A yadda rayuwa take sauyawa yanzu, samun kanka a wannan zamanin a matsayin matashin bahaushe yana cike da ƙalubale. Sanin cewa halaye masu kyau da za a juri yin su yau da gobe suna iya canja rayuwa yana da matuƙar amfani.
A wannan lokacin matashi yana buƙatar ya nutsu ya san me ake ciki, ya san ina aka dosa, ya san ina ya kamata shi kuma ya dosa. Duk matakin da mutum zai kai a rayuwa akwai tasiri na halaye da dabi’unsa. Wasu halayen ma su sukan kai mutum wani mataki, wasu kuma su suke rike shi in ya samu kai wa ga matakin, akwai kuma masu iya jefo shi ƙasa daga sama.
Marubuci James Clear a cikin littafin “Atomic Habits” ya nuna cewa halaye suna da matuƙar tasiri a wajen ginuwa ko rugujewar rayuwa. Daɗin daɗawa kuma ya bayyana cewa ba dole sai an sauya lokaci guda ba, yi kaɗan-kaɗan ko farawa sannu-sannu yana ba da sakamako na ban mamaki.
Tashi Da Wuri
Bahaushe ya ce da sassafe ake kama fara. Wannan magana gaskiya ce, kuma a matsayinmu na musulmai mun san albarkar dake cikin safiya. Ban sani ba ko ni ne ban gama sanin yadda ake jin daɗin duniya ba, amma abun yana ba ni mamaki da takaici na ga matashi ya share awanni da safe yana tiƙar bacci da hujjar cewa bai kwanta da wuri ba.
Lokacin da muna makarantar sakandare, kafin a fara sakalta yara, ba ka isa kandinka (senior) ya bar ka kana baccin safe ba a matsayinka na kwaɗonsa (junior). Ba iya kai ba ma, ko wucewa ya zo yi ya ga wani kwaɗo na bacci zai tashe shi, babban uzuri ne kawai zai hana shi ba shi bokiti ya ɗebo masa ruwa.
Duk abun da mutum zai yi matuƙar ya fara sassafe zai ga alheri sosai a cikin hakan. Misali, wanda ya tashi ƙarfe huɗu (4) ko biyar (5) na safiya, zai samu damar yin nafila, zai yi karatun Alƙur’ani, zai kuma tsara mai zai yi a wunin tun kafin gari ya waye.
Idan mutum ya tsara yininsa sassafe alama ce dake nuna zai cimma abun da kaso mafi yawa na mutane ba za su iya cimmawa ba a wannan yinin, domin ba kowa ne ya damu da ya yi tsari ba, ba ma kowa ne ya san me zai yi a ranar ba. Me kuke tsammanin wanda yake shiryawa ya cimma a kowanne yini bayan shekaru zai cimma in ya doge a haka?
Duk abokaina da na sani masu zarce sa’a a makaranta, tun daga sakandare har jami’a, sassafe suke fita aji karatu, kafin gari ya gama wayewa sun samu abun da suka samu.
Babbar illar da za ka yi wa safiyarka shi ne ka tashi da wuri ka kunna kallo, ko buga wasa a waya, ko shafukan sada zumunta, ko dai duk wata shiririta da ba ta da amfani. Abun shi ne, kamar yadda Bahaushe ya ce da muguwar rawa gwamma ƙin tashi, da ka tashi ka yi abun da zai bunƙasa wani, kai kuma ya danƙwafar da kai, gara ba ka tashi ba. Misali, masu shirya fim ko masu buga ƙwallon ƙafa sana’a suke yi, kuma ba sa wasa da duk abun da zai kawo musu kuɗi a sana’arsu, to kai me zai sa ka sadaukar da safiyarka don sana’ar wani ta ci gaba alhalin ba wani amfani za ka samu ba.
Tashi da wuri ba iya tashi sassafe ba ne, har ka fahimci rayuwa da inda ya kamata ka sa gaba duk shi ma tashi da wuri ne. Wanda ya gane kansa tun yana matashi mai jini a jika ba za ka haɗa shi da wanda sai da rauni ya zo masa ya fahimci wane ne shi da manufar rayuwarsa ba. Wanda yake neman ƙarin bayani game da sanin kai don rayuwa yadda ya dace akwai ƙaramin littafina da ya amsa tambayoyi da yawa a wannan babin, za ku iya sauke shi a wayoyinku da danna “Ka San Kanka”.
Dogaro Da Kai
Zama banza tun a lokacin da duniya take zaune ƙalau ba na matashi ba ne. Idan zaɓaɓɓun Allah cikin halitta (Annabawa da Manzanni) za su kasance suna da hanyar neman na kansu, to kai wane ne da za ka zauna jiran a samu a baka.
Ba lokacin da mutum ya fi buƙatar ya dogara da kansa kamar lokacin da ya zama matashi ya fara sanin ciwon kansa. A wannan ƙadamin ne mutum yake zaɓen irin rayuwar da yake son yi. Idan ɗan makaranta ne to wataƙila ya gama ko yana gab da gamawa, idan ya gama zai fara tunanin ya tsaya da ƙafarsa, daga nan zai iyali, shikenan girma ya zo, dole ya ɗauki nauyin rayuwarsa, ya kuma ɗauki nauyin ta waɗanda suka rataya a wuyansa. Wanda ba shi da abun yi yaushe zai yi duk waɗannan abubuwan?
Na san mutanen da ake guje musu cikin abokansu saboda sun ɗaukar wa kansu rayuwar gayu da jin daɗi, amma sun ƙi yin sana’a. Wanda fa ya huta yana yaro ba zai huta ba bayan ya girma in ji masu iya magana.
Idan aiki mutum yake nema, ba laifi, ya ci gaba da neman aikinsa, amma kar ya yi gangancin zama ba shi da hanyar da taro da sisi za su ke shiga masa walau a wata ko kullum-kullum. Wannan yanayin yana jefa mutane cikin ciwon damuwa har su zo ma su saduda da rayuwa su kasa tsinana komai.
Dogaro da kai ba dole sai da aikin kamfani ko na gwamanati ba, aikin hannu yana daga cikin hanyoyi mafiya sauri na samun kuɗin shiga. Ita sana’ar hannu duk da cewa kyanta a ce mutum ya fara tun kafin ya kawo munzali, za mu fahimci cewa ba ta buƙatar jari na kuɗi, iyaka ubangida ƙwararre, yalwar lokaci da jajircewa take buƙata. Wanda ya haɗa wannan cikin shekara biyu (2) in Allah ya sa masa albarka za ka ga shi ma ya tsaya da ƙafarsa.
Yanzu a zamanance ma hanyoyin koyon aiki ko “skill” sun yalwata, mutum zai koyi “digital skill” yana daga gida kuma ya tallata kansa a san shi a ba shi aiki ya yi a biya shi ba tare da ya je ko’ina ba.
Wanda kuma yake da jari, ko wanda zai iya buɗe masa wurin sana’a to shi abun zai zo masa da sauƙi, kawai zai duba me ake ƙishirwarsa ne ya fara saidawa. Ƙalubalen da matasa suke fuskanta a wannan bangaren shi ne samun mai yarda da su har ya buɗe musu shago ko wurin sana’a. Wannan kuma yana da alaƙa da irin rayuwar da mutum yake yi a matsayinsa na matashi. Idan an san ka da zafin nema, gaskiya, amana da rashin mutuwar zuciya, akwai wanda tun kafin ka nemi jari zai ba ka, wani kuma zai jira sai ka nema tukunna. Abun shi ne, duk lokacin da ka nemi taimakon jari wanda yake da halin ba ka ya fa fi ka sanin wahalar kuɗi, sannan ya fi ka son kansa, don haka abun da zai fara dubawa shi ne shin ta ina zai ƙaru da kai? In ya ga babu mamora a tare da kai ba zai ba ka haɗin kai ba, don kaucewa asara.
Damuwa Da Ilimi
A shekarun baya an yi ta ce mana nan gaba ko sayar da rake sai kana da shaidar kammala karatu kafin ka samu damar yi. Wannan ya sa wasu mutanen suka yi ta barin sana’ao’insu suna shiga boko, sai sun gama kuma sai su ga dai to fa sana’ar nan tasu ita ce dahir. Ban sani ba ko wannan yana daga cikin dalilan da ya sa ake yi wa masu digiri izgilanci ba a yanzu.
Maganar gaskiya ita ce saɓanin yadda muka ɗauka, boko ba sana’a ba ce, don ka yi boko ba ya nuna da karatun za ka ci abinci. Asali ya kamata tun mutum yana firamare a fahimtar da shi cewa ilimi haske ne da zai ci gaba da haska masa in da zai sa ƙafarsa a rayuwa, ba wai hanyar cin abinci ba. Ɗaukar ilimi a matsayin hanyar cin abinci ya sa da dama aka fi mayar da hankali wajen yin karatun a maimakon samun ilimin.
Wasu ba su san ma akwai bambancin karatu da ilimi ba, ilimi ya tattara sanin Allah da manzonsa mai tsira da aminci da yadda za a rayu a amfani kai a amfani al’umma. A bisa wannan ma’anar manomi yana da ilimin noma ko da bai karanci harkokin noma ba a makaranta, kamar haka nan mai sana’a za a ce yana da ilimin kasuwanci da neman kuɗi.
Karatu kuwa an fi ba shi ma’anar da take mayar da hankali kan hanyar da aka samu ilimin (formal ko informal) shiyasa in ka gama makaranta sai dai a kira ka “educated” (wanda ya je makaranta) ba “knowledgeable” (mai ilimi) ba, domin ilimi har gogewa sai ta shiga cikin ma’anar. Wannan fassarar ta ilimi malaman musulunci ne suka yi ta, shiyasa ma wani daga cikinsu yake ganin duk abun da ba littafin Allah da sunnar Manzo ba, zamantakewa da ilimin magani ba to duk ruɗun duniya ne kawai.
A matsayin ka na matashi a Najeriyarmu ta yau, babban gatanka shi ne neman ilimi, kuma za ka nemi ilimi ta hanyar da kake ganin tafi dacewa da kai, walau a makaranta ko a gida ko a kasuwa. Karatu ne wanda za a baka shaida ko wanda babu shaida, kai dai buƙatarka ilimin domin samun wayewar kai game da rayuwa da zamani.
Hatta addini in ba ka tsaya ka nemi ilimi ba ko, to malamai sun dinga gwara maka kai ke nan. To wannan ma fa ke nan da ake ganin ya fi alaƙa da lahira, kuma ba ya canjawa, ina ga abun da ya shafi duniya wacce muke rayuwa cikinta yanzu, kuma take saurin sauyawa.
Za ka nemi ilimi a ɓangaren fannin da kake da ƙwarewa ko kake son ƙwarewa, zamantakewa, mu’amala da mutane, tarihi, sanin halayya, mulki da iko, kasuwanci da neman kuɗi, gwargwadon buƙatarka. Wannan ilimin kuma zai iya zama a makaranta ka koya, ko yau da gobe ce ta koya ma, ko a littafi ka karanta, ko ma saurara ka yi ana bayani.
Neman ilimi musamman ta hanyar karance-karance ba ƙaramin amfani gare shi ba ga ƙwaƙwalwa, wasu suna ganin ma shi ne babban abincin da za ka ba ƙwaƙwalwarka. Mu fahimta, ba iya tuwo ne abinci ba, abun da muke karantawa, sauraro, da hulɗa da shi yau da gobe duk abinci ne, amma na zuciya da ƙwaƙwalwa. Wanda ke son inganta lafiyarsu sai ya dage da ba su abun da ya dace.
Ilimi ba ya zama ilimi sai ana aiki da shi, wanda ba ya aiki da abun da ya koya bai gaza wanda bai san abun ba. Domin kamar yadda na faɗa a farko shi ilimi haske ne, amfaninsa ya haska, to in ya zamto ba aiki me zai haska ke nan? Don haka yake da muhimmanci a yi amfani da shi a yadda ya dace.
Rubutun ya yi tsawo sosai, ba kowa ke da juriyar karatu ba, zan kawo ragowar abubuwan a kashi na biyu. Zan so na ji in kun ƙaru da wani abu a wannan rubutun, da kuma matakin da za ku ɗauka don inganta rayuwarku a matsayinku na matasan Hausawa. Mu haɗu a kashi na biyu.
Trackbacks/Pingbacks