Ina zaune labarin wani mariri ko gada ce (oho) da na taɓa karantawa a wani littafin Hausa shekaru da dama ya faɗo min, ba zan iya tuna cikakken labarin ba kuma ba na kusa da littafin bare na duba, amma ga shigen yadda abun yake.
Wani mariri ne ya je shan ruwa a bakin kogi, sai ya kalli irin halittar da Allah ya masa, ƙahonsa ya birge shi, ya dinga yabon abubuwan kyau game da ƙahon. Bayan ya gama duk yabon da zai yi sai ya iso kan ƙafarsa, da ya ganta ƴar guntuwa sai ya fara kushe ta, yana ganin ita ce ta ɓata masa halittarsa. Kwatsam sai dabbar farauta ta biyo shi, ya ranta a na kare. Ya dinga gudu har ya kusa tsere wa dabbar nan, kawai sai ƙahonsa ya shiga wani surƙuƙi, ya yi ya yi ya fitar da kansa ya kasa har dabbar nan ta iske masa. A sannan ne fa ya gane amfanin ƙafarsa da illar da ƙahon nan da yake ji da shi ya masa. Ban sani ba ko haka labarin yake, ko ba haka yake ba dai za mu ɗauki darussa a wannan.
Ka mayar da hankali kan abun da kake da
Ba cutarwar da ta kai Allah ya maka baiwa ka manta da ita, ka dinga hangen abun da ba ka da shi. Duk wanda hankalinsa ke kan abun da ya rasa ba zai taɓa iya ganin abun da yake da shi ba, bare har ya ci moriyarsa.
Duk abun da Allah ya mana akwai ta inda yake so mu yi amfani da shi. Shiyasa bai yi mu duk iri ɗaya ba ta wajen halitta, halayya har da ma abun hannu. Ka duba ko ciki sahabbai kowanne da akwai ta inda musulunci ya fi amfana da su. Wasu ilimi, wasu ƙarfin hadda, wasu jarumta, wasu dukiya, wasu hikima da hangen nesa, wasu dabarar yaƙi. Idan da kowa sanyin hali ne da shi ko kowa zafin rai ne da shi ya kuke ganin za ta kaya?
To idan kuma da kowa ya tsaya yana raina abun da yake da shi, yana harora wanda ya rasa fa? Kun tuna sahabbai talakawa da suke ganin masu kuɗi sun tafi da aikin lada? Daga ƙarshe Annabi tsira da aminci ce musu ya yi wannan falalar Allah ce da yake ba wanda ya so, bayan ya sanar da su yadda za su ci moriyar nasu lokacin a irin yadda Allah ya ajjiye su.
Godewa Allah
Godiya ta haƙiƙa ba ta yiwuwa ga wanda ya manta da ni’imar da aka masa, ya shagala da abun da ya rasa. Asalin godiya ba iya furtawa da baki ko ƙudurcewa a zuci ba ne, a’a har da aiki.
Idan Allah ya ba ka kuɗi alamun godiyarka bayan ka ci mai kyau ka sa mai kyau, a ga kana tallafawa bayin Allah, a gan ka a hidimar mutane, a gan ka a wajen taimakon Addini. Kai hatta ka dinga hoɓɓasa wajen inganta hanyar samunka shi ma nau’i ne na godiya, kana gode wa Allah da ya ba ka baiwa da tunanin yin kasuwanci.
Idan da maririn nan ya gode wa Allah kan ni’imar ƙaho godiya ta haƙiƙa da ba zai samu lokacin kushe ƙafarsa da take iya kuɓutar da shi duk lokacin da aka farauce shi. Wanda ya gode wa abun da yake da shi ba shi da lokacin damuwa kan abun da ya rasa, saboda farin ciki da jin daɗin abubuwan da yake da su.
Cin moriyar rauni
Daga mutum ya rasa abu, tunaninsa yana karkata kan rashin a maimakon ya duba ta ina zai ci moriyar raunin. Aka ce ɗan hakin da ka raina shi ke tsone ma ido, misali, lokacin yaƙin Jaluta, sun raina su Annabi Dawuda, amma sai ga shi sun yi nasara a kansu.
Wannan dabarar ta cin moriyar rauni marubucin littafin David and Goliath ya yi amfani da ita wajen faɗakar da yadda ƙaramin kamfani zai ci moriyar ƙanƙantarsa ya dinga samun riba fiye da babban kamfani. Idan da maririnmu ya ƙi amfani da ƙafarsa saboda kallonta da yake a matsayin cikas, da kafin ya bar wajen ma an cafke shi.
Wasu rauninsu shi ne ba sa gane karatu, don haka kafin su fahimci darasi har su iya haddace shi, suna buƙatar shafe awanni suna turzawa. Wannan yana koya musu naci da juriya a rayuwa, sannan yana buɗe musu ƙwaƙwalwarsu. Akwai wani “artist” a zamanin baya da duniya take ji da shi, an ce saboda an haife shi ba aure, ba zai iya gadon san’ar gidansu ba, wannan raunin nasa ne ya ba shi ƴancin ɗaukar wancen layin har ya zama zaƙaƙurin da har yanzu duniya take tunawa da shi.
Kar ka tsani kanka
Don ka rasa wani abu baya nufin ka rasa komai, kowa ma ai akwai abun da ya rasa. In da kowa zai tsani kansa don ya rasa wani abu da yanzu duniyar ba ta daɗin zama.
Abun shi ne, ba abun da zai tafi yadda ake so a rayuwarka matuƙar ba ka ƙaunaci kanka a yadda kake ba. Son kai yana daga cikin abubuwa masu muhimmaci da suke taimakon mutum wurin yin abun da zai amfane shi a rayuwa. In ba mai son kansa ba waye zai fita tun safe yana neman abun rufa wa kansa asiri ko da yana shan wahala.
Idan rashin wani abu ya sa mutum ya ƙi kansa, to, ya toshewa kansa hanyar ci gaba, zai zama kullum cikin damuwa, kushe kansa da fatan ya zama wasu da rayuwarsu ke burge shi zai zamar masa abun yi kullum. Ba wanda ya yi wa kansa abun da yake da shi, yadda ka rasa wani abu haka su ma suka rasa wani abu, yadda kake kallonsu wataƙila su ma haka suke ma kallon ka more.
Waɗannan suna daga cikin darussan da za mu koya daga wancen labarin, na tabbata ba iya darussan ke nan ba, za ku iya zaƙulo mana cikin darussan da kuma kuka cira daga labarin don amfanar sauran masu karatu. Allah ya taimake mu.
WannAn rubutu yy sosai Allah qara hazaqa.
amin summa amin, muna godiya