Bahaushe ya ce rashin sanin daɗi shi ma daɗi ne. Wanda bai san zafin bauta ba, ba zai san daɗin ƴanci ba. Mutane da yawa suna da masaniyar a zamanin baya masu kuɗi ne kawai suke iya siyan fili a gidan radiyo, shafin jarida, ko gidan talabijin domin su tallata hajarsu. Kafin zuwan yanar gizo ba ka isa ka tallata sana’arka da kuɗi ƙalilan duk yadda kake so kuma a lokacin da ka so ba, kamar yadda yake faruwa a yanzu.

Sai dai mutane da yawa ba su san cewa yadda sai mai kuɗi ne yake iya samun hankalin mutane ya kai ga hajarsa, akwai wani lokaci da ilimi sai wane da wane. Dalilan da suka kawo hakan kuwa sun haɗa da keɓance wasu mutane da aka yi, wato manyan gari, aka yarda su kaɗai ne suka cancanci ilimi. Akwai kuma rashin wadatuwar littafi da kayan koyo saboda ƙarancin fasaha da ƙarancin malamai. Haka nan yawan yaƙe-yaƙe, sana’o’in hannu na gado, matsin tattalin arziƙi, imani ko addinai duk sun taimaka wajen killace ilimi ga wasu gungu na mutane su kaɗai.

Ke nan in da a wancen zamanin muka zo, yawancinmu da muke raina ilimin da muka samu a makarantu da yanzu ba mu ma da ƴanci ko damar samun yin karatun. Wani hanzari ba gudu ba, akwai bambanci tsakanin makaranta da kuma ilimi. Makaranta a wannan zamanin tana nufin wurin da gwamnati ta yarje a ba da shaidar kammalawa ga wanda ya halarce ta na wani adadin shekaru, ya cika duk sharuɗɗan da ake buƙata don a ba shi wannan shaidar. Shi kuwa ilimi shi ne abun da aka fita da shi bayan an gama makarantar, ko da ba shi ne fannin da aka je karanta ba a makarantar.

Idan mun fahimci wannan bambancin, za mu iya cewa makaranta suna ta tara, ilimin shi ne abun da ya fi muhimmanci. Shi kuwa ilimi ba dole sai a aji ba, a ko’ina kuma a koyaushe a kowanne hali kullum cikin samun ilimi muke. Idan kuwa haka ne zan iya cewa tabbas shafukan yanar gizon da zan lissafa za su fi maka kwalin digiri in dai magana ake ta ilimin tsagoransa.

Google (google.com)

Ba za ku yi mamaki ba idan na ce iya amfanin da shafin google a wannan zamanin ya fi yin shekara biyar a makaranta. Babban aikin google shi ne taimaka mana wajen laluben duk wani abu na ilimi da muke nema, duk abun da ya shige mana duhu muna shiga Google za mu same shi.

Duk abun da muke nema na ilimi, ko littafi, ko ƙarin haske kan wata matsala, ko sanin sabbin bincike da wasu suke yi, ko jinga aka ba mu a makaranta, ko wani “skill” muke koyo muka tuƙe, muna zuwa Google zai wahala a ce mun rasa wani bayani a kai da zai ba mu haske, in ma ba mu samu gaba ɗaya amsar mu ba ke nan.

Youtube (youtube.com)

Youtube jami’a ce mai zaman kanta. Duk wani abu da kake son koya, idan ka shiga Youtube ka lalube shi za ka samu bayanai kaca-kaca, wasu sun ɗauki lokaci sun yi darasi a kan wannan abun. Haka nan ko da wani aiki kake ka tuƙe, kana shiga Youtube za ka ga mafita (solutions) kala-kala da wasu suka yi kan wannan abun.

Wani abun burgewa da Youtube shi ne yana gane me kake yi a cikinsa. Idan kana koyon webdesign zai dinga kawo maka bidiyo na webdesign, in ɗalibi ne kai za ka ga an karantar da course cikakke a sauƙaƙe da kuka kasa ganewa a aji, kana kallon ɗaya zuwa biyu Youtube zai ci gaba da nuna ma su har sai ka ture. Kai hatta lissafi, “practicals” da ake yi a “laboratories” duk za ka samu a Youtube an yi bayani dakki-dakki, kana gani.

ChatGPT (openai.com/chatgpt)

A wannan ƙarnin da ƙirƙirarriyar fasaha ta shiga cikin komai, kuskure ne babba kana matashi a ce ba ka iya amfani da chatGPT ba. Shi chatGPT an horar da shi ne da bayanan da suke tattare a duniya gwargwadon samuwarsu ga wanda suke ƙirƙire shi. Duk abun da ya shiga ma duhu tambayarsa za ka yi kawai ya warware ma biri har wutsiya.

Iya sarrafa chatGPT yana buƙatar ilimin “generative ai” ko  “prompt engineering”, wanda shi ne zai ba ka damar ka yi amfani da kalmomin da suka dace don samun amsar da ta dace da yanayinka. Wani abun burgewa shi ne a yanzu kamfanin Openai sukan bayar da damar tatso bayanai daga GPT-4 na wasu awanni a rana, wanda in yana ba ka amsa za ka ji kamar a gaban wani masani kake.

ChatGPT ba iya amsa tambaya yake ba, yana ba da shawarwari, yana koyar da skill, da warware sarƙaƙiya, a yanzu haka ma har shafin yanar gizon da za ka samu ƙarin haske daga masana zai ba ka. Wasu ma har timetable da to-do list suke haɗawa da shi.

Shin da gaske har zuci na yarda waɗannan shafukan sun fi kwalin digiri? To, ba burina na shiga cikin hayaniyar sana’a ta fi digiri ba ne, ko cikin masu cizon yatsa kan sun yi makaranta amma har yanzu ba su yi kuɗi ba. Mu tambayi kanmu, ta ya ake tara ilimi? Tabbas ana tara ilimi ne ta hanyar tattara bayanai, bayanan nan su sanar da mutum ko su koya masa wani abu, idan suka yi yawa a tare da shi, kuma ake ganin aikinsu a rayuwarsa, to ya zama mai ilimi. Idan kuwa wannan shi ne hanyar samun ilimi zan iya cewa waɗannan shafukan sun fi kwalin digiri mayar da matashi mai ilimi na haƙiƙa matuƙar ya naƙalce su.

Wasu za su ce to in haka ne duk wanda ya iya amfani da su sai ya yaga kwalin digirinsa (hahaha!). Manufar wannan rubutun ita ce zaburar da matasa mu san cewa Allah ya maan ni’ima da ya yi mu a wannan lokacin, don mu mayar da hankali wajen cin gajiyar hakan maimakon ɓata lokutanmu a inda ba za su amfana ba. Idan kuwa kai a ranka ka san ba ka da buƙatar kwalin digiri, to ka naƙalci waɗannan shafukan, za ka samu ilimi na ban mamaki. Zan so na ji ra’ayoyinku kan wannan batu a sashin tsokaci. Na gode.