Daga  Zarah A Zamsarf

Tasiri da yanayin irin al’ummar da muke rayuwa cikinta na ɗaya daga cikin abubuwan da ke danƙwafar tare da taka rawa sosai a kan lalacewar al’amurran mutanenmu.

Ina so na yi magana a kan yanayin takura, tsangwama, kyara da tsanar da ‘yan mata ke fuskanta a kan jinkirin Aure, wanda ko kaɗan  ba a nuna kwatankwacin hakan ga maza. Da za a haifi ‘yan tagwaye ( ‘yan biyu ) a family,  mace da namiji, kuma Allah ya raya su su kai har munzalin da za su iya zaman aure, ba za a taɓa damuwa da namiji  a kan rashin auren ba a kan macen, idan shekarunsu ashirin da biyar-biyar, to gaba ɗaya ma shi ba za a fara sa ka lissafi ba, kuma har shi sai ka ga yana damuwa da rashin auren ‘yar uwarsa, duk da kuwa ya san ba wani bambanci ba ne tsakaninsu na shekaru.

Ban ce ku yi ta zama a gida saboda wasu dalilai na son zuciyarku ba, ban ce kuma ku yi gaggawa saboda ƙauracewa maganganun mutane ba, A’a ina so ne mu fahimci cewar, shi jinkirin aure ga mace da namiji duk hukuncin ubangiji ne, yawan takurawar mutane ko ‘yan gida da iyaye ba ya kawo miji ko mata,  sai ma dai ya haifar da damuwa a zuciyar wanda a ke wa ɗin, wanda za ya iya zama kowane irin sanadi ga rayuwarsa.

Hausawa yawanci muna da wannan ra’ayin da “mentality” na jin cewar mace tana fara tasawa ta yi sauri ta kawo miji a yi mata aure, wanda a yanzu ko ƙwaƙƙwaran bincike a kan irin mijin da ta kawo ba a yi,  saboda ƙagare ake a rabu da ita. Har mu kanmu matan muna jin lallai hakan shi ya kamace mu, dan haka bama nutsuwa mu duba wa ya dace da mu, da yanayin tarbiyya da halayyar sa, kawai kowa ya faɗo mana sai muyi sauri mu riƙe, don kar ya tafi a fara mana gori. Idan kuwa muka zamo  cikin irin ‘yan matan da ba sa tallata samarinsu, ko ba su cika sakin fuska ga waɗanda ba su dace ba, sai a maida mu ‘yan girman kai, masu ji ji da kai, ko mun raina arziƙin mutane. Idan an samu masu sauƙi su ne masu ganin baƙin jini gare mu shiyasa.

Meyasa duk irin waɗannan maganganun a iya mata kaɗai suke tsayawa? Meyasa ba a ganin namijin daya jima bai yi aure ba a yadda ake kallon mu ( mata )? Meyasa ake kyara da hantarar mata a kan hakan, ba tare da duban meye maƙasudin hakan ba, shin laifinta ne ko daga Ubangiji ne? Meyasa hatta a wuraren da muke jin nan ya kamata mu samu sauƙi, idan aka zo maganar jinkirin aure ba wani sauki ko dagi da muke samu? Abin mamakin hatta iyaye sai su riƙa kyara da faɗin baƙaƙen maganganu a kan ‘yar da suka haifa ta cikinsu dan ta jima ba ta yi aure ba.

In ban da gida ban da family da duk sauran dangi a ina ne mace za ta ji sakewa da jin cewa e nima ina da gata. Ku ne ( family) kaɗai fatanta, ta yadda take jin ko duk duniya za ta guje ta a kan rashin aure ku bai kamata ku bi bayan hakan ba, kun san ta tun kafin ta mallaki hankalinta. Amma abin baƙin ciki sai ya zama hatta a gida cikin fargaba take rayuwa, ba kwa tsoron abin da ka iya samun rayuwarta idan kuka  cika takura mata a kan abin da ba ta da iko a kai.

Haihuwa, Aure da Mutuwa na cikin abubuwan da bawa bai da iko a kan su sai yadda wanda ya halicce shi ya yi da shi, mu riƙa kauda kai da rage yawan magana a kan irin waɗannan “issues” ɗin, masu wannan jarabawar suma suna fatan rabuwa da ita.

Allah ya sa jinkirin aure ga duk wata mace ko namiji  ya zama alkhairi ne gare su,  Allah ya bamu ikon cinye dukkan jarabawar da ya jarabce mu da ita 🙏🏽.

               ✍🏽 Zarah A Zamsarf ❤️✨

TSOKACI

Ba shakka marubuciyar ta taɓa inda yake yi wa mata da iyayen da suke da ƴaƴa mata da yawa ƙaiƙayi. A irin wannan zamanin da muke barin garuruwanmu mu koma birane da zama, abu ne mawuyaci mu san asalin mutum da danginsa da inda suka ta so. Iyaye da dama sun sha ba da aure su zo su yi danasani, saboda ba su yi bincike ba ko kuma sun yi binciken amma ba su samu gaskiyar lamari ba.

Wannan matsalar ta fara ne tun daga lokacin da muka saki tsarin addini muka rungumi na maguzawan Indiya da turawan yamma. Abun da musulunci ya hore mu da shi, idan an ga wacce ake so a yi bincike, in an ga ba wata matsala sai a tunkari iyayenta, su kuma iyayen su ba da dama a gana da ita don samun amincewarta, su yi na su binciken a kan dacewar saurayin, in komai ya yi shikenan sai a sa rana a yi aure ba tare da wani ɓata lokaci ba. Malam Abu  Abdullahi Assalafi duk ya tattauna wannan a littafin “Zuwa ga sabuwar budurwa a gidan musulmi na biyu”.

Ɓangare na biyu da ta yi magana a kai, wanda shi ne ma asalin jigon rubutun shi ne halin ƙaƙa-niƙayin da ake jefe ƴan matan a dalin tsangwamarsu da ake yi, wasu hakan ya tursasa su ga faɗawa cikin matsi da damuwa, wasu kuma don gudun faɗawa damuwar su je su yi zaɓen tumun dare. Mutane suna wasa da lamarin tsangwama, wasu ma suna musun cutuka irin na damuwa da fargaba, damuwa da fargaba da zullumi suna ɗaya daga cikin abubuwan da suke saurin karya garkuwar jiki, su raunata wasu muhimman gaɓoɓi da tsaruka na jiki, duk masana sun tabbatar da wannan.

Ba kowa ke yarda da binciken masana ba a wannan babin, hadisi ya tabbata daga Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda, idan an yi mutuwa takan sa a dafa talbina a aika gidan rasuwar, ta ce haka Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi yake yi, kuma ya ce talbina tana kwantar da hankali, tana yaye damuwa. Da wannan da sauraran dalilai malaman musulunci masu bincike kan lafiyar ƙwaƙwalwa suke kafa hujjar cewa lallai akwai damuwa kuma tana iya zama ciwo. (Za ku iya bibiyar shafin Yaqeen.org don karanta wasu rubuce-rubucensu kan wannan).

Abu na ƙarshe shi ne, ko shakka babu bai dace a bar mata da maza su daɗe ba aure ba, duk wanda ya kai munzalin aure mace ko namiji hakkin iyayensa ne su aurar da shi in suna da hali. Akwai kuma hikima a ƙarƙashin wannan, wanda iyayensa suka aurar da shi ba zai iya yanke hukunci kan aurensa ba tare da ya tuntuɓe su ba matuƙar yana da lafiyayyen hankali, wanda ya yi fama ya yi ƙuru ya yi komai da kansa ba ka isa ka ce masa komai ba, wataƙila ma sai dai ka ji labari musamman in jahilci da rashin tarbiyya sun ƙulla abota. Ke nan dai iyayen da ke tsangwamar ƴaƴansu kan rashin aure kamar suna daɓa wa cikinsu wuƙa ne, ku sama mata mijin da ya dace da ita mana kawai ku huta, in kuna tsoron za ta bijire sai ku sa ido duk wanda ya zo kafin a shaƙu a yi bincike a kansa, in ya dace a ce ya fito, in bai dace ba a haska mata yadda za ta fahimta. Sai kuma a miƙa lamari ga Allah.

Tare da wannan bayanin, mu sani cewa komai akwai alƙawarin Allah a kansa, yin aure da wuri jarrabawa ce, rashin aure da wurinma haka, kuma kowa Allah yana gwada shi ne ya ga ko zai iya cin jarrabawar da ya yi masa.

Ahmad Sani.