Na fara damuwa da son sanin ni wanne irin mutum ne fiye da shekaru 8 da suka wuce. Ba ni kaɗai ba, mutane da yawa suna jin daɗi in suka ga suna gane bambance-bambancen da ke tsakanin mutane. Da fari na ɗauka mutum iri na ni kaɗai ne, domin duk mutanen da nake kewaye da su mun sha bamban ta kowacce irin fuska.

Sai dai abun da ban sani ba shi ne, mutane iri na suna nan jingim a cikin duniya suna hada-hadarsu, ko dai ban haɗu da su ba, ko kuma ban san ta yadda zan gane su iri na ba ne. To ta ya ya na san muna da yawa? Abu mai sauƙi, na karanta littafin Tim Lahaye a kan “Temperament” (ɗabi’u na halitta da mutane ke zuwa duniya da su) mai suna “Why You Act The Way You Do”.

Sanin kai wanne irin mutum ne yana da matuƙar muhimmanci, za ka gane inda baiwarka take don ka yi ta aikin ingantata, za ka san rauninka dan ka san abubuwan da za ka guje su da waɗanda za ka yi taka-tsan-tsan da su, da kuma waɗanda za ka daure ka koya. Za ka san irin mutanen da za ka yi haɗakar wani abu da su kamar aure, kasuwanci, abota, dss., saboda su zama sun cike maka giɓin abubuwan da ka rasa a rayuwa.

Za ka san halayen da za su yi saurin cutar da kai da makusantanka a tattare da kai. Hatta aikin yi ko sana’a za ka san wacce za ta fi dacewa da mutum irin ka. Ba wannan ba kaɗai, ko gudunmawa za ka ba wa addini za ka gane kai ta wanne ɓangare ne taka gudunmawar za ta fito.

Kafin na shiga cikin karatun, yana da kyau na fara da bambance yanayin mutum, ɗabi’unsa, da kuma halayensa (temperament, character, personality). A Hausa kusan duk hali zan ce muke kiransu, na ba su sunayen nan ne dan kawai bambancin ya bayyana, ba lallai su zama haka ake kiransu ba a Hausa.

Shi yanayin mutum shi ne halayen da aka haife shi da su, waɗɗanda ya gada daga iyaye da kakanninsa, ɗabi’unsa kuma haɗin gambiza ne ne yanayinsa, tarbiyyar da ya samu, iliminsa, imaninsa, aƙidunsa, muradunsa da sauransu, wannan shi ne dai ainihin haƙiƙanin mutum. Halaye kuwa za su iya zama gaskiya za su iya zama ƙarya, su ma kamar ɗabi’u ne amma mutum yana da ikon bayyana yadda yake so mutane su san shi, dan haka ana iya yin ƙaryar halayya (faking), ana kuma iya ɓoye rauni ko wata manufa a cikin halayya.

Tim Lahaye ya kasafta mutane zuwa gida huɗu (4) bibbiyu, biyun farko su ne mutane masu surutu da shiga jama’a (extroverts) sauran biyun kuma su ne shiru-shiru waɗanda ba su cika shiga mutane ba (introverts).

Na-mutane

A ɓangaren masu surutu akwai wanda na kira “Na-mutane”, waɗannan su ne irin mutane masu yoyon magana ɗin nan, ba sa iya riƙe bakinsu, duk inda suka shiga dole sai an san suna wurin, akwai su da haba-haba da mutane, ga su kuma ba wuyar sabo ko ma ƙulla abota. Ba su san jimami ba, kuma komai suna iya mayar da shi raha, sun yarda da tatsuniyar dawwama cikin farin ciki a rayuwa.

Kaɗan daga cikin ƙarfinsa: yana da saurin sabo, ya iya ba da labari, ba ya gajiya da surutu, yana rayuwa a yanzu (tuna baya ba ya damunsa), yana da nuna tausayawa da alhini kan abu marar daɗi na wani, yana nuna shauƙi kan komai, ga shi da raha da kuma shiga cikin ayyukan sa kai dumu-dumu, saurin ƙulla abota, fara magana in kun haɗu, dss.

Kaɗan daga cikin rauninsa: ba ya iya tursasa kansa ya yi abun da ya dace, in ka ba shi aiki da wuya ka ga sakamako sosai, yanayinsa yana saurin canjawa daga walwala zuwa tausayawa, in ka shiga wani hali sai ya fika nuna jimami dan haka ma ana iya zargin ko na ƙarya ne in ba a san shi da kyau ba, ba shi da tsari, ya fi sauran nau’in mutane girman kai, kuma cikin sauƙi yake samun kansa cikin yaudara, ƙarya da cutar mutane don ya ɓoye rauninsa, yana ƙarawa komai gishiri (kambaba abubuwa), dss.

Jagora

Nau’i na biyu cikin masu surutu shi ne “Jagora”, shi Jagora bai kai Na-mutane surutu ba, shi ma yana da saurin sabo da jama’a, shi ma’aikaci ne, yana da zummar cimmawa, yana zama jagora duk inda ya shiga, yana son a ce shi ke jan ragamar komai koyaushe, yanke abun da zai yi ba ya wahalar da shi, haka ma yanke wa waninsa, yana wadatuwa da kansa, yana da buruka kuma yana tsara yadda zai cimma su.

Kaɗan daga cikin ƙarfinsa: ƙarfin gwiwa, wadatuwa da kai, hangen nesa, duk abunda ya sa a gaba ana ganin ci gaba, yanke abun da zai yi ba ya ba shi wahala, jagora ne, akwai shi da naci, baya jira, in ba ku yi ba zai yi da kansa.

Kaɗan daga cikin rauninsa: ba ya nuna ƙawa zuci (Aɗifa) dan haka bai cika nuna tausayi ba, yana ganin komai zai iya yi da kansa ko ba taimako, yana danne na ƙasa da shi da musu kama-karya, ya iya ƙeta, bai cika yafiya ba, yana da saurin fusata dan haka ma yake yawan faɗa da mutane, kuma ya iya cin fuska da baƙar magana, a taƙaice tunzura mutum yakan iya sa shi nishaɗi, ba ya yabon wanda ya masa aiki, ba kuma ya jin maganar na sama da shi sai ya zama dole.

Ba iya karatun ba ke nan, zan dakata a nan saboda gudun tsawaitawa, sai mun haɗu a kashi na biyu. Kafin nan akwai wanijan hankali, ko da kaga halin wani da ka sani kada ka yi gangancin faɗa masa ko da kuwa abokinka ne, domin in ya ga raunin irin wannan mutumin ba zai yafe maka, kuma da wahala ka iya gamsar da shi cewa ba iya bayanin ba kenan, dan haka gara ka bar shi ya gano da kansa in yana da buƙata. Babbar manufar ita ce, kai ka san kanka, sannan ka fahimci da su wa kake tare, sai a kula.