Rayuwa a ɗan tsukun shekarun nan tana gudana ne kamar haka; kana ƙarami an sa ka a makaranta, bayan shekara 6 ko 7 ka gama ka shiga wata, bayan shekara 5 ko 6 ita ma ka gama ta, daga nan sai ta gabanta, shekara 4 ko 5 ita ma an gama, sai hidimar ƙasa shekara ɗaya, sai kuma fara rayuwa.

A zahiri duk da cewa muna shafe shekaru 17 kafin mu mallaki kwalin degree, ba ma ɗaukar hakan a wani abu. Haƙurinmu yana bayyana ƙwarai a wannan fafutukar, sai dai kash, a yayin da za mu fara rayuwa ba kowa ke iya haƙuri ba.

Ba ina nufin rayuwar neman ilimi ba rayuwa ba ce, rayuwa ce, ba shakka ma wannan ɓangaren yana daga cikin lokaci mafi muhimmanci na rayuwarmu da inda ace muna ribatarsa yadda yakamata, da wata maganar ake ba wannan ba. Bin tsararren jadawali da al’umma ta shimfiɗa yana daga cikin abun da yake hana mutane da yawa fara rayuwa da wuri, sai ka ga mutum ya haura 30 amma bai san inda ya sa gaba ba, saɓanin a da da ɗan shekara 30 da mosti yana iya zama shugaban ƙasa. Wannan batun mu ajiye shi gefe guda, sai wani karon mu waiwaice shi.

Abun da nake son tattaunawa a wannan lokacin ba muhimmancin lokaci ba ne, a’a tasirinsa ne a kan komai. In dai mutum zai iya shafe shekara 17 don samun shaidar karatu guda 4 (PLC, SSCE, BSc, NYSC) to mene ne ba zai iya haƙurin jira ya samu ba a duniyar nan?

An ce wani malami lokacin da yana neman ilimi, ya yi, ya yi, ya kasa samun ilimin, bayan wasu shekaru ya haƙura ya tattara zai koma gida, a kan hanyarsa sai ya ga ruwa yana zuba a saman wani dutse, ya ga duk da siranta irin ta ruwa, da ƙarfi irin na duste, zuba kullum da ruwan yake a kan dutsen ya masa tasiri, don haka ya koma da baya ya nemi malami a ka ɗaura shi a sabon tsari ya ci gaba da neman ilimi.

Yau da gobe ba ta bar komai ba, ba abun da za ka shafe shekaru kana yi ba ka naƙalce shi ba. In kuwa ka ga ba ka yi nasara a ciki ba, to ko dai kana yin abun ba daidai ba, ko kuma an so a jarrabe ka ne, ko ma kai ne ba ka samar da ma’anar cin nasara a wannan aikin ba.

Gaggawa, ci da zuci, hanƙoran abun da ke gaban wasu, alhalin ga namu gaba gare mu, ba inda zai kai mu sai inda ba mu nufaci zuwa ba. Idan ka yi haƙuri ka jure za ka kai gacci. Idan ba ka kai gacci ba, wataƙila ba kan layin da ya dace da kai ba kake, don haka sai ka canja wani layin.

Wai mai haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa in ji bahaushe. Wannan maganar akwai hikima a ciki, duk halin da kake ciki na jin daɗi ko akasinsa lokaci ne, zai iya canjawa cikin ƙiftawar ido. Duk abun da kake son yi ka ba shi lokaci ka gani, duk abun da kake tsoro ka ba shi lokaci ka gani, kai koma mene ne lokaci zai nuna. Idan mai sana’ar hannu yana iya shafe shekara 10 ƙarƙashin maigidansa kafin ya goge a yaye shi, idan yaron shago yana shafe shekara 8 kafin a yaye shi, idan ma’aikaci yana shafe shekaru 20 kafin ya taka wani matsayi, to kai da ka tasa wani babban abu a gaba me zai hana ka jiran lokacinka?

Sai dai a wannan gaɓar kada a min gurguwar fahimta, ba ina nufin haƙuri irin na shanun da ke jiran gawo ya faɗo  su ci ba, ina nufin haƙuri tare da aiki, haƙurin farko (passive) yana da muhallinsa, amma ba nan ba ne, haƙurin da nake nufi (active) shi ne haƙuri alhalin kana ci gaba da abun da kake yi, haƙuri a cikin halin kana faɗi tashin neman mafita.

Da malamai suka lissafo abubuwan da suke taimakawa a samu ilimi sai suka haɗa har da ɗaukar lokaci ana yi. Da Allah maɗaukaki ya nufi bayyana ayyukan da ya fi so bayan farilla sai ya ce (ta bakin Annabinsa mai tsira aminci) “Wanda aka dawwama ana yi, ko da ɗan kaɗan ne…”.

Ba abun da yau da gobe ta bari. Duk wani abu yana bin bayan lokaci ne, basira, ilimi, baiwa, aiki tuƙuru duk suna marawa wanda ya daɗe yana yi ne baya. Daga an samu yankewar lokaci, za su zama tasirinsu ya ƙare. Lokaci ne yake rarrabe tsakanin mazaje, masu nasara da masu kasala, ƴan baiwa na haihuwa da ƴan baiwa na aiki tuƙuru. Matuƙar kana yin abun da kake yi da idanun basira to ka jira lokaci, idan ma ba ka yi da idanun basirar duk dai lokaci zai nuna maka abun da ka rasa.

Wannan dalilin ya sa mutanen da suka taso kan wani abu guda da suke yinsa kullum suke saurin shan gaban waɗanda suka taso a kan abubuwa da yawa. Wannan ya sa ake ganin bambanci tsakanin wanda ya fara yana shekara 13 da wanda ya fara yana shekara 23. Ba iya tsara amfani da lokaci ba ne, ba iya basira ba ce, ba iya baiwa ba ce, ba iya samun kai a gidan masu kuɗi, talakawa ko masu mulki ba ne, ba shakka ko da akwai tasirin waɗannan, amma bambacin daɗewa ana yi shi ne kan gaba. Ko ban ba da misali ba kai ma za ka iya ɗaukan mutanen da ka sani ka misalta, ka ɗauki ƴan shekara 35 guda biyu, wanda ya daɗe a kan wani abu, da wanda ya fara kwanannan, za ka ga bambancin.

Allah muke roƙo ya ba mu tabbatuwa akan ayyuka masu amfani da muka sa gaba. Idan kuna da misalan da za ku bayar, zan so ku ajiye su a sashen tsokaci don abun ya ƙara fitowa fili ga waɗanda ba su fahimta da kyau ba. Sai mun haɗu a rubuta na gaba. Mun gode.