by Ahmad sani | Apr 15, 2024 | Hausa
A ƴan watannin nan abubuwa da dama na ɗaukar hankalina, ɗaya daga cikin abubuwan shi ne yadda yarinyata take ƙoƙarin kwaikwayon duk abun da muke yi. In taga na sa hannaye biyu a baya ina zarya a ɗaki sai ta bi ni tana gwadawa, in ta ji na furta wata kalma sai ta fara...