Daga U.A. IMAM
Fitowa ta farko
Malam shankiɗi mai littafin (Adwa’ul Bayan), Allah ya yi masa rahama, yana cewa a ƙarkashin faɗarsa maɗaukaki: “sannan muka gadar da littafin ga waɗanda muka zaɓa daga cikin bayinmu, daga cikin su akwai mai zaluntar kansa kuma daga cikin su akwai wanda yake daidaitawa kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsere gurin ayyukan alkhairi da izinin Allah, wannan shi ne falala babba, za su shiga Aljannah madawwamiya”.
Allah Mai tsarki da ɗaukaka ya rarraba bayinsa zuwa Kashi uku;
Na farko (mai zaluntar kansa); wannan shi ne wanda yake biyayya ga Allah amma kuma yana saɓa masa.
Na biyu (Mai daidaitawa); shi ne wanda yake biyayya ga Allah kuma ba ya saɓa masa, amma sai dai ba ya kusantar Allah da nafiloli na daga ayyukan biyayya.
Na uku: Wanda yake tsere gurin ayyukan alkhairi; shi ne wanda yake aikata ayyukan da suka wajaba a kansa (kamar salloli biyar na farilla da sauran su) kuma yana nisantar abubuwan da suke na haramun, kuma yana kusantar Allah da ayyukan biyayya waɗanda ba na dole ba (kamar azumin nafila da sauransu).
Sannan Allah ya yi ma dukkansu alƙawari a cikin faɗinsa (يدخلونها) (zasu shiga Aljannah madawwamiya) kuma Shi ba ya saɓa alkawari. Ma’ana zasu shige ta, ya haɗa da mai zaluntar kansa da mai daidaitawa da mai tsere gurin ayyukan alkhairi. Saboda haka ne ma’abota ilimi suka ce “Abin da ya fi dacewa shi ne wannan (wawun) ɗin a rubuta ta da ruwan idanu (hawaye) saboda ba ta rage kowanne musulmi ba daga cikin waɗancan kashe-kashe guda uku. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijina!!!. Ya Allah wa ya kai ka rahama, wa ya kai ka karamci, wa ya kai ka girma!, Fir’auna ya ce: Ni ne ubangijinku ma fi ɗaukaka” Amma ya ya Allah ya mai da masa da zance? Sai Allah ya ce ma Annabi Musa da Haruna: “ku tafi zuwa ga Fir’auna, lallai ya wuce iyaka, ku faɗa masa zance mai taushi ta yiwu ya yi tunani ko ya ji tsoro”.
Wani daga cikin bayin Allah yana cewa a lokacin da ya ji wannan ayar da ta gabata “Ya Allah idan wannan shi ne rahamarka da sauƙin kanka ga Fir’auna wanda ya ce shi ne ubangiji ma fi ɗaukaka, to ya ya rahamarka da sauƙin kanka zai kasance ga wanda ya kira sunanka ya ce: “tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka!!?.