YADDA ZA KA DAINA DAMUWA DA YA MUTANE SUKE KALLONKA

YADDA ZA KA DAINA DAMUWA DA YA MUTANE SUKE KALLONKA

“Ɗabi’a ce mai matuƙar kyau mu dinga lura da yadda mutane suke ɗaukarmu. Wannan ba wani abu ba ne a game da mutum. Muna son jin mu kusa da mutane kuma muna damuwa da halin da suke ciki, a bisa wannan dalilin muke lura da yadda suke tunani game da mu da kuma yadda...
NEMAN KUƊI KO HAƊAMA?!!!

NEMAN KUƊI KO HAƊAMA?!!!

Ya zo a tarihin sahabbai cewa, Annabi tsira da aminci su tabbata gare shi ya haɗa ƴan’uwantaka tsakanin mutanen madina da muhajirai lokacin da aka yi hijira. Mutanen Madinan sun kasance duk wanda aka haɗa su da shi su kan raba dukiyarsu da gidajensu wasu ma har da...
Skill ko Degree?

Skill ko Degree?

Wani “comment” da na taɓa karantawa shekarun baya tun kafin dambarwar degree da skill ta yawaita ya yi matuƙar tsuma ni, kuma na daɗe ina tunaninsa. Ba zan iya tuna inda zan same shi ba amma abun da mai tsokacin yake cewa shi ne “da kuna cewa ko tallen rake sai mai...
TALIYA CE SANADI…

TALIYA CE SANADI…

Daga Ahmad Sani   Duk lokacin da wani mummunan abu ya faru a wannan ƙasar tamu a ɗan tsakanin nan za ka ji mutane na cewa ai taliya ce sanadi. Mutanen da ke wannan furucin ba suna yi ne don alhini ko jin tausayi kan abun da ya faru ba ne bare waɗanda ya faru da...
HANYA MA FI SAUƘI TA KOYON KOMAI

HANYA MA FI SAUƘI TA KOYON KOMAI

A ƴan watannin nan abubuwa da dama na ɗaukar hankalina, ɗaya daga cikin abubuwan shi ne yadda yarinyata take ƙoƙarin kwaikwayon duk abun da muke yi. In taga na sa hannaye biyu a baya ina zarya a ɗaki sai ta bi ni tana gwadawa, in ta ji na furta wata kalma sai ta fara...