Ana gab da fara azumin nan na ga wani bidiyon ‘comedy’ na Abba S Boy, a cikin bidiyon budurwarsa ta kira shi a waya, “Barka da rana” ita ce kalmar da ta yi amfani da ita wajen gaishe shi, buɗar bakinsa sai ya hau faɗa, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita, wai jinya yake da za ta ce da shi barka?! (Wannan a shekarar 2022 ne lokacin da na yi rubutun)

Duk da wasan nishaɗi ne, amma akan samu waɗanda za su so su yi faɗa da ƴan matansu a irin wannan lokaci, ko dan ba su da kuɗin kayan sallah ko kuma ba su yi niyyar yi ba. A bisa wannan dalilin ne na ga dacewar in nusar da ku cewa, duk wacce ta yi faɗa da kai, ko kake tsoron za ku rabu a kan kayan sallah ko na azumi to ba matar da ta dace da kai ba ne, ko aure kuma kuka yi sai wannan matsalar ta bi ku gidan aurenku.

Dalilan da za su kai mace ga wannan halin suna da yawa, kowanne ɗaya kuma ya kai ya sa ku raba gari, zan lissafo kaɗan daga ciki a wannan rubutun dan in irin haka ta faru da kai ka san matsayinka.

Amma kafin nan, a ganina dalili uku ne za su sa mutum ya ƙi yi wa mace hidima a lokutan sallah; ba shi da shi, ba shi da ra’ayin yi, ko kuma yana da rowa. Zan yi ƙoƙarin alaƙanta waɗannan abubuwan da dalilan da za su tabbatar cewa ko dai ba ka da dace da ita ba, ko ita ba ta dace da kai ba.

Tana da kwaɗayi

Asali hidimar sallah ba dole ba ce, kyautatawa ce kawai don ƙara danƙon ƙauna (kodayake waɗanda suke yin soyayyar shekaru 5 yana iya zama musu farilla). Kenan babu wani dalilin da zai sa budurwa ta sa a ranta cewa tunda tana da samari za su mata kayan sallah.

Duk wacce take da irin wannan ƙwallafa ran a kan kyauta daga wurin masoyi akwai alamar kwaɗayi a tattare da ita. Idan ba ƙwallafa rai ba, me zai sa har ta yi faɗa da kai don kawai ba ka mata kayan sallah ba?

Idan ka gane cewa budurwarka kwaɗayayyiya ce, to ba abun da ya dace da kai illa ka tattara naka ya naka ka yi gaba, domin in ma ba ka yi hakan ba, tana samun wani da ya fi ka maiƙo za ta yi gaba abunta.

Ta raina ka

Akwai mazajen da ke zubar da ƙimarsu a wurin yarinya tun farko-farkon haɗuwarsu. Sai ka ga abu bai kai ya kawo ba sun dage suna ta ba da haƙuri. Wannan ɗabi’a tana saurin jawo raini ƙwarai da gaske, wanda kuma raini a zaman aure ba ya haifar da ɗa mai ido.

Idan budurwarka ta nemi yin faɗa da kai a dalilin ba ka mata kayan sallah ba, alhalin ko dai ba ka da shi ne, ko kuma al’adar ba ta kama kanka ba, don haka ba ka da ra’ayin yi, ko kuma kana ganin cewa yakamata sai ta shigo gidanka ne tukunna kafin ka zage dantse da yi mata hidima, ko ma wanne dalili ne, hakan zai iya zama alamar ta rainaka ne musamman ma in ace ka mata bayanin dalilin da ya sa ba za ka iya yi mata ba.

Asali ba ka buƙatar yi mata kowanne irin bayani (ba dole ba ne dama), a ɗan lokacin da kuka ɗauka tare yakamata ta fahimci yanayin tattalin arziƙinka da irin ra’ayoyinka, idan ta fahimta kuma ta ƙi girmama hakan, to gaskiya ɗan uwa ba ka buƙatarta a matsayin mata, domin haka za ta c igaba da yi maka har bayan aurenku.

Ba ta tausayinka

Idan har ta san cewa ba ka da shi ne, kuma ta yi fushi har ta nemi rabuwa da kai a kan kayan sallah ka da ka ɓata lokacinka wajen neman a sasanta, ba ta tausayinka ne matuƙar kana iya ƙoƙarinka wajen kyautata mata da mata kyauta a lokacin da kake cikin yalwa.

Rashin tausayi daga wurin mace ƴar manuniya ce ga cewa za ka ƙare rayuwarka cikin baƙar wahalar ƙoƙarin yin sama da abun da ya fi ƙarfinka.

Wani lokacin ba rashin tausayin ba ne ba ma, ka kinkimo wacce ta fi ƙarfinka ne. Misali kana da dubu 5 da za ka yi wa mace hidima da shi, sai ka ji a gidansu akan bata dubu 10 kuɗin katin waya kaɗai, ta ina za ka iya fara burge ta a wannan halin?

Akwai alamar rashin jituwa

A rubututtukan da Malam Bahaushe ya ke yi a shafinmu na ‘facebook’ da ‘telegram’ ya tattauna matsalar rashin jituwa a faɗaɗe.

Idan kai mutum ne mai ra’ayi da ƙa’idoji, kuma ka tabbatar wa wacce za ka aura kai fa ga irin ra’ayoyinka da yadda kake kallon rayuwa, amma tare da hakan ta yi faɗa da kai a kan abun da ya ci karo da ra’ayin naka, to gaskiyar magana wannan ƴar manuniya ce da ke nuna akwai rashin jituwa.

Idan abubuwan da kuka yi imani da su sun saɓa, kamar irin saɓawar da ke tsakanin akuya da kwaɗo a wajen amfani da ruwa, to lallai ko kun yi aure duk irin soyayyar da kuka sha, zaman doya da manja za ku yi, wataƙila ma ku zama abun buga misali a wurin maƙota.

Don haka in tana girmama kayan sallah da ake yi wa ƴan mata, kai kuma ba ka girmama shi, ba ta dace da kai ba.

Alamar rashin jituwa

Idan tsabar rowa ce fa

Wanda shi kawai cire kuɗin ne ba zai iya ba ya yi hidimar sallah, abun bai ci karo da ra’ayinsa ba, ba kuma bashi da shi ba ne ba fa?

Gaskiyar magana in ba za ka iya yi mata hidima ba a dalilin maƙo, ba ka cancanceta ba, kuma bai dace a gare ka ba ka mayar da ita matarka ka je ka yi ta gana mata azaba. Don haka in kin yi faɗa da shi a kan wannan halin nasa kin fi shi gaskiya kuma bai kamata ki yi haƙuri da shi a haka ba.

Sai dai a wannan gaɓar yana da kyau mu lura cewa, wasu mazan kan ce ai ba a kamfen bayan an ci zaɓe, ma’ana za su zage dantse su yi duk wata hidima da take buƙatar kuɗi da lokacinsu kafin a yi aure, amma ana ɗaura auren sai a ga kamar ba su ba. Don haka yake da kyau ki lura ki tantance dan kar a miki sakiyar da ba ruwa ko kiyi gudun gara ki tad da zago.

Daga ƙarshe, zai fi kyautuwa a gare mu mu taƙaita ɓarnar dukiya da ƙoƙarin burge mutane kan abubuwan da mun tabbata sun fi ƙarfinmu. Kowa yayi rayuwarsa daidai ruwa daidai tsaki. Mu ba wa fahimtar juna muhimmanci sama da hirarrakin da ba sa ƙarar mu da komai a yayin hira da ƴan matanmu.

Wanne abu ne na manta ban shigar da shi ba cikin bayanaina? Ku cikata mana da shi a sashin tsokaci. Idan ra’ayinku ya sha bamban da nawa a kan wannan batun, zan so na ji naku ra’ayin. Mun gode.