Saɓanin yadda mafi yawancin mutane suka ɗauka, sai ka samu aikin da kake so kafin ka yi farin ciki, ga yadda abun yake, waɗanda ke cikin farin ciki su suka fi yin aikinsu yadda ya kamata. Marubucin littafin “Happiness Advantage” ya bayyana yadda bincike ya nuna mutanen da ke cikin farin ciki ke samun damar cimma abubuwa da kammala ayyukansu a lokacin da ya dace. A binciken da aka yi, an gano cewa aikin ƙwaƙwalwa yana ƙaruwa da kaso talatin cikin ɗari (30%) a yayin da mutum ke cikin farin ciki.
Bin abun da ake so
A maimakon mutum ya tsaya neman farin ciki a cikin aikinsa kaɗai, zai iya rungumar abun da yake ƙauna ya mayar da shi aikinsa. A nan ina magana ne a kan abun da ake kira da “passion”. Passion shi ma zuciyar aiki ne, wanda yake da cike da shauƙin aikinsa, ba zai taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen haɓaka sana’ar ko aikin.
Kyakkyawar Manufa
Haka nan samun manufa cikin abun da ake yi, yana sa a samu shauƙin abun, da sauƙin aikata shi. To, ba lallai ya zama mai sauƙi a ma’anar sauƙi da muka sani ba, sa kai ya fi bauta ciwo in ji Bahaushe. Wanda ya san meyasa yake yi, ba lallai ya gane ma lokaci na tafiya ba a lokacin da yake yi.
Ƙwarewa
Ƙwarewa ma ba a bar ta a baya ba wajen samar da nishaɗi da farin ciki a cikin aiki ko sana’a. A wani bincike da Carl Newport ya yi, ya gane cewa mutanen da suka samu ƙwarewa a aikinsu suna yin aiki cike da nishaɗi da farin ciki. Idan mutum ya shiga aiki a farko, ya shiga bai san komai ba a aikin, a hankali a hankali yana yi har ya gama gane kan aikin, daga ya gama gane aikin kuma sai ya zamar masa kamar wasa, yana yi yana ba shi nishaɗi.
Samun sakamako
Amfanar lokaci a yayin aiki ba ƙaramin tasiri ne da shi ba wurin samar da nishaɗi da farin cikin a aikin. Wanda ba ya zama ya yi aikinsa cike da mayar da hankali zai zama aikin yana tsinkewa duk lokacin da ya katse ya shiga wata sabgar, ba za a samu biyan buƙata ba a lokacin da ya dace, hakan kuma zai naƙasa farin ciki da nishaɗin da yake samu a cikin aikin.
Bayarwa
Taimakon mutane su cimma wani abu ta hanyar koyar da su yadda ake yi yana sa mutum ya samu farin ciki a aikinsa. Misali wanda ya raini yaron shago, ya samu ƙwarewar aiki a hannunsa zai zama yana samun nishaɗi a duk lokacin da yake tuna wanda ya yaye a wannan sana’ar haka zai dinga jin farin ciki da nishaɗin ya cimma wani abu.
Akwai wani da na taɓa zuwa wurinsa, yana da yara ƴan makaranta masu samun horon sanin makamar aiki (Industrial training), ya ce shi daɗin da yake ji, ta hanyar koyar da yaran nan kar a tona, domin yana ganinsa a matsayin wanda ke taimakon garinsu ta hanyar horas da yaran da yake.
Koyo kullum
Ci gaba da koyo ma wani abu ne da yake ba wa mutum farin ciki da nishaɗi a aikinsa, wanda yake cikin bincike da koyon sabbin dabaru kan sana’a ko aikinsa don ganin sun haɓaka alama ce ta yadda yake jin daɗin aikin. Idan kana so a daɗe ana yi da kai a duk fannin da kake dole ka ɗaura ɗamarar zama ɗalibi na dindin a wannan fannin.
Shi mai koyo kullum shi ke da riba, za ka zama ɗan gargajiya ne kawai a rayuwa daga ranar da ka daina koyo. Wanda yake koyon sabbin dabarun fasaha kuma ya ɗabbaƙa su a aikace a harkokin aiki ko sana’arsa shi ke zarce sa’a ya yi abubuwan ban mamaki.
Kuɗi fa?
Wasu za su tambayi ya ba su ga kudi cikin jerin abubuwan ba, alhalin kowa na aiki ne don ya samu kuɗi a ƙarshe da zai biya buƙatunsa. Kuɗi yana kawo farin ciki sosai, sai dai farin cikin da yake kawowa ba irin na sauran abubuwan ba ne, nasa na ɗan lokaci ne.
Ga abun da nake nufi, duk wanda yake aiki ko sana’a don kawai ya samu kuɗi, ba zai dinga samun gamsuwa a zuciyarsa ba ko da yana jin daɗin yadda ya fi ƙarfin buƙatunsa da na wasu. Ta yadda za mu gane hakan shi ne, yadda ake faɗi tashin neman farin ciki a wasu abubuwan na sharholiya, kamar zuwa bakin ruwa, tafiya yawon buɗe ido, bukukuwa, shaye-shaye, biye-biyen mata, aure-aure, da sauransu. Idan da aikin yana gamsar da mai samun kuɗi da ba zai shagala da waɗannan abubuwan ba.
Akwai irin aikin da ke kawo kuɗin da me samun kuɗin ma ba kasafai yake samun lokacin cin su ba, sai dai iyalansa su fantama, saboda ƙuncin lokaci ko wahalar da ke cikin aikin. Kuɗi yana da nasa amfanin, da kuma rawar da yake takawa a rayuwa, kowa na buƙatarsa daidai gwargwadon buƙatunsa, sai dai zallar shi kaɗai ba zai samar da farin ciki da gamsuwar da ake buƙata ba, matuƙar babu wasu daga cikin abubuwan da suka gabata.
A matsayinka na matashi, kuskure ne ka kwallafa ranka kan samun aikin da zai kawo kudi masu yawa lokaci guda, wannan tunanin kan iya halakar da kai. Ka yi haƙuri da abun da kake samu, ka koyi aiki, ka ƙware, wataran za a zo gaɓar da kofofin arzikin za su buɗe. Wannan kuma ba ya nufin ka zauna talauci ya halaka ka, ka nemi kuɗi kamar ba gobe malam, ku karanta rubutunmu mai taken “Neman Kuɗi ko Haɗama?!!!” don ƙarin bayani.
Masu samun gamsuwa da farin ciki a aikinsu bas a taba ritaya. E, za su iya ritaya in sun tsufa a daina biyan su albashi ko su daina fita kasuwa ko shago, amma ba za su taba iya zama babu wannan aikin ba. Babban misali shi ne malamai, malamai da yawa suna karantarwa har tsufansu. Haka marubuta, zai wuya ka ga marubuci ya yi ritaya ya daina rubutu kwata-kwata. Akwai masu aikin hannu da ba sa iya daina fita aiki, saboda gamsuwar da suke samu a aikin. Haka masu binciken kimiyya da likitoci. Duk waɗannan abubuwan ko suna kawo kuɗi mai yawa ko ba sa kawowa, za ka samu waɗanda ke da manufa, burin taimakon mutane, shauƙin aikinsu, ƙwarewa da iya amfanar lokacinsu,ba a wayar gari a ce sun daina kwata-kwata sai larura ta kai larura, illa iyaka sukan iya canja salo.
Yana da kyau mai karatu ya tambayi kansa, me nake yi yanzu da nake jin har ƙarshen rayuwata zan ɗore a kansa?