A ƴan kwanakin nan na lura mutane suna ta yin tsokaci kan malaman islamiyyu da yadda ba a biyan su haƙƙinsu yadda ya kamata, har ma wasu suna kiran ustazai da su tsaya da ƙafafuwansu (ma’ana su nemi kuɗi).
Ba iya makarantun islamiyya ba, hatta ƙananun makarantu masu zaman kansu suna yi wa malamansu biyan wulaƙanci. Abun bai tsaya iya kan waɗannan ba, ko a cikin ma’aikatan gwamnati a wasu wuraren za ka samu malaman makaranta su ne mafi ƙarancin albashi.
Ba haka kawai ba ne hakan ke faruwa, ba kuma ko don an raina abun da suke yi ba ne ya sa ake musu wannan cin kashin. A lokacin da nake hidimar ƙasa, na yi tunanin koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta, da muka je muka tattauna da shugaban makarantar, sai na ga abun da zan dinga samu bai wuce na sa kati da siyan sabulun wanki ba.
Ba ni kaɗai ne matashin da ke tunanin da zaman haka bari ya je wata makaranta ya ɗan dinga rage lokaci ba, abun da zai ɗan samun duk da ya san bai taka kara ya karya ba, amma yana ganin dai da ace ba a yi, gwara ana yi ko ya ya ne. Sai dai mutane da yawa sukan manta cewa da muguwar rawa fa gwamma ƙin tashi in ji Bahaushe, kuma ni ma wannan tunanin ne ya hana ni karɓar wannan aikin na koyarwar, sai na koma makarantar gwamnati nake zuwa a matsayin ɗan sa kai “volunteer”.
Mutane da yawa za su iya
Dalili na farko da zai sa a maka biyan wulaƙanci a kowanne irin aiki kake shi ne idan ya zama abun da za ka yi mutane da yawa da za su iya. Kamar yadda muka sani yawaitar abu yana karyar da farashinsa, hakan ne ya faru ga malamai.
Ga abun da nake nufi, an yi wani lokaci a baya da waɗanda suka faɗi “JAMB” ko “WAEC” ne suka fi tafiya karatun harkar malumta wato NCE, har ta kai ana kiran wasu makarantun da gidan biki. Bayan haka, hukumar kula da masu hidimar ƙasa ta NYSC takan tura masu hidimar ƙasa makarantu masu zaman kansu don koyarwa. Ke nan dai an yi yawa a fannin koyarwa, da waɗanda suka san abun da suke, da waɗanda ba su sani ba, kowa ana ba shi alli da littafi ya koyar.
Na buga misali da koyarwar domin shi ne za mu fi saurin ganin misalin a zahiri, don haka ka ɗaura wannan a kan kowanne aiki kake yi. Idan dai mutane da yawa za su iya, to wanda ya ɗauke ka aiki ba zai damu ba, don ya san ko ya rasa ka ba tare da ɓata lokaci ba zai maye gurbinka.
Ba ka da mamora
Dalili na biyu da zai sa a maka biyan wulaƙanci a matsayinka na ma’aika ce shi ne idan ya zamto kai a karon kanka ba ka da mamora. Ma’ana ba ta wani wuri da kake kawo ci gaba wa ma’aikatar.
Kafin a yi mafi ƙarancin albashi na dubu saba’in, 70k, a Najeriya, ma’aikatun gwamnatin tarayya da yawa albashin sabon ɗauka da digiri dubu 60 zuwa 70 ne. Abun da ma fi yawancin mutane ba su sani ba, akwai ma’aikatun gwamnatin tarayya da ake biyar sabon ɗauka da digiri a daidai wannan lokacin albashin dubu 300-400 a wata, ban da sauran alawus na gida, sutura, abun hawa da sauran su.
Mene ne bambacin ma’aikatar da ba a biyan albashi mai tsoka da wacce ake biya? A wajen gwamnati ma’aikatar farko ba ta da wata mamora sosai, ba ta kawo kuɗi, ta biyun ce ake ganin ta fi mamora saboda tana cika lalitar gwamnati. Ba iya gwamnati ba, ko a ma’ikatu masu zaman kansu, ana samun masu biya da tsoka, ana samun kuma waɗanda ba sa biya yadda ya dace. Ba a jima ba wani abokina ya ce min an masa tayin aiki a banki a matsayin software Engr, miliyan ɗaya a wata za su biya shi. Wannan fa digiri ne da shi sai kuma ƙwarewa da yake da ita a fannin.
Idan mai karatu yana fahimtata, duk wani wuri da za ka yi aiki in dai ka zama ba ka da wani abu na ci gaba da za ka kai wurin, to tabbas ba za a biya ka da tsoka ba (sai dai in na gwamnati ne, da ita takan biya mutane bai ɗaya ba tare da duba waye yake abun da ya dace ba, ko itan ma mun dai ji akwai ƴar mowa da ƴar bora a ma’aikatunta).
Mafita
Ai kowacce matsala maganinta shi ne a san me ya jawo ta a karon farko. Idan saboda mutane da yawa za su iya abun da kake yi ne ya sa ba a biyanka yadda ya dace, to ka yi abun da sauran ba sa yi. Misali in kai malami ne, ka koyi abubuwan da suka shafi content creation, ka dinga bidiyo kana ɗaurawa a Youtube ko duk wata manhaja da za ta jawo maka mutane. Idan ka kai wani adadi za su fara biyanka, sannan mutane za su san ka a wannan fannin, don haka in wani abu ya tashi da ake neman ƙwarewa a fannin sai ka ga an sako da kai. Wato dai in kana da kyau ka ƙara da wanka.
Idan mun duba lamarin ustazai da na kawo a matsayin misali, ka je Abuja ka gani, kwashewa suke yi, saboda can samun inda yara za su yi karatu mai inganci yana da ƴar wuya, ba kuma kowa ne zai jure kashe kuɗin “transport” don jigilar yara zuwa islamiyya ba, don haka ustazan sai suka zama suna da abun da ake kira “value”. Yadda na ji ma a wani wurin ana biyan su “per head” ne, wato gwargwadon yawan yaran da suke koyarwa.
Idan kuwa rashin mamora ne matsalarka, to ka nutsu ka canja wa kanka rayuwa ta hanyar koyon abubuwan da za su ɗaga ka, a rarar lokacinka. Idan dai har ma’aikatar tana biyan mutane saboda ƙwazonsu, to ka ƙware a wani fanni da dole sai an dama da kai. Idan kuwa wajen gaba ɗaya a bushe yake, to ka koyi wani abu da zai ba ka damar canja layi, in wuyanka ya yi kauri a fannin, to duk inda ka je rububinka za a dinga yi. Mu fahimta ba wanda ya damu da wahalar aikinka, kowa ya damu ne da ta yadda kake warware matsala ko kawo ci gaba a wurin.
Ina fatan waɗannan abubuwan da na kawo za su taimaka wajen warware waɗannan matsaloli. Idan da wani abu da ban kawo ba za ku iya ƙara mana shi a sashin tsokaci. Mun gode.