Daga cikin taimakon da Allah ya min shi ne ban jima a ƙasa ba bayan kammala karatuna na kama aiki (Allah abun godiya). Amma tun kafin lokacin ina lura da waɗanda suka riga mu kammalawa da kuma irin halin da suke shiga a wannan tsakanin, don haka na ɗan ɗauki lokaci ina bincike a kai tare da shiryawa rayuwar da zan shiga.
Za ka ga mutum ko na kati ya rasa, balle na siyan sabulun wanki da na wanka, ga shi saurayi mai ƴan mata da yawa, ya na son yin ƙwalisa, kuma ya na son kiransu a waya. Waɗannan abubuwan su kan jefa da yawa daga cikin masu kwalaye a hannunsu cikin zullumi.
A wannan rubutun zan kawo kaɗan daga cikin dalilan da ke tsananta rayuwar bayan karatu, watakila waɗanda ke cikin halin za su gane inda matsalarsu take su samu mafita, waɗanda kuma ba su kai lokacin ba za su yi ƙoƙarin tunkarar abun cikin shiri.
Rashin Tabbas
A lokacin da muke makaranta muna ganin cewa a takure muke sosai, mu ne fita sassafe ɗaukar darasi, mu ne dafawa kanmu abinci da kanmu, mu ne kaza mu ne kaza, don haka mutane da dama daga sun gama jarrabawar ƙarshe za ka ga suna ta murna (na kan fassara wannan murna a matsayin murnar rabuwa da alaƙaƙai a maimakon ta cimma wani buri).
Sai dai abun da yawancin mutane suka gaza fahimta shi ne, wannan rayuwa ta makaranta ta ba mu tsarin da mu ke da tabbas a kai. Duk ɗalibi ya tashi da safe ya san me ke gabansa, ya je ya ɗauki darasi, ya yi bita in ya dawo, ya zana jarabawa. Amma wanda ya gama makaranta zai tashi ya rasa ina zai sa kansa. In kallo ne damuwarsa wataƙila ya yi har ya gaji, in zaman bakin hanya ne, in wasanni ne, duk dai ko ma mene, ya ishe shi tun ba a je ko’ina ba.
Rashin tabbas ba iya gundura yake sa wa ba, mutum ya kan shiga fargaba da zullumin rashin sanin mataki na gaba, shin aiki zai jira?, sana’a zai kama? Wacce irin sana’a? wa zai ba shi jari? (Ga wanda ya san kashe kudi ya saba da shi ba nema ba) yaushe zai yi aure? Babban aiki zai samu ko ƙarami?
Ɗaukar Nauyin Kai
Duk da na buɗe rubutun da magana akan rashin tabbas, akwai tabbas guda ɗaya da duk wanda ya kammala makaranta yake da shi, ɗaukar nauyin kansa, lokacin da yake makaranta ba lalle ya damu da batun ɗaukar nauyin kansa ba, domin ko da iyayensa ba sa ɗaukar nauyinsa, za ka samu yana samun kudade ta wasu wuraren, wasu ma su kan yi sa’a su yi dacen abokai waɗanda za su ɗauki nauyin ci da su.
Lokacin da mutum yake yaro, wataƙila ya saba komai a gida ne ake yanke masa me zai yi, ko kuma akan ba shi shawarar me yakamata, yanzu kuma da girma ya zo masa, zai gane cewa lokaci ya yi da shi ma zai dinga yanke shawara da kansa, tun daga nan ɗaukar nauyin kai yake farawa.
Bayan yanke shawara sauran ɗawainiya ta kuɗi musamman in mai son ƙwalisa ne ta hau kansa, ko ya tashi ya nema, ko ya fara yawon bin yan siyasa, ko dogon hannu, ko ya shiga sana’ar zama a zagi mutane a ce ba a taimako.
Rashin Samun Aikin Yi
Yawanci ana shiga makaranta da burin a gama a samu aikin yi, duk da wasu suna ganin don ilimin kaɗai suke shiga (amma fa in da za a daina ba da shaidar kammalawa yan kaɗan ne za su iya zama a aji tsawon shekara 20).
Wannan tunanin shiga makaranta a gama a samu aiki a sayi gida da babbar mota ya sa da yawa ba mu damu da koyon sana’a ba. Wasu kuwa rashin lokaci ne da buƙatar tattara hankali wuri guda ya sa ba sa samun lokacin koyon sana’ar. Ko ma dai a wanne dalili ne rashin samun abun yi da wuri bayan an gama makaranta yana daga cikin abubuwan da ke tsananta rayuwa.
Shi wanda ya yi karatu, ko da karatun bai sa shi girman kai ba, yana kammalawa ne bayan ya zama babba, yana da buƙatu, ga shi ya saba kashe kuɗi, sana’a kuwa ta na buƙatar matse bakin aljihu, don haka zai zama dole bai da wani zabi sai na jiran ya samu aiki.
Rayuwa a cikin al’umma
Yawancin yara ƴan makaranta ba sa sanin wanne hali al’umma ke ciki sai bayan sun gama makaranta. Iya al’ummar da su ke makaranta da su kaɗai ake gogayya, bayan haka akwai dokoki da ƙa’idoji.
Fitowar mutum cikin babbar al’umma kan zama masa matsala domin yadda ya ɗauki rayuwa ta sha bamban da yadda take a zahiri. Zai ga abubuwan ƙi, haka kawai wani zai sa masa ido, haka kawai za a dinga shigar ma sa hanci da duƙunƙune.
A wannan lokacin abokan mutum ba sa kusa balle ya je musu yawo, kowa ya na fafutukar inda zai sa gaba a wannan mataki na rayuwa. Daga nan sai mutum ya dinga yawan samun kansa a kaɗaici da rashin madafa.
A makaranta mun saba sai an ba mu darasi kafin a jarraba mu, a rayuwa kuwa jarabawar ke fara zuwa, wanda ya ɗauki darasin ya huta, wanda bai ɗauka ba kuwa sai abun da hali ya yi.
Waɗannan abubuwan da ma wasu da ban ambata ba suna daga cikin manyan dalilan da ke sa rayuwa ta yi tsanani ga wasu bayan sun gama karatu. Ƙwarai, ba kowa ne dukka waɗannan ke samunsa ba, tunda wasu dama su suka ɗauki nauyin kansu, kuma sun saba komai nasu su suke yanke wa kansu, wasu kuma iyayensu sun tara, kuɗi ba ya zama musu matsala.
Mafita ma fi sauƙi a ganina shi ne wanda ke shirin gama makaranta ya manta da duk gatan da yake da shi, ya yarda cewa ya zo gaɓar da zai fara ɗaukar nauyin kansa, yadda da wannan gaskiyar zai sa ya manta da duk wani uzuri (ba a ba ni jari ba, ban samu aikin yi ba, ƴan siyasa sun lalata ƙasa, ban san kowa ba, dss), kada ya jira dole ta sa shi tashi tsaye, ya tashi tsaye tun da daɗin rai.
Duk da na samu aiki da wuri, kafin samun aikin saboda sanin wannan gaskiyar na fara koyon sana’ar hannu, bayan koyarwa da nake, ina gab da shiga kasuwa gadan-gadan Allah ya kawo. Abokina da ba aiki ne a gabansa ba kuwa NYSC ɗin ma bai tafi a wannan shekarar ba, don yana da abubuwan da suka fi ta muhimmanci saboda ya gane rayuwarsa nauyinsa ce tun da daɗewa.
Daga ƙarshe nake kira ga waɗanda ke cikin matsi yanzu da kar su ɗauka su kaɗai ne, kada kuma su ɗauka karatunsu ɓata lokaci ne, kowa da rabonsa, kada su fara ganin laifin mutane da ƙin taimakon su, wataƙila wani yana nan ya na jira ka fara wani abu don ya samu sukunin taimaka maka, a rage jiran gawo ya faɗo yadda shanu ke yi, a hau bishiyar a tsinko.
Sai mun ji naku ra’ayoyin a sashin tsokaci.
Ni iya Abun da zan iya cewa shi ne ya kamata iyaye su kasance a gaba gaba wajen nunawa yaransu yadda za su koyi sana’ar hannun ko kuma kasuwanci, mafi akasari rashin musu hakan Yana taka muhimmiyar rayawa wajen kawo nakasu da shiga halin qakanikayi. Sannan kuma ga Wanda suke da family business su yi kokari su na zuwa hakan shi zai Basu damar yin tunanin yadda za su inganta sana’ar sa suka tashi suka ga anyi agidansu
Gaskiya ne, wannan shawara ce mai matuƙar kyau da yakamata iyaye su yi aiki da ita.
Shiyasa Ni nake yawan faɗi sau dayawa ni’ima ce babba ka taso gidan Ku baku tara abin duniya ba, saboda hakan zai taimaka maka wurin tashi tsaye kayi aiki tuƙuri domin gina rayuwarka don dama gidan Ku babu abin duniya.
Wannan zai sa koda ka girma ƙalubale basu cika damun kaba don dama tun farka gwagwarmaya kawai ka sani.
Ni ina jami’a kuma ina da sana’a na wlh ba ƙaramin daɗin rayuwata nake jiba, haka nan burgeni wasu cikin abokan karatun mu kawai nake saboda buƙatu na kaso sittin nafi ƙarfin su.
Allah ya sayar damu.
Gaskiya ne, barakallah, amin amin.
Assalamu alaikum. Akwai abun da ke da mun yaran talakawa wani lokacin, shi ne hangen na gaba da su, wani yana da ilimi sosai amma daga lokacin da wani yaron mai kuɗi ya shiga rayuwarsa, sai ya fara claiming shi ma big boy. Ilimin nasa ya fara samun tangarɗa da sana’arsa, saboda kar dai a ce shi ɗan talakawa ne baya aikin gwamnati sai dai sana’a daga nan ne zai fara saka wasa a cikin al’amurran sa. Saboda kawai wannan ɗan mai kuɗin yana ba shi kuɗi; kuma shi yana tsoron ya ci gaba da rayuwa da shi a yadda yake. Akwai wani abokinmu mai ilimi ne sosai a cikin ajin su akwai wani yaron mai kuɗi yaron yana son shi sosai wannan ya sa ya fara wasa ya zo baya mai da hankali a karatunsa, tunda dama shi ɗan mai kuɗin ba karatun bane a gabansa neman abokin mutuwa yake yi. Daga karshe sai da abokin nan namu ya fara shaye-shaye.
Yaron mai kuɗin ya lalata masa rayuwarsa, mu kuma da ba mu da kuɗi ya yi watsi da mu. Har muka shiga jami’a shi ko jami’ar ma bai je ba daga ƙarshe yaron ma ya yi watsi da shi suka rabu ba wan ba ƙanin.
Waalaikumussalam, Allah sarki. Wannan babban ƙalubale ne ga maras shi, Allah ya kare mu.