Matasan su ne ƙashin bayan ci gaban kowacce al’umma, gyaruwar su alamun goben jama’a za ta yi kyau ne, akasin haka kuma na nuna al’umma ba ta da gobe. Ban san ta yadda aka yi matasa suka samun tunanin cewa gobensu na hannun tsofaffi ba, don haka suka bar musu wuƙa da nama sai yadda suka yi da su.

To, ba inda nake son zuwa ba ke nan a wannan rubutun, idan kana jin takaicin yadda tsoffi ke wasa da goben matasa a ƙasar nan, to abubuwan da zan lissafo da matasan ke yi a lokacin azumin Ramadana ya fi wancen takaici da ciwo. Kodayake ba lallai kowa hakan yana ba shi haushi ba, amma wasunmu yana ba mu.

1) Baccin Safe

Idan ka ɗauka ayyukan saɓon Allah zan lisssafo to ka canja tunani, mafi yawancin abubuwan da zan kawo ba saɓo ba ne, amma suna haska cewa gobe ba za ta yi kyau ba.

Matasa da yawa rige-rigen komawa gida suke bayan Asuba don su je su matse kafin gari ya waye. Baccin safe ba ƙaramar asara ba ce ga matashin da yake son rayuwarsa ta haska. Wannan lokacin, bayan albarka da ke cikin sammako, lokaci ne da ba hayaniya, mutane ba su farka ba balle wani ya ɗauke maka hankali ya hana ka yin abun da ya dace. Lokaci ne da ake ribitarsa don a gina kai a ɓoye na tsawon shekaru.

Da yawan matasa ba wai wahala suka sha da rana ba da take kai su zuwa ga baccin safe, a’a sun ƙi kwanciya da wuri ne, sun biye wa hira a dandali (zahiri ko na yanar gizo) da surutai marasa amfani. Ban san ku ba, ni dai in na ga jama’a na sauri su koma gida don su yi bacci nakan ji kamar na shaƙe su!

2) Kallon fina-finai

Wasu kuwa sun mayar da lokacin azumi lokacin baje kolin kallon fim, ko dan saboda sun samu an rage musu wasu awanni a wurin aiki, ko an yi hutun makaranta, ko kuma saboda dama ba su da abun yi.

Rage lokaci ta hanyar kallon fina-finai, ko da kuwa waɗanda ake sa wa a gidajen talabijin sati-sati ne ba ƙaramar asara ba ce ga matashi. Gara ka zauna ka yi shiru ba ka komai in ba za ka yi tasbihi ba da wannan ɓata lokacin. Abun takaici wasu har tanadin fina-finai masu dogon zango suke don zuwan azumi.

3) Zaman Gulma

Faɗin abun ƙi na ɗan’uwanka shi ne gulma. Wani zai ce ai ba ƙarya aka yi ba, halinsa ne. To, dama faɗin abun da ba ƙaryar ba ai shi ake nufi, domin idan ƙarya ne ya zama “buhtahu” (gulma +), ma’ana ya fi gulma hatsari, ga cin nama ga ƙazafi.

Babu alheri a cikin ganawar da mutane suke yawan yi kamar yadda Alƙur’ani ya faɗa mana in dai ba umarni da aikin alheri suke yi ba. Ko da ba gulma kuke ba, zaman rage lokaci ba abun yi ba ne a watan azumi, musamman in abun da kuke tattaunawa ba shi da wata fa’ida gare ku.

4) Wuni a dandalin sada zumunta

Wasu kuwa jarrabawarsu ita ce wayar hannunsu. Ba sa iya zama ba tare da suna “scrolling feeds” na Facebook ba. Babbar matsalata da Facebook shi ne, idan ka shiga don ka yi minti 2, kafin ka ankara ka samu awa 2. Ba ina faɗn haka don zuzuta abun ba ne, da yawan hakan na faruwa da su.

Ko da alheri kake bi, ko da ilimi kake samu, in dai ba sana’ar ka ce kwacokan ta dogara da shafukan sada zumunta ba, to ka dinga sarara wa kanka a wannan lokacin na azumi, ba ka sani ba ko damarka ce ta ƙarshe ta neman yafiyar Ubangiji.

Samun rarar lokaci yana taimakawa wajen daɗewa a dandalin sada zumunta, in kana da yadda za ka yi, ka daure ka cika lokutanka da abubuwan da za su rage maka samun wannan rarar.

5) Shagaltuwa da raddodin malamai

Magabata da dama a zamunnan baya in lokacin azumi ya zo rufe majalisan karatu suke, su shagala da karatun Alƙur’ani a wannan watan. A yanzu da muka samu damar ana fassara mana Alƙur’ani a wannan watan a maimakon hakan ya sa mu dinga tadabburi in muna karanta shi sai muka shagala da yawan jin malamai.

Ba iya shagala da yawan jin nasu ba ne ya fi ciwo, shagala da martani, raddodi da gyara da suke yi wa junansu ya fi shi ciwo. Kai da ba malami ba me ya haɗa ka da saɓanin dake tsakanin malamai na fahimta, aƙida da kuma saɓani na ƙashin kai.

Malamai, Allah ya gafarta musu, ba ka san wahalar da suka sha suka kawo matakin da suke ba a malumta, kai ma matashi kamata yi ka wahala a fanninka don ka kai wani mataki da za ka dinga jin kai ma lallai ka rayu a matsayin “Khalifa” aban ƙasa. Wanda ya daka rawar wani, ba zai samu turmin daka tasa ba in ji Bahaushe.

6) Bara da roƙo

Idan azumi ya zo almajirai ƙaruwa suke yi. Da wanda ya cancanta ya karɓi sadaƙa da wanda bai cancanta ba sai ka ga ana wawar kunu da ƙosai da su. Akwai kuma waɗanda suke fakewa da lokacin azumi su shiga alfarmar watan, su yi ta bin mutane suna neman a taimaka musu.

Wasu kuwa a zamance suke yi, sai su buɗe ƙungiya da sunan tallafawa marayu ko wani abu makamancin haka su fake da wannan su yi ta roƙo da bara. Wasu abun bai tsaya a iya neman abinci da kuɗi ba, har da kujerar umara sai sun je sun roƙa.

Watan azumi ba watan bara ba ne, musulunci ya ƙi jinin mutum mai yawan neman taimako, ko da kana kan abun hawa abun ka ya faɗi, ya fi maka ƙima a addinance ka sauƙa ka ɗauka sama da ka roƙi wani ya miƙo maka, sai dai in ba yadda ka iya ne.

7) Take ciki da abinci

Wai don an ce da ruwan ciki ake jan na rijiya, sai ka ga wasu sun mayar da watan azumi lokacin take cikinsu, saboda su samu guzurin da za su wuni da shi. Ba iya lokacin azumi ba, har lokacin da ba na azumi ba, ana so ka ci ne don ka rayu, ba ka rayu don ka ci ba. Ya ishi mutum ƴan lomomin da za su riƙe masa cikinsa ya yi ibada, kamar yadda ya zo a wani hadisi.

Idan ka sha ruwa, kana da arziƙin cin abinci nau’ika takwas 8, misali, to ka ci kaɗan-kaɗan ka bayar da sauran ya fi maka alheri. Ga lada ga samun ingantuwar lafiyarka. Wasu kuwa har yawon zuwa buɗe baki suke don su je su take cikinsu, yau wannan ƙungiyar ta kira sun je, gobe wata ta sake kira an gan su a wurin.

8) Sangarci da kasala

Azumi gaba ɗayan sa jarrabawa ce, jarrabawa kan sha’awowinmu. Akwai mutanen da haka suke ba sa iya jurar yunwa ko kaɗan. Irin waɗannan mutanen azuminsu yakan fi na waɗanda suke iya jure yunwa lada matuƙar ba su fake da hakan wajen lalaci ba.

Kasala daga sheɗan ne da kuma bin son zuciya. Idan mutum bai yaƙe su ba, ya ɓuge da son hutu, da rashin motsa gaɓɓansa don kar abincin da ya ci ya ƙare, to zai fita daga makarantar azumi ba tare da ya ƙaru da darasin komai ba. Azumi lokaci ne na dagiya, haƙuri da juriya.

9) Ƙorafi

Wasu kuwa ƙorafi ne matsalarsu. Duk inda suka zauna sai dai ka ji suna kiran azumin yau ba a magana, kai! Yau an zabga rana, yau an sha ƙishi, yau na ji jiki, da sauran nau’ika na ƙorafi.

Yin magana don labari ba matsala ba ne (shiru ya fi), amma in ya zama mutum har ransa ƙarofi yake nufi da wannan surutun, to ba shakka yana haifar da giɓi wa ladan azuminsa, har ma imaninsa. Ƙorafi yana da wata illa ta daban bayan wannan, yana samar da hanzari ga mutum (excuses), ma’ana za ka yi ta ɗaukarsa a matsayin uzuri, uzurin da zai rage maka himma, har azumin ya fita ba ka yi wani abun ku zo ku gani ba.

10) Rashin nace wa Alƙur’ani

Malamai suna ta faɗa mana cewa watan azumi, watan Alƙur’ani ne. Idan har cikin magabata na ƙwarai za a samu masu rufe wajen ba da karatunsu don su yi ta karanta Alƙur’ani ba dare ba rana, kai mene ne naka hanzarin?

Ka karanta Alƙur’ani gwargwadon iyawarka, in ba za ka yi sauka a kwana 3 ba, ka yi a sati, in ya gagara ka yi sauka 2, ko 1, kar ka yarda ace ka iya karanta Alƙur’ani daga farko har ƙarshe amma azumi yana zuwa yana fita ba ka sauke ba. Idan kuwa surori kaɗan ka iya, to su za ka yi ta maimatawa kullum, ko bayan kwana ɗaya ka je ga zago (ya danganta da yawansu), har watan ya fita.

Abun da zai sauƙaƙa maka wajen yawan karanta Alƙur’ani shi ne daina ko taƙaita abubuwan da aka lissafa a sama, domin kowannensu akwai ta inda suke da alaƙa da wannan. Daina su zai samar da lokaci da sararin yin wannan ɗin.

Ina fatan Allah ya karɓa mana ibadunmu, idan rubutun ya yi tsauri sai a karɓa da haƙuri, domin igiyar kan hanya kowa fyaɗe shi take, hatta mai rubutun bai tsira ba, don shi ma mutum ne kamar ku. Zan so na ji ƙarin wasu abubuwan da suke sosa muku rai lokacin azumi in kun ga matasa suna yi a lokacin azumi a shashin tsokaci. Mun gode.