A ƴan watannin nan abubuwa da dama na ɗaukar hankalina, ɗaya daga cikin abubuwan shi ne yadda yarinyata take ƙoƙarin kwaikwayon duk abun da muke yi. In taga na sa hannaye biyu a baya ina zarya a ɗaki sai ta bi ni tana gwadawa, in ta ji na furta wata kalma sai ta fara ƙoƙarin kwaiwakwayona a yadda na furta. Idan ta ga littafi a hannuna ita ma sai ta ɗauko wani ta zauna, in waya ce sai ta yi ƙoƙarin ƙwacewa don ita ma ta danna. Ko rubutu nake ban isa na tashi na bar abun rubutun a wurin ba, in kuwa na yi gangancin bari zan dawo na tarar ta cika takardar da irin nata rubutun!
Wannan ya sa na fara tunanin kan yadda ta koyi zama, rarrafe, tafiya har ma da furta wasu ƴan kalmomi. Duk waɗannan abubuwan na lura ta koye su ne ta hanyar gwadawa da kuma yi kullum, wannan kuma ita ce hanya mafi sauƙi wajen koyon komai a rayuwa.
A ɗabi’a haka Allah ya yi halitta, muna zuwa duniya ba mu san komai ba, a hankali muke koyo daga wajen iyayenmu. Bayan mun yi wayo mu ci gaba da koyo daga abokai da malamai da sauran mutanen gari.
Idan har mun yarda wannan ce hanyar da muke koyon komai da ita meyasa yanzu muke ganin akwai hanyar da ta fita?
Ina nufin, don me muka yarda cewa da karanta littafi kan rayuwar tsirrai ko dabbobi za mu zama ƙwararru a fannin noma? A wanne dalili muka ɗauka cewa don muna karanta littafi kan kasuwanci za mu wayi gari rana ɗaya mun zama shahararrun ƴan kasuwa?
Abun a bayyane yake ƙarara, duk lokacin da aka zaunar da mu a aji da nufin a koya mana abu daga cikin littafi, kuma aka tsaya iya nan, kamar ana nuna mana cewa in mun iya daga littafin mun koya kenan. Wannan ne ya sa muke tunanin za mu iya koyon abu ba tare da mun taɓa gwada shi ba.
Mutane da dama sun tashi da wannan tunanin na cewa in sun karanta ya kamata ace sun iya kawai ko da ba su taɓa gwadawa ba, don haka duk ranar da suka zo gwadawa suka yi asara ko bai fito musu yadda suke so ba sai su watsar su fara neman hujjojin kare kansu.
A yadda rayuwa take shi ne, ilimi haske ne, zai dinga haska maka inda za ka sanya ƙafarka ne, amma ya yi kaɗan ya maye gurbin takunka. Za ka zama malami ƙwararre ne ta hanyar koyarwa kullum. Za ka zama marubuci ne ta hanyar rubutu kullum. Za ka zama maƙeri ne ta hanyar yin ƙira kullum. Za ka zama ɗan siyasa ne ta hanyar yin siyasa kullum. Za ka zama likita ne ta hanyar yin likitanci kullum. Za ka zama ɗan kasuwa ne ta hanyar saye da sayarwa kullum.
Kada ka ɗauka don an ba ka shaidar cewa ka karanta fanni kaza shikenan ka gama, ina! Ba ka ma fara ba, wannan ba ka shaidar shi ne mafari, ya rage naka in ka fito duniya ka koya ta hanyar yi yau da gobe.
Inda wannan yake fitowa ƙarara shi ne a wurin da ake koyar da aikin hannu, za a koyar da yaro abun tun daga tushe, ana sa shi yana yi jifa-jifa har a kai lokacin da zai dinga yi kullum, zuwa wasu shekaru sai ka ga ya zama ƙwararre a wannan fannin.
Duk da cewa mutane kala-kala ne a wajen koyo, kowa akwai hanyar da ya fi saurin koyo, in muna son samar da masana waɗanda suka san abun tun suna ƙanana sai mun dage da gwada abubuwan da muke koyo a aji kamar yadda yake a jadawalin karatukanmu. A matsayina na wanda ya karanta engineering, tutuni na daina kallon kai na a matsayin engr, saboda ba shi ne abun da nake yi kullum ba, domin shi ilimin ba a shaidar yake ba, a abun da ka iya ne kuma kake yawan yi, ni kuwa koyarwa da rubutu ne abun yi na.
Wata illa da ba ma lura da ita shi ne, a lokacin da muka dage da yin wasanni, ko kallon wasannin, ko kallon fina-finai, ko hirar ƴan siyasa, ko zaman kashe benci, ko danna waya, ko karanta labarai, ko karanta litattafai, da sauransu kamar mun ɗauki hanyar ƙwarewa ne a waɗannan abubuwan ba tare da mun shirya ba. Illar hakan kuma shi ne za ka zama ƙwararre a kasuwancin wani, wanda hakan zai ja ka rasa ƙwarewa a naka. Ba kuwa asarar da ta kai wannan, in dai ba dama kana da sha’awar ɗaukan layin ba ne dan haka kake yi don koyo.
An rubuta kuma an yaɗa ranar 27/11/2022.