A gaba ɗayan rayuwata, ina kallon ta inda na bambanta da mutane sosai, wannan bambancin har ya sa a da nake tunanin anya daidai nake kuwa. Sai daga baya nake gane cewa tabbas daidai nake, kawai na zaɓi na yi iya abun da nake ganin ya dace da ni ne a rayuwata, ba tare da na kallafawa kaina yin rayuwa kamar sauran mutane ba.
Idan ka ga mutane suna yayin wata sutura, da mai hali da marar hali duk suna ta faɗi tashin ganin sun mallaki wannan sutura, ko suna yayin karantar wani fanni a makaranta, ko suna yayin mallakar wata waya, ko abun hawa, ko yayin bukukuwan kece raini, ko yayin wani dandalin sada zumunta, sai kai ma ka shiga ba tare da sanin ta inda za ka amfana ba, to akwai yiwuwar rashin iya amfani da wannan kalmar.
Wacce kalma ce wannan? Wannan ba wata kalma ba ce face kalmar “a’a”. Duk wanda bai iya faɗin a’a ba, a aiki ko a magana, to zai zama kullum cikin bin yarima ya sha kiɗa a rayuwarsa.
Sutura
Don kowa na ɗinka shadda misali, sai ka ga kai ma to ai ba su fi ka da komai ba, bari kai ma ka fara ɗinkawa ba tare da ka duba me ka fi buƙata ba a halin da kake ciki, ba tare da ka duba aljihunka ba, ba tare da ka duba irin ɗawainiyar da shadda ke buƙata ba bayan an ɗinka ta ba, to ka gaza wajen amfani da kalmar a’a.
Biki
Lokutan bukukuwa lokaci ne na yin abubuwan kece raini, a nan wanda ba shi da gashin wance yaki damun kansa sai ya yi irin kitsonta. Duk wanda ya iya faɗin a’a a lokacin biki ya hutar da kansa. Ba dole sai ka je ɗaurin aure ba don kowa zai je, ba dole sai ka yi anko ba don kowa na yi. Ba dole sai ka yi dinner, da sauran events da ake yi ba don kowa na yi.
Ko da lokacin hidima ne, yana da kyau ka dinga duba abubuwan da ba su ci karo da imani da manufarka ta rayuwa ba, ka kuma duba ƙarfin aljihunka. Wanda ya kasa faɗin a’a kan abubuwan da ba su da ce da shi ba, dole zai afka cikin matsala da dana sani daga baya.
Dandalin sada zumunta
Dandalin sada zumunta yana cikin wuraren da muke saurin ɗaukar yayi da aron rayuwar wasu mu yafa. Misali, duk da kowa na Facebook, amma a shekarar 2017 da na ga nawa asusun ba ya taimakata wajen cimma komai goge shi na yi. Na rasa abubuwa da yawa ko? Wataƙila dama ba na buƙatarsu ne.
Abu ne mai sauƙi ka ga mutum yana Fesbuk, IG, X, Snapshot, Tiktok, Linkiden, Telegram, da sauransu don kowa na yi. Shi ba content yake ƙirƙira, bibiyar masu ƙirƙira yake yana nishaɗantuwa. Wanda ya mayar da dandalin sada zumunta wurin samun nishaɗi da rage lokaci tabbas ya gaza ne wajen amfani da kalmar a’a, inda yana amfani da ita da ya tace ya reraye, ya zaɓi abun da zai dace da manufarsa.
Ko tallace-tallace da ake yi a dandalin sada zumunta, akwai abubuwan da ba ma buƙatarsu, kawai kyan tallar zai burge mu, ko kuma munga kowa na siya sai mu saya. Mu fahimta, dandalin sada zumunta wajen neman kuɗin wasu ne, duk lokacin da kuwa ka fi ba sana’ar wasu muhimmanci sama da taka, to ka shiga matsala.
Kallo/Wasanni
Hatta harkar wasanni da kallon fina-finai ko kallon wasannin rashin amfani da a’a yana daga cikin abun da ke sa mutane su shagala a harkar kallo. Daga an fitar da sabon series da za su iya cewa a’a, su yi amfani da lokacinsu wurin da ya dace, da ba haka ba.
Wasu saboda sa harkar wasa a rai duk inda suke komai muhimmancin abun sukan iya barinsa su shiga gidan kallo, ko da ace za su iya ganin wasan ta waya, sun gwammaci su shiga gidan kallon su kalla tare da mutane, hujjarsa kawai kowa can yake zuwa, kuma kallon ya fi daɗi a haka.
Wanda bai iya cewa a’a ba, ba lallai ya iya cin moriyar lokacinsa, dukiyarsa, alaƙarsa, iliminsa ko dabarar kasuwancinsa yadda ya kamata ba. Akwai alfanu a cikin amfani da kalmar a’a, za ka samu salama a rayuwa, za kuma ka daina ɗaga hankalinka kan sai ka yi wani abu da mutane ke yi don kawai suna yi, ba don kana buƙatarsa ko zai taimaki manufarka ba.
Idan da wani amfani na kalmar a’a da kuka sani da ba mu bayyana ba, za ku iya sa mana su a sashin tsokaci. Allah muke roƙo ya ba mu ƙwarin gwiwar amfani da wannan kalma a inda ta dace, domin sai da taimakonsa a irin wannan rayuwar da ake yi. Mun gode.