ATIKA TA SAMU KOMAI… SAI DAI TA RASA KANTA

ATIKA TA SAMU KOMAI… SAI DAI TA RASA KANTA

Cin nasara a rayuwa abu ne da kusan dukkaninmu muke muradi. Amma me kuke tsammani idan cin nasarar da muke ta faɗi tashin samu ta zo a gagarumin farashin da ba mu taɓa zato ba?Atika da daɗe tana jin ana faɗin cin nasara yana buƙatar gagarumar sadaukarwa. Kasantuwar ta...
SANA’AR HANNU AIKI KO KASUWANCI?

SANA’AR HANNU AIKI KO KASUWANCI?

Gen Z ko Indomie generation kamar yadda ake kiran su, da mu kanmu millenials mun samu kanmu a cikin ruɗani a wannan zamanin. Ba ina son cewa a lokutan baya babu ruɗani ba, a’a, amma in ka duba halin da muka tsinci kanmu a dandalin yanar gizo da shafukan sada zamunta...
MEYASA AIKIN YI YAKE WAHALAR SAMUWA?

MEYASA AIKIN YI YAKE WAHALAR SAMUWA?

Abarba tana daga cikin ƴaƴan itacen da nake matuƙar jin daɗin tauna su, musamman idan na ci karo da mai zaƙi sosai. Ko jiya ma (a 2022 lokacin da na yi rubutun) da na zo wucewa ta kusa da wani mai abarba, sai da na tsaya ya yanka min wacce zan shiga gida da ita.A...
DALILAI BIYAR (5) DA ZA SU HANA A BA KA JARI

DALILAI BIYAR (5) DA ZA SU HANA A BA KA JARI

“Na rasa meyasa babana ya ƙi ba ni jari, in da zai ba ni jari ai da yanzu nima ina ta jujjuya kuɗin a business’’ ya ce da abokin tattaunawarsa.Watarana na je wani shago zan yi siyayya, sai na tarar da wani matashi suna tattaunawa da wani, yana ƙorafi a kan yadda wani...
ABUBUWAN TAKAICI GUDA 10 DA MATASA KE YI A LOKACIN AZUMI

ABUBUWAN TAKAICI GUDA 10 DA MATASA KE YI A LOKACIN AZUMI

Matasan su ne ƙashin bayan ci gaban kowacce al’umma, gyaruwar su alamun goben jama’a za ta yi kyau ne, akasin haka kuma na nuna al’umma ba ta da gobe. Ban san ta yadda aka yi matasa suka samun tunanin cewa gobensu na hannun tsofaffi ba, don haka suka bar musu wuƙa da...
ABU 4 DA ZA MU KOYA DAGA MAZAJEN NOVELS

ABU 4 DA ZA MU KOYA DAGA MAZAJEN NOVELS

“Angona na shirya ni ma, yau tare za mu tafi ofis” Amaryar ta ce da shi.“Kowa yana barin matarsa a gida sai ni ne zan ɗauki mata goɗai-goɗai na tafi ofis da ita?” Angon ya ba ta amsa.“Haba masoyi, ba za ka yi irin na mazajen novels ba, haka suke yi fa” ta sake...
DALILAI 2 DA SUKE SA A MAKA BIYAN WULAƘANCI A WURIN AIKI

DALILAI 2 DA SUKE SA A MAKA BIYAN WULAƘANCI A WURIN AIKI

A ƴan kwanakin nan na lura mutane suna ta yin tsokaci kan malaman islamiyyu da yadda ba a biyan su haƙƙinsu yadda ya kamata, har ma wasu suna kiran ustazai da su tsaya da ƙafafuwansu (ma’ana su nemi kuɗi). Ba iya makarantun islamiyya ba, hatta ƙananun makarantu masu...
ƊABI’A GUDA ƊAYA DA TA FI KAIFIN BASIRA

ƊABI’A GUDA ƊAYA DA TA FI KAIFIN BASIRA

Lokacin da ina makarantar sakandare masu ƙoƙari iri biyu ne, waɗanda ana yi a aji suke ganewa in sun dawo kuma su yi ta bita, da waɗanda ba sa iya ganewa tun a ajin amma akwai su da nacin karatu.Da na shiga Jami’a ma dai haka na taras, har ma a nan na san...
LABARIN WASU MATA GUDA BIYU

LABARIN WASU MATA GUDA BIYU

Wannan wani labari ne da yake kamanta wasu mata guda biyu, kowacce mijinta daban kuma suna rayuwa a gidaje mabambanta.Macen farko:Ta tashi da Asuba ta yi sallah, sannan ta shirya girki wa mai gida da yara.Mace ta biyu:Ta yi sallahr Asuba gab da lokacin sallahr zai...
YADDA ZA KA GANO BAIWARKA

YADDA ZA KA GANO BAIWARKA

Ba kasafai nake iya tuna abubuwan da na yi a yarinta ba kamar sauran mutane, ko da yake da yawa ma ba sa iya tunawa, sai dai wasu sukan samu masu ba su labari, wanda ni ban samu hakan ba.Yawancin abubuwan da nake iya tunawa su ne waɗanda suka faru bayan na haura...
ABUBUWAN DA KE SA SAMUN FARIN CIKI A SANA’A KO AIKI

ABUBUWAN DA KE SA SAMUN FARIN CIKI A SANA’A KO AIKI

Saɓanin yadda mafi yawancin mutane suka ɗauka, sai ka samu aikin da kake so kafin ka yi farin ciki, ga yadda abun yake, waɗanda ke cikin farin ciki su suka fi yin aikinsu yadda ya kamata. Marubucin littafin “Happiness Advantage” ya bayyana yadda bincike ya nuna...
DARUSSA DAGA LABARIN MARIRI GA WANDA YA GANO BAIWARSA

DARUSSA DAGA LABARIN MARIRI GA WANDA YA GANO BAIWARSA

Ina zaune labarin wani mariri ko gada ce (oho) da na taɓa karantawa a wani littafin Hausa shekaru da dama ya faɗo min, ba zan iya tuna cikakken labarin ba kuma ba na kusa da littafin bare na duba, amma ga shigen yadda abun yake. Wani mariri ne ya je shan ruwa a bakin...
ABUBUWA UKU MUHIMMAI DA MATASHI ZAI YI DA SASSAFE

ABUBUWA UKU MUHIMMAI DA MATASHI ZAI YI DA SASSAFE

A lokacin da muke makaranta, kullum muna sa wa a ranmu cewa gobe in mun tashi muna da aji kaza da kaza, muna da jinga, jarrabawa, gwaji ko shiga kasuwa, kai har ma da wanki da girki duk ba ma barin su a baya a lissafinmu.Bayan mun gama makaranta idan aiki muke mun san...
MUTANE IRI HUƊU: WANNE IRI NE KAI? (KASHI NA BIYU)

MUTANE IRI HUƊU: WANNE IRI NE KAI? (KASHI NA BIYU)

Idan mai karatu yana biye, zai iya kiyaye bayanai sun riga da sun gabata a kashi na farko kan kason mutane ma su surutu, yanzu zan ɗaura a kan masu shiru. Ɗan-baiwa Nau’i na gaba wanda shi ne na farko cikin mutane shiru-shiru shi ne “Ɗan-baiwa”, waɗannan su ne irin...
MUTANE IRI HUƊU: WANNE IRI NE KAI? (KASHI NA BIYU)

MUTANE IRI HUƊU: WANNE IRI NE KAI? (KASHI NA FARKO)

Na fara damuwa da son sanin ni wanne irin mutum ne fiye da shekaru 8 da suka wuce. Ba ni kaɗai ba, mutane da yawa suna jin daɗi in suka ga suna gane bambance-bambancen da ke tsakanin mutane. Da fari na ɗauka mutum iri na ni kaɗai ne, domin duk mutanen da nake kewaye...
KA SAN KANKA

KA SAN KANKA

A ƴan shekarun nan, ana ƙara samun yawaitar jumlar nan ta zamto kamar yayi wato “Bi abun da kake so” wacce take nufin ka mayar da abun da kake ƙauna sana’arka, aiki ko karatunka.Akwai saɓani da yawa tsakanin mutane, tun daga kan masu bincike kan halayyar ɗan’adam da...