“Na rasa meyasa babana ya ƙi ba ni jari, in da zai ba ni jari ai da yanzu nima ina ta jujjuya kuɗin a business’’ ya ce da abokin tattaunawarsa.
Watarana na je wani shago zan yi siyayya, sai na tarar da wani matashi suna tattaunawa da wani, yana Æ™orafi a kan yadda wani ya yi kane-kane a kan harkokin babansa, shi kuma baban ba ya É—aura shi a kan harkokin. Har yana ganin ma an fi yarda da wancen a kansa a matsayinsa na É—an gida. A lokacin ne yake furta waÉ—ancen kalaman da suka gabata a farko.Â
Irin wannan ƙorafin ba sabon abu ba ne, mutane da dama suna zargin iyayensu ko wasu na kusa da su da daƙile su, suna ganin cewa an ƙi barin su su gwada, ko an ƙi ba su dama ne balle a ga me za su yi. Irin wannan ƙorafin a mafi yawancin lokuta ana yin sa ne don mutum ya rufe gazawarsa, ya ba wa kansa hanzari.
Haka yawancin matasa musamman waÉ—anda suka yi karatun boko suka tsinci kansu, sun gama makaranta aiki bai zo ba, abu na gaba da za su fara tunani shi ne a ba su jari su jarraba kasuwa tunda aikin ya yi wahalar samuwa.Â
Akwai abubuwa da dama da suke hana irin waÉ—annan matasan samun jari, yawancin matsalar daga gare su ne, amma suna jinginawa wasu laifin. A wannan rubutun zan kawo kaÉ—an daga cikin dalilan da za su iya hana ka samun jari a matsayinka na wanda ya gama makaranta yana jiran samun aikin yi.
Tsakaninka da kuÉ—i kisa ne
Na taɓa faɗa wa mahaifina ina son yin kasuwanci, tambayar farko da ya fara yi min ita ce a ina zan samu jari? Abun shi ne babana ya sanni, ya san kuma ina samun kuɗi a koyarwar da nake, ya san na yi bautar ƙasa, dan haka yana so ya ji ko ina da wasu kuɗi ajiyayyu ne da zan yi jari da su.
Yawancinmu da ake É—aukar nauyin karatunmu ba mu saba da adana kuÉ—i ba, balle a je ga batun juya shi. Ba ma ya cikin lissafinmu, domin mun san daga mun shiga matsalar kuÉ—i kiran waya É—aya ko biyu zai warware mana.
Idan muka gama makaranta, har muka gama hidimar ƙasa ba tare da muna da wata ƙwandala a ajiye ba, ba wanda za mu je mu ce masa muna neman jari ya kalle mu, domin abu na farko da zai fara faɗowa ransa shi ne, wannan fa kashe kuɗin zai yi kamar yadda ya saba.
Kowa yana son kansa sama da waninsa, babu wanda zai iya cire kuÉ—insa ya bayar don a salwantar masa da su.
Ba ka komai a kan kasuwancin da kake tunanin farawa
Mutane da dama bayan sun gama makaranta sukan ta tara business ideas, amma ba sa yin komai a kan kowacce idea. Dalilin farko da za su ba ka in da za ka tambaye su shi ne ba su da jari.
Wani abu da ba mu sani ba shi ne, duk wanda bai ga kana hoɓɓasa ko faɗi tashi wajen ganin ka cimma burinka ba, ba abun da zai iya yi maka, domin kai da kanka ka nuna masa ba da gaske kake ba, ta ya ya shi zai ɗauka da gaske kake?
Abun da ya faru tsakanina da mahaifina shi ya fara farkar da ni daga baccin da nake, don haka na duƙufa kan aiki a kan ideas ɗina, kuma nake ajiye kuɗi dominsu.
Dangote kawunsa ne ya ba shi jari, ban iya kiyaye adadin kuÉ—in ba, amma ba haka kawai ya É—auka ya ba shi ba, saboda ya san shi a matsayin mai faÉ—i tashi kan kasuwanci tun kafin ya gama karatu.
Ba ka yadda da farawa kaÉ—an ba
Lokacin da na fara business ɗin sayar da takalma 50k ce da ni, a cikinta ne na je na sayi wasu takalma na fara kasawa a kasuwa. Duk da cewa daga baya na yi saurin ƙara jarin saboda rashin ƙwarewa, wanda inda na ɗan ba shi lokaci, da zai fara ƙaruwa da kansa kafin na ƙara shi.
A hulÉ—ata da abokanaina da suka kwana biyu a kasuwanci, na gane cewa ba dole sai da kuÉ—i mai yawa za ka fara ba, hasalima tsayawa jiran kuÉ—i masu yawa ne yake hana mutane da yawa yin komai a kan idea É—insu.
Duk wanda bai taɓa juya 30k ba, kuskure ne ya zauna yana jiran a ba shi 500k ya fara business, don babu wanda zai taɓa bashi waɗannan kuɗin haka siddan ba tare da ya ga wata hujja da ke tabbatar da kuɗin za su juyu ba.
Akwai Æ´an kasuwa daga cikin masu gidajen mai da wasu za ka ji ance daga jan tankar mai suka fara, haka nan a singa a Kano akwai waÉ—anda daga yaran shago suka fara, ba za a rasa ma waÉ—anda suka fara da dako ba fa, tunda wasu ma asalinsu almajiranci ne ya kawo su garin.
Ba ka nemi jari a inda ya dace ba
Mutanen da za su iya ba ka jari ba ma’aikata ba ne, waÉ—anda iya aikin suke yi ba wata sana’a, ba kuma Æ´an siyasa ba ne, waÉ—anda iya abun da zai taimaki burinsu suke dubawa.
Alal haƙiƙa, ɗan kasuwa, wanda ya taɓa gina wani kasuwanci, kuma ya yi nasara, shi ne wanda ya fi dacewa a nemi jari a wurinsa.
Sai dai irin mutanen nan matsalarsu guda ɗaya ce, suna buƙatar ka zo da wani sabon salon kasuwanci, ba wai ka yi abun da kowa yake yi ba, sannan ka ce za ka nemi kuɗi masu yawa.
Saboda gogewarsu kana fara magana za su iya gane cewa da gaske kake, ko kuÉ—in kashewa kake nema kawai, za su gane ka san a kan abun da kake magana, ko romon baka kake musu.
Yawanci abun da suka fi la’akari da shi shi ne gwagwarmayarka, yadda ka san ciki da wajen kasuwancin, matakin da yake yanzu da kuma Æ™warin gwiwar da kake da shi kan cin nasara.
Idan idea É—inka ba sabuwa ko ‘revolutionary’ ba ce, shawara ka nemi kuÉ—i É—an kaÉ—an a hannun Æ´an’uwa ka fara, kada ma ka tunkari masu saka hannun jari.
Ka yi saurin sarewa ko ka É—auka an daina taimako
Wani zai ce to ai duk abubuwan nan da aka faÉ—a ba ni da matsala da su, amma har yanzu na rasa mai taimaka min. Ba mamaki ko dai ka sare da wuri ne, ko kuwa dama a ranka ka É—auka an daina taimako.
Ba lallai ne ko da ka cika sharuɗɗan da za su sa a gamsu a baka jari ba a baka, wannan ya sa dole sai ka zama ba ka da saurin sarewa, in ka tuntuɓi wannan ba ka samu ba, sai ka tuntuɓi wannan, a haka har a dace.
Haka nan in ka É—auka cewa mutane sun daina taimako shi ma ba za ka samu jari ba, domin wannan tunanin ba zai bar ka ma ka jarraba gwada nema ba, balle ka samu.
Akwai investors suna nan suna ta jiran wanda zai zo da dalilan da zai gamsar da su su cire kuɗinsu su ba shi, ina da abokan da suke business, ba da kuɗinsu ba, amma ba za ka taɓa ganewa ba.
Ina ganin ko a nan na dakata na bayyana manya daga cikin dalilan. Mafita shi ne yin akasin kowanne dalili, ka gamsar da Æ´an uwanka da iyayenka da abokanka kan cewa duk abun da ka sa a gaba sai ka ga abun da ya turewa buzu naÉ—i, a sanka a matsayin mai faÉ—i tashi kan kasuwancinsa, to ko su ba su ba ka ba, za ka samu mai ba ka jari in dai ka nema, wasu ma su za su neme ka su ba ka, ba haka kawai na faÉ—a ba, na san wanda hakan ta faru da shi.
Ka tanadi kuɗi ka fara abun da kake son yi, kafin ka nemi taimakon wani, hanyoyin tanadar kuɗi suna da yawa. Za ka iya farawa da wani abu da ba ya buƙatar jari, kamar aikin hannu ke nan, daga cikin abun da kake samu sai ka dinga ajiye wani kaso har ya kai daidai yadda za a fara kasuwanci da shi. In ma ba ka aikin hannu, kuɗaɗen da kake ɗan samu nan da can a ciki za ka iya ajiye wani ka ɗan fara.
Ba ka bukatar farawa da kudi masu yawa, domin yawancin business ɗin farko asara ake yi, in ka zuba kuɗaɗe da yawa asarar za ta maka jijjigawar da ba za ka sake yunƙurin gwada wani abu ba, wannan ya faru da ni a lokacin da na fara business na smoked fish, idan da ace na sa kuɗi masu yawa da har yanzu ban farfaɗo ba.
Addu’a da neman taimakon Allah kan komai shi ne gaba da komai, kada ka sa girman kai wa kanka, kar kuma ka bari wasu su sa maka, ka fara da duk abun da ya samu ko babu tabbas É—in bullewa, darasin da za ka samu ya fi kuÉ—in da za ka rasa muhimmanci.