Akwai wani bawan Allah a zamanin baya da Allah ya azurta shi da yara guda goma sha biyu (12). Sai ya zamanto ya fi son ɗaya daga cikin yaran nasa. Wannan soyayya da ja a jiki da yake nuna masa sai ta harzuƙa sauran yan’uwansa suka dinga zargin uban da rashin yi musu adalci har ma suka haɗe kai tare da yunƙurin hallaka ɗan lelen. Wannan ya faru ne da Annabi Yusuf kamar yadda Allah ya ba mu labari.

Idan Allah ya ba ka ɗaukaka a rayuwa dole ne za ka fuskanci ƙalubale ta hanyoyi da dama. Ɗaukaka kowacce iri ce tana janyo maka idon mutane, zuwan idon mutane gare ka kuwa yana sa wasu su dinga jin babu daɗi ko don su ma suna son irin abun da ka samun ya same su ko kuma suna ganin kai ba ka kai ka samu ba.

Mece ce Hassada

“Hassada ita ce tsana da ƙin jinin wani abun alheri da yake tattare da wanda ake yi wa hassadar” kamar yadda Malam Ahmadu ɗan Taimiya ya faɗa a littafinsa na cututtukan zuciya.

Hassada cuta ce ta zuciya da mahassadin ke fama da ita. Matuƙar wanda yake yi wa hassadar yana cikin jin daɗi da walwala to shi zai ci gaba da tabbata a cikin ƙunci. Ba kowanne mai hassada ne yake burin ya samu abun da yake yin hassadar a kai ba, wani in dai wanda yake yi wa hassadar zai rasa to buƙatarsa ta biya, wani kuwa yana son abun ya bar hannun wanda yake yi wa hassadar ya dawo wurinsa.

Hassada kala biyu ce, mai kyau da maras kyau. Mai kyau ita ce wacce za ka ga wani yana aikin alheri da dukiyar da aka ba shi, ko yana bautar Allah da Alƙur’anin da ya ba shi, sai ka yi fatan ka samu irin wannan abun don ka dinga irin aikin da yake yi. Wannan ta zo a hadisi ta halatta, don haka ma ba a saka gasa da rigegeniya wajen aikata alheri a matsayin hassada duk da suna ɗaukar ma’anar.

Hassada marar kyau mataki biyu ce, akwai wacce mutum zai dinga jin cewa don me wane zai samu ni ban samu ba, ni ne na fi cancanta na samu, kuma yana fatan abun ya kuɓuce daga wajen wanda yake yi wa hassada ya dawo wurinsa.

Akwai kuma wanda yana ganin tunda wane ya samu shi ma ya kamata ya samu, in bai samu ba zai ci gaba da jin haushin samun da wanda yake yi wa hassadar ya yi.

Meyasa ake yin hassada?

Idan na kawo maka wayar siyarwa da ba ka taɓa ganin irinta ba, ba mamaki duk farashin da na ba ka ka siye ta a haka. Amma idan da zan kawo guda biyu masu kama kuma farshinsu ya bambanta za ka samun ma’auninka kai ma kan yadda ya kamata farashin ya kasance.

Ban sani ba ko wannan misalin ya fita, abun da nake ƙoƙarin nunawa shi ne mutum kullum yana ƙoƙarin kamanta wani abu da wani kafin ya gane wanda ya fi. Na farkon saboda babu abun kamantawar ba yadda ya iya a misalin da na bayar a sama. Amma wanda aka kawo masa guda biyu ya samu abun da zai kamanta da shi. Wannan buƙatuwa zuwa ga son kamanta abubuwa da yake a dabi’a ta mutum masana halayyar ɗan’adam sun tabbatar da ita kamar yadda ya zo a littafin “predictably Irrational”.

Mai hassada yana ƙoƙarin kamanta kansa da wasu ne, daga lokacin da mutum ya fara tunanin cewa wane ya kai matsayi kaza ni ban kai ba, to in bai yi da gaske ba zai ɗauki layin hassada.

Abun nufi dai a taƙaice, ƙoƙarin kamanta kanka ko rayuwarka da rayuwar wani shi ne yake buɗe ƙofar gasa, kishi, jin haushi, ganin kai har ya kai ga matakin hassada.

Haɗama ma tana cikin abubuwan da suke jawo hassada, mutum ya samu amma yana son samun sama da haka don haka sai ya ji baƙin ciki in wani ya samu don samun wancen zai rage masa samun da zai yi a tunaninsa. Duk dai in muka lura abun yana komawa kan kamanta kai ko rayuwa ko wani abu da aka mallaka da na wani.

Wa ake yi wa hassada?

Ana yin hassada ne ga wanda ya samu ɗaukaka a mafi yawancin lokuta ɗaukaka ta mulki ko shahara musamman. Don Allah ya rufa maka asiri kana zaune lafiya da iyalinka ba lallai a maka hassada ba, amma daga sunanka ya ɗaukaka ka zama shahararre sai a fara cewa wane ne fa, da tare muke kaza da kaza da shi.

Abokai suna sahun gaba wajen yin hassada, saboda wanda bai sanka a da ba, ba lallai ya gane matsayin da ka samu ba balle har ya damu da kai. Amma ka ga wanda ya maka farin sani kuma kuke tare da daɗewa, in bai yi da gaske ba sai ya samu kansa a halin yi maka hassada.

Yahudawa sun zauna da larabawa na tsawon lokaci kafin Annabta, suna musu kallon gidadawa sai Allah ya turo Annabi daga cikinsu, don haka zuciyarsu ta kasa karɓar wannan suka fara hassada, me kake tunani in da ba su zauna tare da sun san su ba?

Illolin hassada

Ko da ace illar da hassada za ta yi wa mai yinta ita ce dawwamar da zuciyarsa cikin ƙunci wannan kaɗai ya ishe shi uƙuba, balle kuma ana bayyana shi a matsayin mai faɗa da wanda yake bayarwa ga wanda ya so a lokacin da ya so. Hassada tana hana al’umma ci gaba, domin duk wanda ya taka wani matsayi kuma yake da zuciyar yin alheri, in aka sako shi a gaba da hassada sai ka ga matsayin ya kuɓuce ba a amfana da komai ba.

Idan wanda ake yi wa hassada ba a ci moriyar samun matsayinsa ba me kuke tunanin mahassadi in ya taka wani mataki zai aikata? Ai ba zai so kowa ya raɓe shi ba bare ya lasa masa wani abu. Hassada tana haifar da gaba da ƙiyayya da raina juna, ƙyashi, mugunta, rashin taimako da jin daɗi in bala’i ya afka wa al’umma.

Hassada ba iya mai yinta take yi wa illa ba, wanda ake yi wa ma wani lokacin tana kama shi don haka Allah ya sauƙar da surah ta 113 ga Annabinsa da al’ummarsa don mu dinga neman tsari daga sharrin mahassada.

Ya ake daina hassada?

Wanda ciwon hassada ya kama kuma yake son dainawa sai ya dinga neman taimako a wajen Allah domin shi kaɗai zai iya yaye masa. Ya guji yawan zaman gulma da zama da magulmata. Ya dinga godewa Allah kan abubuwan da ya ba shi da bai ba wa waninsa ba (don kuwa yana da su). Ya taƙaita kamanta rayuwarsa da waɗanda suka fi shi in dai ba kan wani aikin alheri ba ne. Ya sani cewa mugun nufi da baƙar zuciya ba za su ba shi abun da yake nema ba shi ma. Shagaltuwa da abubuwan da aka sa a gaba, da rage bincike kan me wani yake ciki. Abu na ƙarshe kuma shi ne tsoron Allah, wanda ya ji tsoron Allah zai ba shi mafita zai kuma azurta shi ta inda ba ya tsammani.

Kaucewa mahassada

Tsira daga sharrin mahassada sai kariyar Allah, domin dole matuƙar za a samu ɗaukaka za su yi. Don haka sai mutum ya dinga addu’o’in neman tsari, da zikirori. Wanda ba ya so a masa hassada shi ma kar ya yi wa wani. Mutum ya taƙaita bayyanawa duniya halin da yake ciki musamman lokacin da ya samu wani ci gaba, hakan zai taimaka ƙwarai. In kana tare da mutane a wajen aiki ko kasuwa ko ka fi su komai (wanda zai yi wuya) wani lokacin ka dinga shigar da wauta cikin lamurranka don kada idanun na sama da kai ya dawo kanka su taka ka, sa’anninka kuma su maka hassada.

Wasu ba sa damuwa da aikata abun da zai tara musu maƙiya ko mahassada, idan da Allah yana so mu tara maƙiya da mahassada ne da bai turo mana Annabin rahama ba, bare ya saukar mana da saura sukutum ta neman tsari. Kar ka ruɗu da cewa hassada ga mai rabo taki ce ga dinga yin sakaci, ko a maganar ma ba ka ji an ce “ga mai rabo” ba, ke nan in ba ka da rabo za ta iya raba ka da hankali ko ma rayuwarka, tabbas “Ido gaskiya ne”!

Ina ganin ko a haka waɗannan bayanan sun tattara abubuwa a dunƙule kan hassada, duk da haka zan so na rufe da wani tsokaci. Mutanen da ba sa son gaskiya wani lokacin suna fassara gyaran da ake ƙoƙarin yi musu da hassada. Misali, wani ya ba ni labarin wani da ya samu maƙocinsa kan ya ja wa ɗansa kunne kan abokan da ya ga yana alaƙa da su sai kawai mutumin nan ya hau faɗa yana cewa ana yi wa yaronsa hassada, kuma har ya je ya samu yaron ma ya ba shi labarin abun da ya faru. Ka ga wannan bai fahimci hassada ba, domin da ya fahimta da zai san cewa yaron nasa bai da abun da za a masa hassada, tunda daga ƙarshe ba a jima ba sai ga shi an kulle yaron ya je belinsa.

Allah ya ba mu dacewa ya kare mu daga yin hassada, ya tsare mu daga sharrin ma su yinta.