A kashi na farko na wannan rubutun, na bayyana wasu halaye guda uku (3) cikin shida (6) da na ce tilas kowanne matashin bahaushe ya runguma daga yau. A wannan kashin zan ƙarasa mana ragowar ukun, domin karanta ukun farkon sai ku danna nan, don samun kyakkyawar fahimtar rubutun tun daga tushe.

Girmama Manya

Abun takaici ne ka ga mutum ya zaƙalƙale yana zagin wani a media ba tare da duba girma, mutunci, daraja, ilimi ko shekarunsa ba don kawai suna da bambancin ra’ayi. Rashin girmama manya ba a iya dandalin sada zumunta ba ne yake faruwa, sai dai na lura kamar a dandalin sada zumunta matasa sun fi cin karensu babu babbaka

A ƴan kwanakin nan na karanta labaran wasu da saboda tsokaci a wani rubutu dama ta kuɓuce ko ta kusa kuɓuce musu. Abun shi ne a matsayinka na matashin da ya san ciwon kansa, hayaniya kowacce iri ce ba taka ba ce. Domin hayaniya aiki ne na jahilci, to kai me ya same ka da za ka saukar da kanka zuwa ga matakin jahilai?

Girmama mutane hali ne mai kyau da kowanne matashi yake buƙata. Idan ya zama mutum ya ɗabi’antu da girmama manya to fa yana ba da adireshin in da ya fito ne da irin tarbiyyar da ya samu. Gaskiya ne masu ɗaukar aiki a yanzu sukan bibiya shafukan sada zumunta don su san wanne irin mutum ne suke shirin ɗaukar aiki.

Misali, akwai wani kafinta da kwanakin baya labarinsa ya yi ta bazuwa kan yadda ya kusa cinye wa wasu kuɗi ba tare da ya musu aiki ba, idan ka ga wannan labarin za ka yarda ka yi kasuwanci da wannan mutumin? Ko shakka babu ba da garaje ba. Kamar haka ne masu nuna halin rashin daraja ga dattawa da masu mutunci ake ganinsu.

Akwai mutumin da ana faɗarsa da rashin ba wa mutane daraja za a tuna shi, ka ga kuwa ko kai ne wata dama ta biyo ta hannunka wacce zai amfane ta ba za ka so ya samu ba. Halin girmama mutane abu ne mai asali a addini da al’ada. An hore mu da girmama mutane da kaucewa zakkewa mutuncinsu.

Ko ba dan rasa wata dama ba, rashin girmama manya kan sa a rasa albarka, domin wani ba a san matsayinsa a wurin Allah ba duk da ana masa kallon ƙasƙantacce. Wanda ke girmama manya lallai zai kasance cikin alheri dumu-dumu, zai dinga samun alfarma da ci gaba a rayuwarsa, kuma sai an fi saurin taimaka masa in yana cikin halin neman taimako. Sai dai wannan baya nufin ka girmama mutum kaɗai don kana ganin zai sama maka aiki, ko zai ba ka jari, a’a, ya zamar maka jiki kawai, kuma don Allah kake yi, domin saɓanin haka, za a zo gaɓar da mutum zai gaji ya watsar in buƙata ba ta biya ba.

Ƙulla Alaƙa Da Mutane

Wai suka ce “your network determine your net worth” yawan mutanen da kake mu’amala da su yana da alaƙa da arzikinka. Abun da ake nufi da wannan shi ne alfarma da sanayya tana aiki a ko’ina. Akwai abun da ake cewa in kana da kyau ka ƙara da wanka, misali a samu mutane biyu duk sun cancanci abu, a cikinsu wanda yake da sanayya ko wani ya tura sunansa shi za a fi gabatarwa.

Mutane da yawa in sun ji maganar “connection” sukan kai hangensu nesa ne, irin ace sun san wani babba; babban attajiri, dan siyasa, malami, mai sarauta ko mai mulkin siyasa. Su a ganinsu sanin waɗannan shi ne kaɗai zai ba da damar a dama da su.

Taƙaita ma’anar ƙulla alaƙa da mutane a kan manyan mutane kaɗai rage wa abun ma’ana ne. Akwai damarmakin da a wurin taro ne za a haɗu da mutum ya yi silarsu. Misali a ce an shirya wani “workshop” ko “conference” ko wani taron ƙarawa juna sani, to ka ga duk mahalarta taron za su zama suna da tunani ne ko buri iri ɗaya “like-minded”, ke nan cakuɗuwa da su da shiga cikinsu zai ba mutum damar faɗaɗa jama’ar da yake alaƙa da su, wanda bai san kuma alherin da hakan zai iya kawo masa ba.

Ba sai iya wajen taro ba, ko a dandalin sada zumunta ana haɗuwa da mutanen da suke zama “network” a gaba. Hatta cikin abokai da sa’anni da aka taso tare akan samu “network”. Abun da ba a so shi ne ya zama tun yarinta har tsufa da “network” ɗin mutum yana nan ba canji, ba ya samun sabbin dabaru daga waje, ba kuma ya hangen ma wani zai iya masa wata rana a gaba.

Babban abun da matashi zai duba wajen ƙulla alaka shi ne wanda ya san me yake yi, ko da ba fannin aiki ko sana’arku ɗaya ba, matuƙar ya san me yake to za ka amfana da shi. Shi wanda ya san me yake yi alaƙa da shi tana da riba sosai, ko da bai ba ka kuɗi ba, zai amfane ka da shawarwari, zaburarwa, nuna maka hanya, tare da wayar da kai. Bayan haka kuma cikin mutanen da yake alaƙa da su wataran in wata buƙatarka ta tashi zai gane cewa da wane ya kamata a haɗa ku.

Mu fahimci cewa, ba dole ne kowa ya zama babba ba, ba kuma lallai sai kowa ya san manya ba, sanin me kake yi da ƙulla alaƙa da mutanen da suka dace shi kaɗai zai iya kai ka zuwa kowanne mataki da kake son zuwa.

Akwai wani abokina da kamfaninsa yake ayyukan da suka shafi “technology”, yana ayyuka wa gwamnatin tarayya da wasu jihohin. Abun da na sani game da shi shi ne, bayan ƙwarewa da yake da ita, duk inda ya shiga yana ƙulla alaƙa da mutane, a cikin hirar in ta kama za su iya sanin irin ayyukan da yake yi da baiwar da Allah ya masa, daga nan sai ka ga in dama ta samu sun tuna da shi. Lallai in kana da kyau ka ƙara da wanka, kuma sabo da maza jari in ji bahaushe.

Addu’a

Wata rana ina duba shafukan sada zumunta sai na ci karo da bidiyon wani bawan Allah da yake ba da sirrin addu’o’i da suka fito daga bakin manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi. A cikin addu’o’in da ya bayar sai wani ya ce ya yi addu’ar ya samu aiki a wata babbar ma’aikata. To wani da bai yarda ba sai ya yi tsokaci da cewa gaskiya sai dai in dama yana da hanya a wurin..

Matasan hausawa a wasu lokutan sukan yi wasa da addu’a musamman waɗanda suke ganin sun waye sun sha boko, suke ɗaukar cewa komai ƙoƙarin mutum ne da wayonsa ke ba shi. Akwai wani da ya ce shi bai yarda istigfari yana kawo arziki ba, a ganinsa malamai ne ke wasa da hankalin mutane kawai.

Ire-iren waɗannan mutanen ana samun su yanzu, ko ba su bayyana ba, aikinsu yana nuna ba su yarda da tasirin addu’a ba.

A halin da ake ciki matashi ba shi da wani makami da ya wuce addu’a, domin mai bayarwan ake roƙo kai tsaye, shi kuma taskokinsu ba su da iyaka, ba shi da rowa, yana bayarwa ga kowa har wanda ya kafirce masa ba ya hana shi.

Akwai abubuwa da yawa da suke faruwa da rashin addu’a ke haifar da su. ko aiki ko sana’a mutum yake bai tsira ba, bare kuma mai zaman banza. Akwai mutanen da za ka tsira daga sharrinsu ne kawai ta hanyar addu’a, domin suna ganin su ne suka cancanci wannan matakin da ka taka ba kai ba. Kuma za su yi duk mai yiwuwa don jawo ka ƙasa.

Addu’o’i suna nan ba adadi, masu dunkulalliyar ma’ana, ga saurin biyan bukata. Misali wanda ya yi wa Allah kirarin “Ya Allah ina roƙonka don lallai na shaida kai ne Allah, kai kaɗai, wanda ake nufa da buƙata, bai haifa ba ba a haife shi ba, kuma ba shi da wani sa’a na daban” Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi ya ce duk wanda ya faɗi wannan ya roƙi Allah da kalmomin da in dai an roƙe shi yana bayarwa.

Akwai irin su “hasbiyallahu wa ni’imal wakil”, “la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” da sauran addu’o’in neman agajin gaggawa da suke aiki kamar yankan wuka. Lallai babu abun da zai gagari Allah, sai dai in ba a roƙe shi da yaƙini ba, ko kuma ya yi nufin jarraba mutum.

Malamai suka ce akwai ƙaddarar da ake jingina ta da wani abu, misali Allah zai iya ƙaddara mutum zai samu wani alheri ko ya nema ko bai nema ba. Zai iya kuma ƙaddara cewa in bawa ya yi addu’a sau 5 zai samu abu kaza, in bai yi ba kuma shi ke nan ya zama ba rabonsa ba. A matsayinka na bawa da ba ka san ƙaddararka ba, yawan addu’a zai kawo maka alheri marar adadi, zai kuma tsare ka daga abubuwan da ba ka sani ba na cutarwa. Haka nan kuma za ka fita daga cikin waɗanda Allah ke fushi da su kan rashin roƙonsa.

Ba iya halayen ba ke nan, amma tunda na taƙaikta a kan shida, a nan zan dasa aya. Kamar yadda na yi bayani a baya, hali ba dole sai an canza shi lokaci guda ba, ana iya bi sannu-sannu kwana nesa don samun ɗorewarsa.

A cikin halayen nan wanne ne kuke sakaci da shi a da a yanzu kuma kuka ɗaura ɗamarar dagewa a kansa? Sai mun ji daga gare ku.