Wannan wani labari ne da yake kamanta wasu mata guda biyu, kowacce mijinta daban kuma suna rayuwa a gidaje mabambanta.

Macen farko:

Ta tashi da Asuba ta yi sallah, sannan ta shirya girki wa mai gida da yara.

Mace ta biyu:

Ta yi sallahr Asuba gab da lokacin sallahr zai fita, sannan ta koma ta ci gaba da baccinta

Macen farko:

Bayan sun karya kumallo ta shirya yara zuwa makaranta sannan ta taya mai gida kimtsawa cikin nishaɗi da daɗin rai.

Mace ta biyu:

Ta tashi a makare, ta hau faɗa ga yarinyarta saboda ba ta taje kanta ba, ta ɗaga murya wa ɗanta saboda har lokacin bai bar makwancinsa ba. Daga nan gida ya hautsine sai ihu da hayaniya da faɗa ake ji. A haka mai gidan ya tashi ya fice daga gidan bai ko karya ba, ya tsaya a hanya ya ci abinci wanda hakan ya ja masa makara a wajen aiki.

Macen farko:

Bayan mai gida da yara sun fice zuwa makaranta da wurin aiki, sai ta zauna ta huta na awa guda. Daga nan ta ɗauki Alƙur’ani ta karanta izu guda da ta saba yi kullum. Bayan ta gama ta yi sauran ayyukan gida tana mai sauraren kaset na wa’azi, daga nan ta haɗa abincin rana.

Mace ta biyu:

Ba tare da wani jinkiri ba, mai gida da yara suna fita wurin aiki da makaranta ta koma bacci, ba ta farka ba sai can rana. Da ta tashi kuma sai ta shiga maƙota har yaranta suka dawo sannan ta dawo gida. Tana dawowa kacaniya ta ci gaba daga inda aka tsaya, a haka ta musu abincin gaggawa da za su kashe yunwarsu da shi.

Macen farko:

Tana bakin ƙofa tana jiran dawowar mai gida fuskarta cike da annuri da murmushi, ta ci kwalliya da kaya masu kyau ga ƙamshi ta ko’ina. Bayan ta marhabance shi ta kawo masa abinci ya ci, daga nan ta bar shi don ya huta, ta kwashe yaran zuwa wani ɗaki na daban don su yi ayyukansu na gida da aka ba su a makaranta.

Mace ta biyu:

Mijin ya dawo gida yana mai sa ran samun nutsuwa da farin ciki, amma rashin sa’arsa yana shigowa ya ci karo da takalman yara da kayansu a tsakar gida, matar fuskarta a murtuke, ga kayan girki a jikinta ƙamshin albasa da kayan haɗi sai tashi yake. Abincin ma bai samu nan take ba sai da ya jira. Ya yi ƙoƙarin ya ɗan rintsa amma halin da gidan yake ciki bai ba shi dama ba.

Macen farko:

Bayan sallar La’asar ta sake gyara gidanta, ta kimtsa yara, ita ma ta ƙara kimtsawa don bata sani ba ko mai gida zai ce a fita ziyara. Mai gidan yana zaune cikin jin daɗi yana wasa da yaransa, fuskarsa cike da walwalar ganin su tsaf-tsaf.

Mace ta biyu:

Bayan La’asar ta kwanta bacci, ba ta farka ba sai da maƙota suka mata magana. Haka ta bar gidanta a yadda yake ba gyara ta shiga maƙota tsegumi.

Macen farko:

Bayan Sallar Magariba da Isha’i ta tattara yaran ta koya musu wani abu daga Alƙur’ani da addu’o’i. daga nan ta tafi ta shiryo abincin dare ta bar su suna bita. Bayan sun ci abinci suka yi wasa na awa guda kafin daga bisani su kwanta. Daga nan sai ta shiga wurin mai gida tana sanye da kayan bacci masu kyau da sauran kayan ado na mata (su sarƙa da zobe). Suka yi baccinsu cike da farin ciki.

Mace ta biyu:

Bayan Sallar Magariba da Isha’i sai yaranta suka ci gaba da wasa suna ta hayaniya da ihu da tsalle-tsalle har ƙarfe ɗaya na dare kafin nan suka yi bacci. Mai gidan ba zai iya bacci ba saboda hayaniyarsu. Haka ita ma matar ta zo ta kwanta a gajiye ba tare da ta kula da haƙƙinsa ba.

Mene ne tunaninku game da waɗannan mata biyun? Wacce za ka so ka aura? Wacce ce za ki so ace kina koyi da ita?

An ciro daga littafin “Winning the Heart”.