Yana daga falalar Ubangiji ya samar da bacci cikin rayuwar ɗan’adam kamar yadda yake cewa cikin Alƙur’ani mai girma:

وَمِنْ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبْتِغَآؤُكُم مِّن فَضْلِهِۦٓ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَأَيَٰتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ 

[Surah Ar-Rūm: 23]

Ma’ana “Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa”.

Sannan ya ƙara cewa: وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا

[Surah An-Nabaʾ: 10]

Ma’ana “Kuma, muka sanya dare (ya zama) sutura”

Bacci shine babbar hanyar Samar da nutsuwar jiki data ruhi ga Dan Adam Wanda Babu banbanci tsakanin Mai kudi da talaka hasalima dai talakawan sunfi more wannan Ni’imar.

Bahaushe Yana cewa “Dare mahutar Bawa”

Bacci Yana cikin abubuwa mafi muhimmanci a rayuwar Dan Adam kamar yadda masana suka ce “Idan ba bacci rayuwar bazata cika ba”

Bacci a kimiyyance na nufin wani mataki da mutum Bai iya sarrafa kansa saboda Yana tsakanin rayuwa ne da mutuwa kamar yadda Allah S.W.T yake cewa

ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلْأَنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَٱلَّتِى لَمْ تَمُتْ فِى مَنَامِهَا فَيُمْسِكُ ٱلَّتِى قَضَىٰ عَلَيْهَا ٱلْمَوْتَ وَيُرْسِلُ ٱلْأُخْرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَأَيَٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ

[Surah Az-Zumar: 42]

Ma’ana: “Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa’an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.”

Bacci kamar yadda Likitoci suka nuna wani abinci ne na ruhi sannan hanyace ta habaka lafiyar kwakwalwa da samun koshin lafiya ta jiki. Rashin bacci ko karancinsa Kan sauya yanayin rayuwar Dan Adam da kuma aikin kwakwalwarsa

Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS a wani cikakken bayani da ta yi game da muhimmancin bacci, fa’idarsa da illolinsa ta ce mutum ɗaya cikin uku suna fama da matsalar bacci tare da damuwa da kuma yin aiki ba hutu.

Binciken ya ce bacci yana da muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam, domin yana warkarwa da gyara zuciya da jijiyoyin jini. Kuma rashinsa na da alaƙa da hatsarin manyan cututtukan da suka shafi zuciya da ƙoda da hawan jini da ciwon suga da kuma mutuwar jiki. Don haka samun isasshen bacci yana da muhimmanci ga ɗorewar rayuwa cikin ƙoshin lafiya da kuma aiwatar da jin ɗadin rayuwar, kamar yadda bincken NHS ya ce bacci na ƙara ƙarfin jima’i da kuma rashinsa na hana haihuwa.

BBC ta tattauna da masanin lafiyar ƙwaƙwalwa, Dr. Shehu Saleh shugaban asibitin masu fama da lalurar taɓin kwakwalwa ta Kware a jihar Sokoto a Najeriya wanda ya yi bayani kan muhimmanci da illolin bacci ga lafiyar ɗan Adam. Baccin da mutum yake buƙata ya danganta da shekarunsa, domin wasu suna buƙatar da yawa wasu kuma kaɗan ya wadatar da su.

Dr Shehu Saleh ya ce ko wane ɗan adam akwai awannin da ya kamata ya samu isasshen bacci a kullum bisa ga shekarunsa na haihuwa.Abinda yake da muhimmanci shi ne mutum ya gano adadin baccin da yake buƙata kuma ya yi ƙoƙarin samun baccin domin ƙoshin lafiyarsa.

Acikin wani bincike da hukumar lafiya ta kwashe shekaru biyu tana gabatarwa sun fitar da jadawalin bacci ga kowanne rukunin shekaru

1. Dattawan da suka Kai shekaru 65 zuwa Sama suna bukatar baccin akalla awa 7 zuwa 8

2. Matasa daga shekaru 26 zuwa 64 suna bukatar baccin akalla awa 7 zuwa 9

3. Yaran matasa daga shekaru 18 zuwa 24 suna bukatar baccin akalla awa 7 zuwa 9

4. Yara daga shekaru 14 zuwa 17 suna bukatar baccin akalla awa 8 zuwa 10

5. Yaran da suka isa zuwa makaranta masu shekaru 6 zuwa 13 suna bukatar baccin akalla awa 9 zuwa 11

6. Yaran da basu fara makaranta ba masu shekaru 3 zuwa 5 suna bukatar baccin akalla awa 10 zuwa 13

7. Yara kanana masu shekaru 1 zuwa 2 suna bukatar baccin akalla awa 11 zuwa 14

8. Jarirai daga wata 4 zuwa 11 suna bukatar baccin akalla awa 12 zuwa 15

9. Jarirai daga kwana 1 zuwa wata 3 suna bukatar baccin akalla awa 14 zuwa 17

Idan ko wane rukuni na shekaru ya samu wadataccen bacci, zai kasance sun ƙara samun ƙarfi da ƙoshin lafiya a washegari idan ba haka ba, akwai sauyi da matsaloli da yawa da za su fuskanta. Idan mutum ya tashi daga bacci yana jin kasala kuma daga baya ya ji kamar yana jin bacci, hakan alamu ne da ke nuna mutum bai samu isasshen bacci ba.

MUHIMMANCIN BACCI GA LAFIYAR JIKI

1. Yana Kara lafiyar kwakwalwa da kaifin basira

2. Yana rage hadarin kamuwa da cutuka kamar su hawan jini, ciwon suga, ciwon zuciya da sauransu

3. Yana inganta garkuwar jiki

4. Yana Kara karfin jima’i

5. Yana karawa mutum nutsuwar yin tunani Kan muhimman abubuwa

ILLOLIN RASHIN BACCI GA LAFIYAR JIKI

1. Yawan mantuwa

2. Yawan kasala da rashin kuzari

3. Rashin bacci na jefa mutum cikin ciwon tsananin damuwa, idan ya yi muni mutum yakan iya kashe kansa ko ya halaka wani

4. Rashin bacci na jefa mutum cikin fargaba da kasancewa cikin tsoro

5. Yana sa ciwon zuciya

6. Hawan jini zai ƙaru saboda rashin bacci

7. Ciwon suga na iya tsanani saboda rashin bacci

8. Mutum zai kasance cikin fushi saboda rashin isashen bacci

9. Rashin bacci na sa rashin fahimta

10. Rashin bacci na janyo rashin gani sosai

11. Ga mai tuƙin mota, rashin isasshen bacci na janyo hatsarin mota

12. Yana raunata garkuwar jiki

Likitoci suna Jan hankalin mutane tare da gargadin al’umma musanman matasa Kan yawan anfani da wayar salula musanman lokutan da ya dace ace suna bacci

Masanin lafiyar ƙwaƙwalwa, Dr. Shehu Saleh ya ce rashin samun isasshen bacci na haifar da lalurar kwakwalwa da kuma damuwa. Masanin ya ce ya kamata mutum ya bambance lokacin bacci da kuma lokacin amfani da wayar sa. Ya ce shaƙuwa da waya kan haifar da illa sosai ga al’adar mutane ta bacci kuma matsalar ta shafi yara da manya.

Baiwa wayar salula muhimmanci lokacin bacci kan janyo wa yara rashin fahimtar karatu da shiga damuwa, a cewar masanin.Rashin bacci kan kasance silar rikicin da ake samu na zamantakewa tsakanin iyali da kuma abokan aiki.

Idan ka kwashe watanni ba ka samun isasshen bacci, dole ka tsara yadda za ka biya bashin baccin.Mutum zai iya ƙara awanni a lokacin baccinsa domin rama bashin baccin da yake binsa kansa.

Kamar yadda ake cewa bacci na ƙara yawancin rai, masana sun ce yana da kyau mutum ya ba lafiyarsa muhimmanci ta hanyar gaggauta kwantawa bacci idan lokacinsa ya yi, kuma ya bari har lokacin tashinsa ya yi.

Masana lafiya sun yi gargaɗi kan yawan amfani da magungunan saka bacci domin aikinsu na ɗan lokaci ne kuma za su iya tarwatsa al’adar baccinka.

LAFIYA SAI DA KULAWA!