A lokacin da muke makaranta, kullum muna sa wa a ranmu cewa gobe in mun tashi muna da aji kaza da kaza, muna da jinga, jarrabawa, gwaji ko shiga kasuwa, kai har ma da wanki da girki duk ba ma barin su a baya a lissafinmu.
Bayan mun gama makaranta idan aiki muke mun san lokacin zuwa aiki da lokacin tashi, haka in kasuwa muke fita duk mun kiyaye lokacin buɗe shago da lokacin rufewa. In mun dawo gida ma muna da lokacin zaman majalisa, da teburin mai shayi, har ma da na kallon labarai.
Ba iya wannan ba, idan mu ma’abota kallon wasanni ne, muna kiyaye da yaushe ƙungiyarmu za su buga wasa, awa nawa ne, da ma waɗanda za a buga wasan da su. Idan kuwa a layin kallon fina-finai masu dogon zango muke na sati-sati da ake sa wa a gidajen talabijin, duk muna ƙoƙarin kiyaye ranaku da lokutan don kar abun ya wuce mu.
Duk wannan na nuna mana yadda rayuwarmu take a tsare, ko mun tsara hakan ko ba mu tsara ba, ko mun sani ko ba mu sani ba. Idan kai matashi ne mai son ci gaba, ka biyo ni a wannan rubutun don ji abubuwa muhimmai da za ka yi duk yadda za ka yi ka dinga cimma su da safe.
Tsari
Bayanan da na zayyano a baya suna nuna mana yadda muke kan wani tsari ne a rayuwa. Akwai lokutan da haka abun yake kawai an riga da an tsara, mu namu bi ne, akwai kuma lokutan da mu ne muka ba abun muhimmanci har muka sanya shi cikin tsarin mu.
A nan ina magana a kan tsarin da zai amfane ka kai tsaye a rayuwa ba wanda aka tsara maka ba. A matsayinka na matshi mai manufa, yana da kyau in ka tashi da safe ka rubuta abubuwa guda biyu zuwa uku da kake son cimmawa a wannan yinin kana mai duba da halin da kake ciki na ɗalibta, sana’a ko ma zaman haka.
Masana sun bayyana rubuta abun da za a cimma ko aikata a wuni a matsayin hali mai kyau da ke kai mutum in da bai taɓa tsammani ba. Abun shi ne, duk nasarar da kake nema a rayuwa da wuri za ka same ta matuƙar kana tafiya kan tsari. Duk abun da aka ce yau ka yi shi, gobe, jibi, duk ka yi, har ka shekara ko ka yi shekaru to sai ka zama gagara-badau.
Tsari yana taimakawa wajen tsayar da hankali wuri guda, yana hana watangareriya da lokaci, yana sa a ƙarshen yini ka samu nishaɗi, sannan zai ba ka ma’aunin auna abubuwan da ka yi a wannan yinin.
Mu fahimta, musamman a yanzu da muke tunkarar sabuwar shekarar Bature, abun da za ka rubuta a msatayin burukanka na shekara ba su da wani tasiri, tsarin abubuwan da za ka yi kullum da kuma aiki da tsarin shi ne zai ba ka damar kai wa ga nasara.
A lokacin da muke ƙoƙarin tsara rayuwarmu yana da kyau mu fahimci kuma mu gujewa abun da ake kira da “analysis paralysis”. Shi wannan wani yanayi da zai sa mutum ya zamto kullum cikin wasiƙar jaki da lissafin me yake son yi. Yin tsari mai kyau ta hanyar rubutawa a takarda yana cikin hanyoyi mafiya sauƙi da za ka tsira daga wannan matsalar.
Karatu/Ibada
A matsayinka na matashi, babban abun da ya kamata ka sa a lissafinka a lokacin da kake tsara yadda yininka zai kasance shi ne lafiyar ruhi da ƙwaƙwalwarka. Domin dama amfanin tsarin shi ne ka rayu yadda ya kamata, to in ya zamto waɗannan abubuwa biyun ba sa nutse babu abun da zai tafi daidai.
Saɓanin yadda da yawanmu muka ɗauka, tuwa ba shi kaɗai ne abinci ba, abubuwan da muke karantawa, aikawata, saurare, cuɗanya da su duk su ma abinci ne amma na ƙwaƙwalwa, ruhi da zuciya.
Wanda yake son wuninsa ya masa daɗi ya fara da karatun Alƙur’ani gwargwadon ikonsa. Karatun Alƙur’ani yana jaddada imani, ya ƙara nishaɗi da albarkar rayuwa. Daga nan sai Sallah ga wanda ya tashi kafin Asuba. Wanda kuwa bai samu hakan ba, shi ma yana da damar yin wuridi na zikirori tabbatattu daga sunna don amfanar kansa.
Daga nan sai karatu na ilimi, ita ƙwaƙwalwa kamar yadda mai motsa jiki yake gina gaɓoɓinsa haka mai karatu yake gina tasa. Idan kana da wani ilimi da kake nema, ka bibiye shi da sassafe kafin gari ya waye a samu hayaniya. Amfanin neman ilimi ko yin karatu da safe shi ne ba ka da wani da zai zo ya uzzura maka domin kusan kowa na can na bacci.
Daɗin daɗawa kuma, samun lafiyayyen jiki yana da alaƙa da lafiyar zuciya, ƙwaƙwalwa, da salamar ruhi. Akwai rubutuka da muka yi da yawa a baya kan alaƙar su, wataƙila watarana mu sake warwarewa. Mun san kuwa komai na rayuwa sai da lafiyayyen jiki.
Gina Kai
A misalin da na fara buɗe wannan rubutu da shi, idann kun lura da wani abu, duk waɗancan abubuwan muna yin su ne don sun zamar mana dole. Ko da yake ba dukka ne dole a kanmu ba, amma sun zama dole saboda ai sa kai ya fi bauta ciwo.
A rayuwa ne ana yin zarra ta hanyara aikata abubuwan da sauran mutane ba sa aikawa. Idan kowa yana yi don ka yi ba za ka bambanta da saura ba, amma in ka yi na kowa kuma ka ƙara da wanda ba kowa ke yi ba nan ne za ka ga samu sakamakon da ya dace.
Ga abun da nake nufi, da ɗalibin da iya karatun cin jarrabawa yake, da wanda yana bin komai tas sai ya fahimci komai, ya haddace duk abun haddacewa, wa zai fi samun ilimi? Da ma’aikacin da iya zuwa ofis yake ya yi abun da ya kai shi ya dawo, da wanda yake ƙarawa da wasu ayyukan da sauran ba sa yi wa zai fi saurin samun ci gaba? Da ɗan kasuwar da yake yin komai kullum iri ɗaya tun iyaye da kakanni, da wanda ya shigar da zamani cikin kasuwancinsa kuma kullum yake bincike kan sabbin dabaru wa zai fi samun ci gaba?
A duk waɗannan misalan, wanda yake yin wani abu ƙari a kan na dole shi ne ke gaba da ɗan’uwansa. Ko a Musulunci wanda ke ibada ta nafila ba ɗaya yake da wanda iya ta farilla yake ba. Wannan shi nake nufi da gina kai sassafe.
Idan aikinka ko kasuwancinka ba ya maka abun da kake so, abu mai sauƙi ka ware minti 30 zuwa awa guda a safiyarka don gina kanka ta hanyar koyo ko aikata abun da tsarakin ba sa yi. Idan ɗalibi ne kai, ka gina kanka ta hanyar koyon skill ko wani ilimi da ba ka koya a makarantar a safiyarka. In ma’aikaci ne ka, ka ware ƴan mintoci na koyon sarrafa kuɗi, mu’amala da jama’a, talla, iya magana ko duk wani abu da zai taimake ka a wurin aikin ko ya sama maka ƴanci a bayan ka bar aikin.
Waɗannan abubuwa guda ukun, duk matashin da ya riƙe su, zai yi mamakin inda rayuwa za ta kai shi a shekaru goma zuwa ashirin masu zuwa in ya yi nisan kwana. Mafi muhimmanci kuma zai ci moriyar rayuwarsa a yanzu da yake raye, don ko da bai yi tsawon rai ba, ya san ba aikin banza yake ba, zai kuma amfana ya amfanar, ko da bai yi kuɗi ba, zai samu rufin asiri da ƙima a idon waɗanda yake tare da su.
Abubuwan ya kamata su fi haka, amma za mu dakata a nan saboda gudun tsawaitawa, ku ƙara mana da wasu da kuke ganin su ma suna da muhimmanci a shashen tsokaci. Mun gode.