Gen Z ko Indomie generation kamar yadda ake kiran su, da mu kanmu millenials mun samu kanmu a cikin ruɗani a wannan zamanin. Ba ina son cewa a lokutan baya babu ruɗani ba, a’a, amma in ka duba halin da muka tsinci kanmu a dandalin yanar gizo da shafukan sada zamunta za ka yarda idan na ce a yanzu an fi shiga ruɗani a dalilin yawaitar bayanai, da sanin halin da wani yankin da wasu al’adun ke ciki.

Ɗaya daga cikin abun da yake damun matasa a halin yanzu shi ne me za su yi in sun gama makaranta? Sana’ar hannu ko aiki ko kasuwanci? Idan sana’ar hannu ce wacce iri za su koya? Idan aiki ne wanne irin aikin kuma wa zai nema musu? Idan kasuwanci ne wacce irin kasuwa kuma a ina za su samu jari? Shin suna ma buƙatar kwalin digiri ɗin ma kuwa?

Duk a baya mun yi ta fama da irin wannan tunanin kuma har yanzu ma ba mu bari ba. Domin mutum daga ya samu abun da yake nema hankalinsa yana komawa kan abun da zai nema na gaba. Mutane da yawa da suke aiki ko kasuwa ko leburanci suna da tunanin cewa wannan abun ba ya riƙe su ko ba ya kawo musu kuɗin da suke tsammani, don haka yakamata ace sun canja wannan abun, ko sun ƙara da wani da zai dinga cike giɓin.

Idan da mutum zai zo neman shawarata kan sana’ar da yakamata ya yi kai tsaye ba zan iya ce masa ya yi kaza ba. Ba ni kaɗai ba, mutane da dama in ka same su za ka ga ba abu guda ɗaya da za su iya ce maka ka yi, domin su ma ba su sani ba. Misali, a shekarun baya wasu abokaina suna ce min yakamata ka tashi tsaye, kar ka dogara da aikin koyarwa kaɗai, talauci zai danne ka, ka dinga buga-buga. Duk lokacin da na tambaye su me suke nufi da na tashi tsaye? Wacce sana’a zan yi? Ta ya zan fara buga-buga? Da sauaran tambayoyi sai na ga sun yi turus, sun rasa me za su ce, daga ƙarshe ma sai su ce kai za ka duba… (hahahahah!) turƙashi!

Wannan amsar da suke bayarwa ta kai za ka duba ita ce ginshiƙin wannan rubutun, ma’ana mai karatu ka sani rayuwarka nauyinka ce, kai ne za ka duba abun da ya dace da kai, ba dole sai ka bi abun da kowa yake faɗa ba. Zaɓin sana’ar da za ka yi ya danganta da kai wane ne, burukanka, inda ka taso, shekarunka, iyalanka da matakin da kake a rayuwa yanzu.

Sana’ar hannu

Idan na ce sana’ar hannu ina nufi sana’o’in hannu, kamar su ɗinki, ƙira, saƙa, kanikanci, kafinta, gini, gyaran wuta, haɗa sola, graphics design, web design, content writing, da sauran duk wani abu da mutum zai koya ya dinga yi da hannunsa ana biyansa.

Lokacin da ya fi dacewa matashi ya koyi sana’ar hannu shi ne lokacin da bai san daɗin kuɗi ba, kuma babu nauyi a kansa, sannan bai fara kula ƴan mata ba, kana bai kammala karatu ba bare ya yi girman kai. Idan mutum ya fara koyon sana’ar hannu a wannan matakin na rayuwarsa, zai zama gaba ɗaya tunaninsa yana wuri ɗaya ne, sannan a dalilin ƙanƙantarsa, ba zai ji wani abu ba don yana hidimtawa uban gidansa da yi masa biyayya.

A ɗan iya abun da na karanta na labaran mutane, na fahimci cewa mafi yawancin mutanen da suka samu ƙwarewa ko shahara a wani fanni da wuri, sun fara shi ne tun suna ƙanana, kullum shi suke yi, ba fashi, kuma shi kaɗai.

Sana’ar hannu matsalarta guda ce, in ƙarfinka ya ƙare, ko zamani ya juya ba ku juya tare ba, sai ka ga an daina yi da kai, don haka wanda ya fara yana ƙarami, ana tsammata masa zai yi abun kansa da wuri a sana’ar har ma ya kafa wasu, shi kuma ya shiga wata kasuwar da rarar kuɗinsa.

Idan kana wannan matakin na rayuwa, ina ba da shawarar ka fara da wannan. In kuwa ka wuce nan, amma kana jin a ranka za ka iya jure akwai da babu duk da tulun buƙatunka, sannan za ka iya haƙurin jure wulaƙancin wanda kake koyo a wurinsa (kamar yadda wasu ke ɗauka wai wulaƙanci ne), to za ka iya jarraba sa’arka. Ko da sana’ar nan digital skill ce kuwa fa, domin ita ma ai aikin hannu ce, tana buƙatar ƙwarewa, sanuwa, da haƙurin koyo daga masu koyarwan.

Aiki

Idan ba za ka iya jurewa koyon sana’ar hannu ba saboda girmanka, to a shawarce aiki ne ya dace ka nema. Duk da suka da aikin gwamanti da na kamfani suke sha daga wurin mutane da yawa, amma suna da wata rana guda ɗaya. Idan ka riga da ka girma, nauyi da buƙatu sun fara hawa kanka, abun da zai yi saurin rufa maka asiri shi ne aiki, domin kuwa kana fara shi za a biya ka albashi a ƙarshen wata.

Wani abokina ya taɓa ce min yana son su yi kasuwanci kiwo shi da wani, amma shi yana aiki, wancen kuma ba ya yi, ya yi ta binsa yaga kamar ba ya so. Abun da na ce masa shi ne, to ai yana da buƙatu, ka ga kiwo kuma sai an jira, wataƙila wannan yake dubawa.

Matsalar aiki shi ne kafin a same shi. Domin aikin yana wahalar samuwa. Wasu sun gama karatun tun da daɗewa suna jiran abun da Allah zai kawo. Akwai wani rubutu da na yin kan dalilan da suka sa aikin yi ke wahalar samuwa za ku iya karanata shi a nan don ƙarin haske.

Abun shi ne, gama makaranta ba tare da mun iya wani abu ba yana daga abun da yake sa muke gani aikin yi ya yi wahala. Bayan haka kuma muna ɗaukar kanmu yanzu mu ma fa mun kai wani mataki a rayuwa, don haka ba kowanne irin aiki za mu iya ba. Amma alal haƙiƙa, ana samun ayyuka, ko da ba na gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu ba, akwai ƙwadago. In dai mutum zai yi haƙuri da ɗan abun da zai samu, ya ɗauki hakan a matsayin matakin farawa, yana mai kuma gina kansa a sirrance don ya matsa matakin gaba, abubuwa za su zo masa da sauƙi in sha Allahu, musamman in tun yana gab da gama makaranta ya fara wannan tunanin na neman aiki.

Kasuwanci

Idan ba ka taso a kan harkar kasuwanci ba tun kana ƙarami to shi ma yana da illa kamar aikin hannu, wato dole ka haƙura da duk buƙatunka ka raine shi. Kasuwa akwai albarka, duk tulin mutanen da muke gani a cikinta kowa rabonsa yake zuwa samowa, kuma Allah yana ba su.

Jari yana daga cikin abubuwan da yake ci wa matasa tuwo a ƙwarya a lokacin da suka nufi fara kasuwanci. Za ku iya karanta rubutuna a kan dalilan da ke sa a hana matashi jari don samu fa’ida.

A ra’ayina, jari ba iya kuɗi ba ne, ƙwazo, gaskiya da amana, duk su ma jari ne ga mai sha’awar fara kasuwa. Idan kana da wani tunani na wani kasuwanci, musamman a wannan zamanin na digital marketing, ka shiga kasuwa ku yi yarjejeniya da masu kaya, kana musu talla, suna ba ka kamasho in an siyar. In kuma akwai inda za ka iya zama yaron shago to ka daure ka je ka zauna a wurin. Ɗan abun da ka samu na kuɗi, da ilimin kasuwancin da ka samu a wannan lokacin da kake ƙarƙashin wani, su ne jarinka. Kafa naka da za ka yi bayan an yaye ka shi zai sa har wani ya ga ka burge shi ya ƙara maka jari (ta hanyar kyauta, aro, ko sa hannun jari).

Bana so rubutun ya yi tsawo da yawa, amma akwai misalai da yawa na abubuwan da nake ƙoƙarin haskawa. Babban abu dai shi ne, mutum ya duba kansa, da matakin da yake a rayuwa. In kana da juriya da ladabi da biyayya kuma ba nauyi sosai a kanka, ka koyi aikin hannu, ko ka zama yaron shago ko ka fara ƙwadago.

In kuwa kana da nauyi a kanka, ko kuma ba za ka jure waɗancen abubuwan ba, ko ba ka da lokacin koyo, to ka nemi aiki, amma ka tabbata ba ka bari neman aiki ya zama aikinka ba. Ka ƙulla alaƙa da mutane, alaƙa mai kyau ta yadda daga sun ga wata dama za su ma magana ka jarraba sa’arka. Don wani bai samu ba, ba ya nufin kai ma ba za ka samu ba, kowa rabonsa yake ci.

A yadda yakamata, yadda rayuwa ta nuna yanzu, son samu kowa kowa ya taso da sana’arsa, in hakan bai yiwu ba to a daure a koyi wani abu gab da za a gama makaranta, ko da zarar an gama. Idan an riga da an wuce lokacin wannan, to sai a koma zuwa ga duban me ya dace daga abubuwan da na lissafa a sama.

Arziƙi nufi ne na Allah, ba shi da alaƙa da wanne irin neman kuɗi kake, a ko’ina rabonka zai iya zuwa ya same ka, kuma ma kai da ka san dole sai ka cinye arziƙinka a duniya kafin ka mutu mene ne zai dame ka? Ka koyi tattali, kyauta da sadaƙa, ka nemi sirrin yadda ake haɓaka dukiya a wajen waɗanda suka riga suka haɓaka tasu, sai ka bar wa Allah sauran. Ko da ka haura shekara 30 matuƙar kai mai tsawon rai ne, ba za ka cire rai da samun taka damar ba a gaba, kai dai ka yi aiki, irin aikin da ake yi a samu abun da kake nema, da sannu rabonka zai zo.

Wannan batu ba ƙarshensa ba ke nan, zan sake waiwayarsa a wani lokaci na gaba in mai dukka ya amince, domin har yanzu ban amsa tambayar “Wacce irin sana’a zan fara?” ba, don ni ma ban san amsar ba, kai ne ka san kanka da muradanka. Duk abubuwan da na faɗa ra’ayina ne kawai, ba lallai su zama gaskiya ba, ina maraba da gyara ko ƙarin haske daga gare ku. Na gode.