Akwai wani bawan Allah mai himma da son addini, sai dai ya gaza a wasu dabaru na hulɗa da mutane. Watarana ya kama hanya zai je sallahr azuhur a masallaci cikin shauƙin son yin sallahr da kuma girmama addini. Ya na sauri don kada a tada iƙama bai karasa ba.
A kan hanyarsa sai ya iske wani mutum a kan bishiya, yana aiki. Sai mamaki ya kama shi, a ransa yace “waye wannan da bai damu da sallah ba haka! Ya na yin abu kamar ma bai ji kiran sallah ba, ko ma bai damu da iƙamar da za a yi ba!”
Cikin fushi da ɓacin rai ya yi magana da babbar murya, “sauko ka je ka yi sallah!” Mutumin ya amsa masa cikin taushin murya da kalmar “to, to”. Bawan Allahn nan bai haƙura ba ya sake cewa da shi “yi gaggawa ka sauko ka tafi, dabba kawai”
Wannan kalmar ta fusata mutumin nan, ya rarumi ice zai maka masa a kansa, kafin ya samu damar hakan ya tafi shi kuma, kuma ya rufe fuskarsa dan kar ya gane shi. Mutumin nan ya sauko daga bishiya ya zauna ya huta, sannan ya tafi gida ya yi sallah, ya dawo yaci gaba da aikinsa.
Da la’asar bawan Allahn nan ya sake dawowa zai wuce sai ya ƙara ganin mutumin nan a kan bishiya yana ci gaba da aikinsa. Sai yayi shawarar ya canja salonsa a wannan karon.
Cikin taushin murya ya masa sallama, su ka gaisa, sannan ya tambaye shi ya dabinon nasa, bayan amsa masa da komai lafiya sai ya masa addu’ar nasara akan harkarsa da kuma ladan aikin da yake yi na neman halal. Mutumin ya ji daɗin addu’ar sosai ya amsa da amin.
Daga nan sai bawan Allahn yace “kamar ka shagaltu da aiki, gashi kuma an kira sallah, har ana ƙoƙarin tayar da iƙama, da son samu ne da ka sauko yanzu ka ɗan huta, sannan ka yi shirin ƙarasawa masallaci ka yi sallar. Ka ga bayan sallar sai ka zo ka ƙarasa aikinka, Allah ya ƙara maka lafiya”
Mutumin ya amsa da “in Allah ya so, in Allah ya so” ya sauko a hankali ya mika masa hannu suka gaisa cikin annushuwa, yace “dole na gode maka saboda kyakkyawar mu’amalarka. Don kuwa akwai wanda ya wuce ni da azahar, da zan haɗu da shi, da na nuna masa waye ainihin dabbar! (An ciro daga littafin Enjoy Your life na Al’arify)
Kada taken rubutun ya ruɗe ka, ba mafaka za a ba masu aikata laifi ba, muna son nusar da masu ƙoƙarin hani da mummuna, su gane cewa samun sauyi a cikin salon yin gyara yana taka rawa wajen karɓar gyaran, kamar yadda munana salo kan jawo a ƙi karbar gyaran, har ya zama an fassara masu addini da munana mu’amala, wanda hakan zai jawo ƙyamata ga addinin.
Farmakar mai laifi ba laifin ba
Idan mu ka yi duba zuwa ga bawan Allahn nan da labarinsa ya gabata, za mu gane cewa ya na cike da shauƙin son yin gyara ne, amma sai ya kuskure hanya a karon farko, wato a maimakon ya ja hankalin mutumin zuwa ga abun da yake na ba daidai ba sai ya farmake shi, farmakar da ta sa ya ƙi ɗaukan karatun, balle ma ya yi aiki da shi.
Wannan hali na farmakar mai laifi yana taka rawa sosai wajen hana mutane ɗaukar wa’azi. Ba ance kullum a dinga lallaba mai laifi ba ne, har ma ya ɗauka abun da yake ba wani laifi ba ne, ana cewa idan dai gyaran ake so to a yi koyi da wanda ya zo da gyaran.
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yana ɗaukar zafi in aka taɓa Allah ko aka taka wata doka ta addini, amma ba ya hucewa a kan mai laifin, yana yin magana a kan laifin ne da kuma girmansa a wurin Allah, da haɗarin da mai aikatawa yake cusa kansa.
A wasu lokutan ya kan yi jawabi kan mai uwa da wabi, duk da ya san ayyanannun mutanen da suka yi laifin, amma sai ya sakaya saboda su samu saukin karɓar gyaran ba tare da sun kunyata a cikin mutane ba. Misali:
Wata rana Annabin Allah mai tsira da aminci, ya lura da cewa cikin sahabbansa wasu in suna sallah su kan ɗaga kansu su kalli sama wanda kuma a sallah ana son kallon gurbin sujuda ne. Sai yace “me ke damun mutane ne da suke ɗaga kansu suna kallon sama a cikin sallah?” Da ya ga ba su daina ba sai ya ce “ko dai su daina ko kuwa a ɗauke musu ganinsu”.
Tsumbula baki a cikin komai
Mutane da sunan sun waye (sun zama intellectuals), ko da sunan su masu jin wa’azi ne, sai ya zama komai suna da ta cewa, kuma faɗin nasu bai tsaya iya tsakaninsu da abokanansu ba, duk abin da ake yi sai sun bayyanawa duniya ra’ayinsu.
Irin waɗannan mutanen ba ƙaramin cutar da addini suke ba, domin suna yawan shiga hurumin da ba su kai su shiga ba (ko da huruminsu ne). Abun da ake nufi shi ne, kowacce magana akwai waɗanda ya kamata su yi ta a irin yanayin da ya dace.
Idan kai ba mai mulki (mulkin gida, makaranta, unguwa, gari ko kasa) ba ne, ba ka da ikon hana mutum aikata wani laifi ta hanyar tursasawa, idan ba ka da iko a kan mutum (ka girme shi ko yana ganin ka da mutunci), ba ka da ikon hana shi laifi da fatar baki, aikinka shi ne ka ji ba daɗi a zuciya ka je ka yi ta neman gafarar Allah.
Abun da na ke so na ce shi ne, duk abun da wanda bai kai ya yi magana ba ya yi, ƙarshe dagula lamari yake. Ina jin daɗin yin misali da ƴan wasan kwaikwayo, abu kaɗan za su yi a yi ta yaɗawa ana zaginsu da ci musu fuska wai a matsayin nasiha, amma fa duk sabon shirin da suka fitar za a nema a kalla. Kenan dai an ƙi cin biri an ci dila, shi ya sa ba a fahimtar juna da su da ma su mu su gyara. Me kuke tsammani in da hukuma ce ta kama su ta ɗaure?
Wayayyun da suke da ta cewa a kan komai, yawanci suna debo abubuwan da suka fi ƙarfin iliminsu da tunaninsu, su yi magana, wasu dan a caccake su su samu ƙarin mabiya, wasu kuma gaskiya suka nufa amma ba su bi hanyar da ta dace ba, koma dai mene dalilin daga ƙarshe abun ya na cutar da sauran jama’a da ke mu’amala da kafafen sada zumunta, don ko ba komai shakku zai iya samun su.
Bibiyar sirrin mutane
Wata rana sayyadina Umar lokacin ya na kalifa, ya samu labarin wasu da suke ɓuya suna shan giya, sai ya haura musu cikin dare da nufin ya kama su, yana dira kuwa ya gan su, sai suka ce masa mun yi laifi ɗaya, kai ka yi guda uku. Mun ɓuya ka bibiyemu, ba ka mana sallama ba, ba ka shigo ta ƙofa ba, sannan ba ka nemi izini ba.
Ko a cikin unguwa ba za ka rasa sanin wani da ba ya iya gani ya yi shiru ba, koyaushe cikin ƙoƙarin nuna wa mutane kura-kuransu ya ke, da nusar da su don su gyara. Allah ya saka ma irin waɗannan mutane da alheri.
Matsala ɗaya da irin waɗannan ƴan gaza gani suke da ita in an yi rashin sa’a ita ce bibiyar mutane da sanya musu ido, komai aka yi a kan idonsu ko kunnensu. Wannan daɓi’a tana sa mutane su tsani mutum, ba yadda za a yi kuma a tsane ka ka ce za ka kawo gyara a karɓa.
Ku duba irin soyayyar da ake yi wa Annabi tsira da aminci, amma da ya zo da gyara sai aka bijire, kyawawan halayensa da bai sauya ba su ne suka taimaka wajen yaɗa da’awarsa yadda yakamata, har ya zama akwai lokutan da ba ya buƙatar ma ya yi wa’azi ko nasiha, kyawun halinsa kaɗai zai nuna sai a karɓi gaskiyarsa, a hakan fa ana sonsa ne, ina ga inda a ce ƙinsa ake?
Bayyanar da Ɓarna
Dukkanmu mun yarda ba wanda ya fi ƙarfin zamiya, kuskure da kauce hanya. Mai ƙoƙarin yi wa mutane gyara ya kamata ya fi kowa taka-tsantsan a kan aikata laifi a bayyane. Duk wanda yake bayyana ɓarna ko da yana da bakin yi wa mutane gyara a farkon al’amari, za a zo gaɓar da mutuncinsa zai zube a daina saurararsa.
Abu mafi muhimmanci a wannan gaɓar shi ne kare mutunci da kaucewa faɗawa shubhohi, duk abun da ya zama shubha Manzon Allah tsira da aminci ya ce wanda ya auka masa to ya auka cikin haram.
Allah yana cewa ” za ku umarci mutane da aikin ɗa’a kuna mantar da kawukanku alhalin kuna karanta littafi…”.
Duk iya wa’azinka ba ka kai Annabi Musa ba, kuma duk fitsarar mai fitsara ba zai kai Fir’auna ba, amma sai Allah ya ce da Annabinsa Musa da Haruna:
“ku faɗa masa magana mai taushi domin ya ɗauki wa’azi wataƙila ya ji tsoron Ubangiji.” Q20:44.
Duk da wannan kuma fa, yakamata mu sa a ranmu cewa shiriya ta Allah ce, aikin mai yin gyara kawai ya fada, amma a yi aiki da gyaransa ko a daina laifin ba a hannunsa yake ba, ko da wanne irin salo ya yi, illa iyaka dai yin abun yadda ya dace ya fi mayar da shi mutum kuma an fi sa ran gyaran zai fi shiga.
Daga ƙarshe, shawara ga waɗanda ake musu gyara suke tawili ko su ƙi karɓa da hujjar cewa ba a faɗa musu a yadda ya dace ba, ku sani cewa ƙin karɓar gaskiya alama ce ta girman kai, karɓar gyara da nadama halin ƙwarai ne, idan muka biye duba zati ko salon mai mana gyara, za mu iya rasa masu faɗa mana gaskiya, don wasu ko da sun ga gaskiya sukan ɓoye don gudun ɓata wa mutum rai. Mutane kowa da irin ɗabi’ar da yake kai, ba kuma kowa ba ne ra’ayinmu zai zo ɗaya, kuma ba kowa ne za mu ƙaunace shi ba, amma ita gaskiyar dai sunanta gaskiya. Allah ya ba mu dacewa.
Ma shaa Allah. Allah ya saka da alkairi.
Ma sha Allah, amin summa amin
Wannan zungureriyar nasihar ta shafi kowa; ta biyo ta kan mai laifi da mai yi wa mai laifi gyara/wa’azi.
Haƙiƙa a cikin wannan nasiha na koyi abubuwa da dama kuma an tunasar da ni abubuwa masu yawa. Allah ya ba mu ikon ɗaukan gyara idan an yi mana gyara kuma Allah ya sa mu ke yin nasiha da hikima da salon basira ga wanda suka kasance masu ɓarna.
Gaskiya ne. Ma sha Allah, amin summa amin.