“Angona na shirya ni ma, yau tare za mu tafi ofis” Amaryar ta ce da shi.
“Kowa yana barin matarsa a gida sai ni ne zan ɗauki mata goɗai-goɗai na tafi ofis da ita?” Angon ya ba ta amsa.
“Haba masoyi, ba za ka yi irin na mazajen novels ba, haka suke yi fa” ta sake faɗa.
“To ni ba mijin novel ba ne, ni mijin ahalari ne don abu ta kazarki..” ya ba ta amsa.
Haka na karanta wannan kwanakin baya mutane suna ta ɗaurawa a status. Jingina wannan mijin da ahalari ne ya ja hankali na, domin na ji hakan kamar cin fuska ne ga ma su addini.
Na fara karance-karancen littafan Hausa na yaƙi tun ban fi aji 4 na firamare ba, yadda mata ke zama su saurari littafi a gidan rediyo haka nake zama wani lokacin wani saurayi a maƙotanmu yana karanta mana litttafi ina saurare (kafin na ara ko na hayo na karanta ni ma).
Sai dai ban damu da na soyayya ba, sai da na girma ne ma na ɗan karanta wasu kaɗan, kafin daga baya ma na bar karatun irin littafan kwata-kwata. Ban san meyasa ba, tun dama can soyayya ba ta kama kai na, daga baya dai na gane dalilin, wataƙila wata rana zan yi tsokaci a kansa.
Akwai mabanbanta ra’ayi kan litattafan novels da finanan soyayya da muke karantawa ko kallo, wasu suna sukarsu ba tare da sun taɓa karantawa ba, wasu suna ba su kariya ba tare da sun san mene ne a ciki ba. Wasu kuma sun karanta sun san illa ko amfanin da ke ciki amma sun zaɓi su ba wa ɓangare ɗaya kariya.
Koma dai mene ne, akwai wasu halayya da na ke ganin mazaje ya dace su koya daga mazajen novels, domin matan da suke rubuta novels suna haska irin muradan ƴan uwansu mata a ciki, da abin da suke sa ran samu/fantasy (ba dukka ne gaskiya ba, tunda dama tatsuniya ce kawai, ana ƙara wani abun ne dan labarin ya ƙawatu). Wannan ba iya novels ba, ko fim ɗin indiya da muke kallo suna nuna mana soyayyar ƙarya da za mu kwaɗaitu mu samu irinta.
Kalamai ma su daɗi
A lokacin da ake soyayya a waje za ka samu kowa yana ƙoƙarin faɗawa ɗan uwansa kalamai ma su daɗi don ya ƙara samun wurin zama a zuciyar masoyin. Abu komai ƙanƙantarsa sai an yaba wa masoyiyar.
Wannan yana daga cikin abubuwan da ya kamata a fi ba su muhimmanci bayan aure don ƙarawa soyayyar armashi, sai dai kash, saɓaninsa ne yake faruwa. Daga zarar ido ya buɗe daga fizar soyayya a matakin farko abu na gaba da zai biyo baya shi ne rashin burge juna da rashin kalamai masu daɗi.
Kyauta
Saurayin novel akwai shi da kyauta, za ka ji yana kyauta kamar kuɗin a zube suke kawai ɗiba yake. Ba saurayin novel ba kaɗai, samari a zahiri ma haka ne, sun yarda kyauta na ƙara danƙon soyayya, don haka ma da kansu suka ƙirƙiro wa kansu Ramadan basket, Sallah basket da sauransu bayan kyauta ta yau da kullum da suke yi.
Wannan ɗabi’a da miji ta fi dacewa ba saurayi ba, domin miji ya fi buƙatar soyayyarsa ta zama koyaushe a raye saboda ya ga komai, ya samu komai da yake nema, ƙanƙanin abu zai iya sa wa su ji soyayyar ta dusashe.
Kyauta ba iya kuɗi ba ne, ko wani abu da za a siya da kuɗi, ba da lokaci ma kyauta ne, yabo kyauta ne, nuna kulawa kyauta ne duk kuma waɗannan kyautukan ana buƙatarsu. Daidai ruwa daidai tsaki, ka da mutum ya ce sai ya yi yadda wasu suke yi.
Yin sabon abu lokaci-zuwa-lokaci
Kamar yadda masana suke faɗa, yana daga cikin abin da ya ke sa soyayya a matakin farko ta rufe wa mutum ido saboda komai sabo ne. Duk lokacin da aka yi wa mutum wani sabon abu zai ji shauƙi na musamman.
Bayan an yi aure wannan shauƙin yana tafiya saboda yau da gobe, daga nan sai komai ya komawa mutum kawai yana yi ne don dole ba don soyayya ba. don haka waɗannan masanan suka bayyana cewa yin sabon abu a zaman aure yana saurin farfaɗo da soyayya.
Misali ku fita unuguwa tare da matar, ka siya mata wani abu na bazata da ka san tana matuƙar so lokacin kuna soyayya (Nakan siya wa tawa matar, in ina da hali, wani chocolate da na siya mata a lokacin da nake neman aurenta kuma tana jin daɗin hakan), haka kawai ka ci kwalliya ka zauna a gida saboda ita (Abdullahi ibn Mas’ud haka yake yi), ka yi cefane na musamman dan ku ci wani abu da kuka daɗe ba ku ci ba, duk dai wani abu da a zamantakewarku za ku iya irga shi a matsayin sabunta wani abu da aka daɗe ba a yi ba.
Yabo
Wannan yana iya faɗawa cikin kalamai masu daɗi, yana iya kuma cin gashin kansa. Misali wancen mijin da a maimakon ya gwasale matar nan, da ya nuna jin daɗinsa da irin soyayyar da take nuna masa, wataƙila ma ya mata alƙawarin wani abu da zai mata ko zai kawo mata da za ta ji daɗin kalamansa.
Shi yabo yana zuwa ne a lokacin da ta yi wani abu na bajinta, misali in ta ci kwalliya sai kace “kai! ke ce kuwa, da a hanya muka gamu ba zan gane ki ba, kinga yadda kika haɗe sai ka ce daren amarcinmu, wannan kwalliyar dole na yi kyauta”
Ko kuma “duk lokacin da na ci girkinki sai na ji girkin da ba naki ba lami ne”, “wannan turaren da kika fesa ba zai bar ni na fita daga gida ba yau”, da sauransu a salon dai da ya dace da kai, matar da kuma yanayin, wannan misali ne kawai.
Wani zai ce shi ba zai yi ƙarya ba, wataƙila kwalliyar ba ta kai ta samu wannan yabon ba, amma ba shi ake dubawa ba, ta yi? E, to in ta yi a yaba kuma a kambaba abun yadda kanta zai fashe. Hakan ne zai sa ta ƙara zage dantse, kuma kai ma idonka zai ƙara buɗewa ka ci gaba da kalon kyawawan abubuwan da take yi a maimakon munana.
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya lissafa wasu mutum 3 da ya ce ba zai irga su a matsayin maƙaryata ba, ciki har da mijin da zai yi wa matarsa ƙarya ko ita ta masa don zamantakewa ta yi kyau (miji da mata ba saurayi da budurwa ba, a lura). Malamai sun bayyana irin waɗancen misalai na yabo a wannan babin.

Yanzu Ahmad kana so mu koma karatun novels kenan? Wani zai tambaya. Amsar ita ce a’a, ni kai na na manta rabon da na karanta, kuma ba zan iya bai wa wani shawarar ya karanta ba, na ba wa rubutun wannan taken ne don wancen labarin kawai (novels da dama suna nuna yadda mazaje ke ƙuntatawa mataye, wasu kuma suna buɗe wa mata ido kan ƙin biyayyar aure, da bin bokaye), amma in ka so ka karanta ka gani, in ka amfana to, in kuma ka cutu to, ya rage naka (balil insanu ala nafsihi basirah).
Saƙon dai shi ne, soyayya kamar batir ne, yadda cajin batiri yake ƙarewa sai an masa sabo, haka take buƙatar a dinga sabuntata ta hanyar aikata waɗannan abubuwan da ake aikatawa a farkonta, wannan kuma yana buƙatar sadaukarwa da aiki tuƙuru bayan auren saɓanin kafin aure da komai yake zuwa a sauƙaƙe.
Wataƙila a gaba mu yi rubutu na musamman kan yadda ake farfaɗo da soyayyar da ta dusashe, in hakan bai samu ba na tabbata rubutun Mallam Bahaushe na “Soyayya Ta Yi Kaɗan” zai tattauna wannan batu don haka sai a ci gaba da bibiyarmu.