Cin nasara a rayuwa abu ne da kusan dukkaninmu muke muradi. Amma me kuke tsammani idan cin nasarar da muke ta faɗi tashin samu ta zo a gagarumin farashin da ba mu taɓa zato ba?

Atika da daɗe tana jin ana faɗin cin nasara yana buƙatar gagarumar sadaukarwa. Kasantuwar ta taso a ƙaramin gari, ta ga yadda iyayenta suka yi ta fama don a samar musu da abun sa wa a bakin salati. Don haka ta ƙuduri aniyar cewa duk runtsi sai ta fita daga wannan ƙangin. Da ta duba abubuwan da suke kewaye da ita, sai ta gamsu cewar ba ta da wata mafita illa ta riƙe karatun boko hannu bibbiyu. Tun da ta shiga makarantar sakandare, ta ɗaura ɗamarar fin kowa ƙoƙari.

Tana tashi da duku-duku tun kafin asuba ta yi bitar karatu, tana raba dare tana haddar fomuloli, in an fita tara kuma ta shige ɗakin karatu ta ci gaba da bita, a sa’ilin da abokan karatunta ke waje suna wasanni da raha. Wai a zauna a yi bitar karatu tare da ƙawaye? Sam, ba ta yarda, ta yi imanin cewa ta fi saurin koyo ita kaɗai. Wuraren nishaɗi da shaƙatawa? Hahha, ɓata lokaci ma ke nan. Ta gamsar da kanta cewa ƙulla abota ma zai dinga raba mata hankali ne, don haka ba ta ƙawaye take ba, tana ganin duk daƙiƙa guda da ta ɓata wajen biye musu, kamar tana nisa da cikar burinta ne.

Malamanta sai koɗa ta suke a aji, iyayenta suna cike da alfahari da ita, ƴan ajinsu kuwa yadda take tursasa kanta ta yi abun da ya dace ne yake ɗaɗa su da ƙasa. Sukan ce “Lallai za ta cimma abubuwa manya a rayuwarta”. Kuma haka ne, domin Atika ta gama makaranta da sakamako ma fi kyau a duk makarantar. Ta samu kyatuttuka, tallafin karatu, har ma an gayyace ta ta yi magana a taron yaye ɗalibai, sai tafi ake mata, yayin da iyayenta ke zubar da hawayen farin ciki, ƴarsu ta ci nasara.

Daga nan fa sai rayuwa ta canja salo. Atika ta shiga Jami’a, ta tarar da gasar da ake a can ba ta wasa ba ce. Kasantuwar ta zo daga ƙaramin gari, tana shan baƙar wahala wajen karatun. Ga shi ta riga da ta taso da rayuwarta a cikin ƙin ƙulla alaƙa da kowa, don haka yanzu da take sabon wuri sai ya zama ta kasa sake jiki. Idan aka ba su aikin da za a yi tare (group assignment) hankalinta tashi yake. A yayin da sauran ɗalibai ke haɗuwa su yi bita da nazari tare, ita ta samu kanta a ƙangin yin aiki fiye da ƙima da kuma kaɗaici.

Daga nan fa sai lafiyarta ta fara taɓuwa. Baccin da ta tara na shekaru ya fara damunta. Ciwon kai mai tsanani ya addabe ta, yawan jin ciwon jiki da kuma fargaba suka aure ta. Likitoci sun ba ta shawarar ta ɗan dinga sararawa amma ina! Tana ganin hutu a matsayin gazawa. Don haka ta zage ta ci gaba da fafatawa. A lokacin da ta kammala jami’a, ta gama da ma fi kyan sakamako, amma da ma fi munin yanayi/lafiya (well-being).

Lokacin da ta samu aikinta na farko, sai wata gaskiya ta bayyana gare ta. Abokan aikinta suna haɗa hannu su yi aiki tare, su tattauna dabaru, su ƙara wa juna ilimi, su fita su ƙulla alaƙa da mutane, wanda hakan yake buɗe musu ƙofofin samun alherai. Atika kuwa, duk da ƙwaƙwalwarta, ta kasa sake jiki ta saje da su. A sannan ne take gane cewa, cin nasarar rayuwa ba iya tara ilimi ba ne, iya ƙulla alaƙa ne da mutane, iya mallakar kai, da kuma iya daidaita rayuwa tsakanin aiki da rayuwar kai da kai.

Wani yammaci, bayan ta ɗebo gajiyar wurin aiki, ta zauna tana duba wayarta, sai ta ci karo da wani tsohon hoton ƴan ajinsu na sakandare. Hoto ne da suka yi tare a lokacin da aka fito tara suna cike da murna da fara’a. Sai dai kash ba ta cikin hoton, lokacin tana ɗakin karatu tana bita, don cimma burin da a yanzu ya zamar mata kamar wani alaƙaƙai.

Lallai Atika ta ci nasara a ɓangaren karatun aji, amma ta faɗi a makarantar rayuwa. Nasararta ta zo mata da babban farashin da ba ta taɓa tsammani ba.

Wannan abun da ya faru da Atika shi ake kira “Pyrrhic Success”, ma’ana nasara ta zo a gagarumin farashin da zai jawo rashin nasara a gaba.

Labarin Atika ba labarinta ba ne ita kaɗai. Akwai dubban matasa a wannan jirgin a yau. An koya mana cewa cin nasara yana da alaƙa da sakamakon makaranta, kyaututtuka, da shaidoji (certificates). Amma a ƙashin gaskiya, nasara ta gaske ta zarta duk waɗannan.

Nasara a kowanne fanni tana buƙatar aiki tuƙuru da daɗewa ana yi kamar yadda Atika ta yi. Sanin kanka da burinka zai iya zama matakin farko. Amma mu sani, bayan waɗannan, alaƙa, kyakkyawar mu’amala, kula da lafiya, gogewar rayuwa suna gaba da komai. Duk ƙoƙarin da za ka yi a makaranta a matsayin ka na ɗalibi, kar ka sake ace ba ka koyi hulɗa da mutane ba, tattaunawa da iya magana a cikin jama’a, aiki tare, jan ragama, abota, da iya sarrafa kai in rai ya ɓaci. Waɗannan abubuwan da ba lallai a koyar da su a aji ba, sukan sa waɗanda suka iya su yin fintinkau a rayuwa ga waɗanda ba su iya su ba.

Me kuke tunani game da wannan batun? Kun taɓa samun kanku a wani yanayi da kuka manta da more rayuwa saboda wani aiki da kuka tasa gaba? Zan so na ji ra’ayoyinku a shashen tsokaci.

JH: Gaba ɗayan labarin nan ƙirƙirarre ne, idan ya yi kama da naku, ko na wani da kuka sani to ku sani an samu kamanceceniya ne kawai, ƙago shi aka yi. Mun gode.