su watsar da karatu su buɗe kamfanoni, yakamata su fahimci cewa, in ma kyakkyawan abu suke nufi ba kowa ke da fahimta mai kyau ba. Ai kuma ayyukanku akwai inda kuka dogara da masu degree, akwai sana’ar da kafin ka samu lasisin yi ma sai kana da shaidar karatu ko mai shaidar karatu a fannin. Manufar yin karatun ne da salon karatun suke buƙatar canji, ba wai daina karatun ba. Waɗanda ba sa sha’awar karatu kuma, ba sai kun matsa wa kanku ba, domin ai kowa da kiwon da ya karɓe shi, sai ku rungumi abun da za ku iya da bai saɓawa shari’a ba. Mu tare a wuri ɗaya shi ne matsala, amma in muka warwatsu kowane ɓangare aka samu mutane, to mu sani rahamar Allah da faɗi take, hannunsa a shinfiɗe suke, ba ya hana mai nema. Allah ya ba mu dacewa gaba ɗaya.