FOUR TEMPERAMENTS IN HAUSA

A ƴan shekarun nan, ana ƙara samun yawaitar jumlar nan ta zamto kamar yayi wato “Bi abun da kake so” wacce take nufin ka mayar da abun da kake ƙauna sana’arka, aiki ko karatunka.

Akwai saɓani da yawa tsakanin mutane, tun daga kan masu bincike kan halayyar ɗan’adam da ƴan kasuwa (business people) da masu ƙirƙirar kasuwa (entreprenuers) da marubuta har ma da masu sana’ar magana dan zaburar da mutane (motivational speakers).

Wasu suna ganin ka bi abun da kake so ɗin yana da kyau, hujjarsu in ba ka so ba lallai ka mayar da hankali ko ka iya jurewa ba. Yayin da a ɗaya ɓangaren wasu suke ganin ɓata lokaci ne ka tsaya neman abun da kake so, zai fi maka ka so duk abun da kake yi. Akwai ma masu ganin samun ƙwarewa a abun da kake yi shi ne zai ba ka irin wannan son, don haka komai kake yi ka mayar da hankali wajen ƙwarewa, da sannu zai zama maka jiki kuma za ka so aikinka maƙurar so.

Duk me ya jawo wannan cece-kucen? A fahimtata gaba ɗaya abun yana komawa ne kan buƙatar mutum ta son yin rayuwa mai daɗi, don haka kowa yake ƙoƙarin ba da mafitarsa kan inda rayuwa mai daɗin take. Ba iya jin daɗi kaɗai ba, mutum yana da buƙatar ya gan shi a wani matsayi na musamman, wato samun ɗaukaka da nasarar rayuwa duk abubuwa ne da muke burin samu.

Dr Abraham Maslow, ya raba buƙatun mutum zuwa gida biyar, akwai buƙatu na jiki waɗanda suka haɗa da abinci, ruwa, iska, muhalli, akwai buƙatu na tsaro wanda suka ƙunshi samun kariya, bin doka da oda, samun zaman lafiya, akwai buƙatu na alaƙa waɗanda suka haɗa da soyayya, samun karɓuwa a cikin jama’a, akwai buƙatu na ji da kai, waɗanda suka haɗa da samun ɗaukaka, matsayi da yin nasara, akwai kuma na ƙarshen wanda shi ne samun gamsuwa da kai.

Mutane mataki-mataki ne a waɗannan buƙatun, wanda yake fama da yunwa da baƙin talauci ba zai damu da tsaro ba, sai ya ci ya ƙoshi ne zai fara fatan a samu tsaro, haka inda ake yaƙe-yaƙe, ba soyayya da tara abokai ba ne a gabansu, a samu zaman lafiya shi ne muradinsu. Wanda duk waɗannan ba matsalolinsu ba ne shi ne zai fara tunanin samun matsayi da ɗaukaka, daga nan sai ya fara ƙoƙarin biya wa kansa buƙatu na taƙama da ji da kai, wanda duk ya wuce matakan nan kuma sai ya koma neman yadda zai gamsu da kansa, ya ji cewa abun da yake yi ya kai ya samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwar da yake buƙata.

Idan muka lura, mataki na ƙarshen shi ne wanda mutum ya gama gane gaskiyar rayuwa, duk nasarar da yake nema ya samu, matsayi da ɗaukaka duk Allah ya ba shi, dukiya ga ta nan tsababa in ita yake son tarawa, amma duk waɗannan sun kasa wadatar da shi, zai fara tunanin inda kuma zai dinga samarwa da kansa gamsuwa. Wannan dalilin ya sa ma wasu masanan suke ganin cewa buƙatun nan da Abraham ya raba ba fa a jere suke ba, a’a a kowanne mataki mutum yake zai iya neman na ƙarshen, wato gamsuwa da kai, wanda shi ne ma asalin jin daɗin rayuwar.

A ra’ayina, ko mutum ya bi abun da yake so, ko bai bi abun da yake so, yana rayuwa ne Allah yana buɗe masa fahimtarsa, yana gane rayuwa, yana gane abubuwan da suke ci da waɗanda ba sa ci, yana gane me ya dace da shi, yana gane abubuwan da yana yi ne kawai don ya saje da jama’a ba don shi yana da buƙata ba, wasu sukan samu dama su kai har lokacin da suke iya fahimtar kansu, da irin baiwar da Allah ya musu, da ta inda za su amfani jama’a da wannan baiwa.

Wasu mutanen sukan samu damar gane kansu tun da wuri, wato tun suna yara, don haka kafin rayuwarsu ta yi nisa za a dinga ganin abubuwa na ban mamaki a tattare da su, domin tun asali sun gane ƙarfi da rauninsu, sun kuma san inda suka sa gaba a rayuwarsu.

Wasu kuma sai girma ya riske su, sun gama tara iyalai, shekaru sun ja, jikinsu ya yi laushi, ƙwarin gwiwa da zimmarsu sun mutu sannan suke gane kansu, a wannan lokacin suke gane ashe rayuwar wani suka yi ta yi ba ta su ba, ga yadda yakamata su rayu. Wannan ya kan zama musu darasin da suke koyar da ƴan baya don kar su samu kansu a irin halin da su suka tsinci kansu.

Wasu kuma yakan zamar musu abun danasani da cizon yatsa, sai su ɗauki alhakin komai su ɗaura kan shuwagabanni da iyaye dan su samarwa kansu hanzarin da za su dinga fakewa da shi a matsayin uzuri na rashin rayuwa a kan tsari da manufa.

Akan samu waɗanda duk da lokaci ya ƙure kafin su farga, ba sa yin ƙasa a gwiwa za su canja akalar rayuwarsu don dama abun da suke ta neman sani kenan, don haka yanzu da ya zo musu kwatsam suka ankare, sai su juya su koma irin rayuwar da ta dace da su.

Idan mai karatu yana biye, zai iya fahimtar cewa, ina ƙoƙarin nuna muhimmancin mutum ya fahimci kansa da wuri ne a rayuwa, da kuma illar rashin sanin kansa da wuri gare shi. Wanda ya san kansa abubuwa sun fi zuwa masa da sauƙi, kuma ba zai damu da dole sai ya yi abun da zuciyarsa take muradi ba, ya san cewa abun da zai samu a ƙarshe ya fi wannan jin daɗin na ɗan lokaci.

Domin amsa duk tambayoyinku kan sanin kai, amfaninsa da yadda rayuwa take daɗi ga wanda ya san kansa, na tattara wasu bayanai daga masana a fannin a littafin “Ka San Kanka”. A halin yanzu littafin ana iya samun kwafinsa na pdf kyauta.

Wanda yake buƙatar sauƙe littafin sai ya danna wannan link ɗin domin sauke shi. Ina fatan za ku amfana da saƙon dake cikin littafin. Wanda ya karanta ya amfana yana iya turawa makusantansa don su ma su karanta su amfana. Allah ya ba mu dacewa.