Idan mai karatu yana biye, zai iya kiyaye bayanai sun riga da sun gabata a kashi na farko kan kason mutane ma su surutu, yanzu zan ɗaura a kan masu shiru.
Ɗan-baiwa
Nau’i na gaba wanda shi ne na farko cikin mutane shiru-shiru shi ne “Ɗan-baiwa”, waɗannan su ne irin mutane masu basira ɗin nan, wanda kowa yake mamakin baiwarsu, akwai su da lissafi, sadaukar da kai, da son ganin komai ya cika 100 bisa 100. Ba su da saurin ƙulla abota amma in suka ƙulla abota da kai ba za su ci amanarka ba, yanayinsu yana saurin canzawa dan haka sun fi duk sauran saurin shiga damuwa. Duk da ba su da surutu amma in suka samu wuri za ka rantse ba su ba ne. Akwai su da tattali da rowa, in an ɓata musu rai suna da fushi amma ba kamar Jagora ba, su a zuci za su ci gaba da tafarfasa dan haka akwai yiwuwar su ɗauki fansa ma.
Kaɗan daga cikin ƙarfinsu: ƴan baiwa ne, akwai su da basira, suna da lissafi, suna son ƙyale-ƙyale da ado, suna iya tursasa kansu su yi abun da ya dace, suna da zurfin tunani da tsari, ba su cika son hayaniya ba, kaɗaici yana ba su damar zurfafa tunani, ba su cika yin raha da ba saboda komai da muhimmanci suke ɗaukarsa, suna da baiwar ƙirƙira da bincike, duk aikin da suka sa a gaba sai sun ga ƙarshensa, sun fi sadaukar da kansu kan abin da mutane za su amfana, dss.
Kaɗan daga cikin rauninsu: saboda zurfin tunaninsu cikas suke fara hangowa a kan aikin da za su yi, caccanzawar yanayinsu ya sa suna saurin shiga da kuma daɗewa a damuwa, saboda suna son yin komai 100 bisa 100 ya sa ba a cika burge su ba, ko su ma suna barin ayyukan da suka ga ba za su cika yadda suke so ba, ba sa shiga mutane, suna kallon rayuwa a yadda ya kamata a rayu ba a yadda take a zahiri ba, basirarsu ta sa suna da saurin zargi da mummunan tunani kan abubuwa, suna da saurin kushe abu tare da caccakar abin da bai kai a ma’auninsu ba, saboda sadaukar da kansu kan wani aiki sukan manta ma da kansa, wanda hakan kan cutar da lafiyarsu da alaƙarsu da mutane, dss
Miskili
Kaso na ƙarshe shi ne “Miskili”, su waɗannan shiru-shirunsu har ya fi na Ɗan-baiwa, domin ba wani shauƙi da za su samu kansu a ciki da zai sa su zama masu surutu. Da wuya ka ga sun yi fushi ko an ɓata musu rai, suna da mugun sauƙin kai don haka sun fi sauran daɗin sha’ani, suna da kakaci amma ba su cika dariya ba ko da sun yi kakacin, ba sa wuce iya abun da aka sa su in an sa su aiki, ba su cika son ɗaukar nauyin komai ba, sun fi jiran rayuwa ta zo ta same su sama da su tasi su tunkare ta.
Kaɗan daga cikin ƙarfinsu: nutsuwa da rashin hayaniya, suna da sauƙin kai da daɗin sha’ani, za ka iya dogara da su, sun iya sasanta mutane, suna da tsari, akwai su da kakaci, suna kallon rayuwa a zahiri, ba sa yin abu ba tare da tunani da kuma kyakkyawan tsari ba, ba sa fara aiki da kansu amma in dai an sa su za su kammala shi, suna da son tsafta, ba su cika shiga sha’anin mulki ba, amma duk lokacin da aka gano su aka zaƙulo su aka ba su mulki, suna yin mulki da ƙwarewa ta ban mamaki, suna da son zaman lafiya da gujewa tasin hankali, dss.
Kaɗan daga cikin rauninsu: ba sa iya zaburar da kansu, suna da ganda, suna da son kansu, akwai su da rowa da tsoro, suna da yawan damuwa da zullumi kan abubuwa, ba sa iya saurin yanke me za su yi balle su yanke wa wani, kullum cikin ƙoƙarin tsare kansu suke daga cutuwa ko asara dan haka da wuya su ɗauki kasada, suna da turjiya da tawaye, za ka iya musu bayanin me kake son su maka su yi kamar sun yarda amma da sun juya baya su yi yadda suke so.
Tim Lahaye bai tsaya a iya kasa mutane gida huɗu ba, ya ƙara bayani da cewa kowanne mutum haɗin gambiza ne na kaso huɗun, kowa ya haɗa ɓangare biyu amma ɓangare ɗaya yana fin rinjaye, akan samu masu haɗa uku amma su suka fi ƙaranci, don haka ya ce mutane za su iya kasuwa gida 12. A takaice dai kai tsaye mutum ba zai iya gane wanne ya fi rinjaye a tattare da shi ba, yana da kyau a karanta littafin dan samun ƙarin haske. Don sauƙaƙa wa mai karatu, akwai ƙaramin littafi da na rubuta mai suna “Ka San Kanka” ku danna kan sunan littafin don sauke shi kai tsaye a wayoyinku, za ku ji daɗinsa ƙwarai, don da yawa sun ce sun ji.
Abu na gaba da zan ƙara shi ne, su waɗannan ɗabi’u na halitta koyaushe suna tare da mutum har ƙarshen rayuwarsa domin gadonsu ya yi, amma iliminsa, tarbiyyarsa, imaninsa da aƙidunsa su suke mayar da shi mutum. Don haka yana daga cikin amfanin gane ƙarfi da rauni na halitta, mutum zai san ina zai karkata a rayuwa, sannan zai san waɗanne halayya ne zai zama a ankare da su dan kar su dinga ɓata masa hulɗa da jama’a.
Misali, Na-mutane dole ya yi aiki a kan rashin iya sauraren mutane, ya koyi kama bakinsa ya ji su ma me za su ce. Jagora dole ya koyi daina yin ƙarfa-ƙarfa da danne na ƙasa da shi, saboda wannan zai sa su daina ganinsa da ƙima. Ɗan-baiwa dole ya koyawa kansa kyakkyawan tunani kan abubuwa, in ba haka ba basirar tasa ba za ta masa amfani ba. Miskili sai ya koyi zaburar da kansa ko zama wurin da za a dinga yawan zaburar da shi in ba haka ba zai tsinana komai ba a rayuwarsa.
Wannan raba mutane da Tim Lahaye ya yi ba lallai ya zama cif-da-cif 100 bisa 100 ba amma a cikin duk rabe-raben da ake yi ana ganin cewa wannan na san ya fi tattara kowa da kowa. Mene ne mafita kan rauninmu? Bin Addini sau da ƙafa, Allah ne ya halicce mu a haka, kuma ya ce ga yadda yake so mu yi ko da hakan yaci karo da yadda muke, don haka mafitarmu, tana cikin kwatanta koyarwar addini sau da ƙafa. Shi kan sa Tim Lahaye abin da ya bayyana a matsayin mafita ke nan a matsayinsa na kirista.
Babban abun ma da yake nuna cewa mutum ba zai amfani kansa ba a rayuwa shi ne ya dinga kafa hujja da cewar ai haka yake, don hak ba zai sauya ba. Kowa yana da abubuwan da Allah ya masa da za su taimaka masa wajen aikata daidai da cin nasara a rayuwa.
Daga ƙarshe Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi yace “ Allah ya halicci Annabi Adamu daga wata damƙa da ya yi daga ƙasa (a wurare mabambanta), don haka ƴan Adam an halicce su a gwargwadon haɗe-haɗen ƙasar. Sai ya zamto a cikin mutane akwai ja, akwai fari, akwai baƙi akwai kuma tsaka-tsakin dukkaninsu, akwai mai kyan hali, akwai mai munin hali, akwai mai sauƙin lamari, akwai mai wahalar sha’ani” (Abu Dawud da Tirmizi, kuma sun ce hadisi ne kyakkayawa).