Ya zo a tarihin sahabbai cewa, Annabi tsira da aminci su tabbata gare shi ya haɗa ƴan’uwantaka tsakanin mutanen madina da muhajirai lokacin da aka yi hijira. Mutanen Madinan sun kasance duk wanda aka haɗa su da shi su kan raba dukiyarsu da gidajensu wasu ma har da matansu su ba wa yan’uwan nasu.

A cikin waɗannan sahabbai akwai Abdurrahman bin Auf, lokacin da ɗan’uwansa na madina ya masa tayin irin wannan tagomashin sai ya sanya masa albarka a dukiyarsa da ahalinsa, amma bai karɓa ba, sai ma ya buƙaci da wannan sahabi ya nuna masainda kasuwa take.

Ance ba shi da ko sule nasa ya shiga kasuwar, ya fara kasuwanci, amma kafin ya bar duniya sai da ya zama babu mai dukiya kamarsa a wannan tsakanin (dama tsohon ɗan kasuwa ne da ya sadaukar da komai na sa don ya tsira da addininsa, Allahu Akbar!).

Ba iya Abdurahman bin Auf ba, su sayyadina Abubakar, Usman, Nana khadija, duk suna daga cikin misalan mutanen da su ka tafiyar da tulin arziƙinsu wurin ɗaukaka Addinin Allah. Abun da da yawa daga cikin mutane ma ba su sani ba shi ne, cikin sahabbai 10 da aka yi wa bushara da Aljannah a lokaci guda ance bakwai daga cikinsu hamshaƙan masu kuɗi ne.

Sanannen abu ne cewa Annabin Allah yana neman tsari daga talauci, kuma ya koya mana mu nemi tsari daga talaucin. Shi talauci ya kan zo a matsayin jarrabawa ne ba a matsayin abun ado ba, wanda aka jarrabe shi ya yi haƙuri shi ne zai samu lada. Wanda dama zaune ya ke haka kurum bai kamata ya yi kuka ba, domin bai nema ba balle ya yi ƙorafin ya rasa.

Na taɓa halartar wani taron yaƙi da talauci a Kano, wanda wata ƙungiya ta su Malam Ibrahim Khalil ta shirya wacce ban kiyaye sunanta ba, ɗaya daga cikin mutanen da suka gabatar da takarda a wannan taron ya kawo wasu manufofin da suka zaburar da sahabbai wajen neman arziƙi:

  •     Godewa Allah da ya hore abun da za a nema ɗin
  •     Samun ƴanci
  •     Barwa ƴaƴa gado kar su yi bara bayan ba su
  •     Nuna Godiya ga Allah ta hanyar gusarwa bayinsa damuwoyi

A wasu lokuta mukan samu kanmu cikin ɗaukar cewa neman arziƙi haɗama ne, ko son duniya, sai dai wannan tunanin yana hana mu rawar gaban hantsi. Amma in muka duba cikin abubuwan da mai takardar ya lissafo ɗin nan (a sama), ko dan ƴanci ma kaɗai za ka so ka nemi na kanka. Za ka ji a tarihi Annabawa duk da sana’o’insu, ba zaune suke haka ba.

Ba a san Hausawa da son ci a huce ba sai bayan da muka waye muka rungumi karatun boko, daga nan muka ɗauka kakarmu ta yanke saƙa, muka watsar da sana’o’inmu na gado a maimakon mu inganta su, wannan tunanin shi ya kai mu ya baro, kuma ya na ci gaba da kai mu inda ba ma so ɗin. Ko da ma ba ma son mu ci gaba da yinsu ai zamani ya zo mana da hanyoyin neman kuɗi da dama, wasu suna nema da wayoyin hannunsu ma ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta ko shafukan yanar gizo (digital marketing) da duk mai buƙata zai iya zama ya koya.

Ba waɗanda suka fi saurin rasa ƴancinsu a dalilin rashin arziƙi irin masu ilimi, saboda in buƙatu suka yi yawa, kuma suka rasa yadda za su yi, in ba Allah ne ya kare ba, sai su kauce hanya. Ba fa a iya zamanin ne kaɗai ba, fiye da shekara 800 baya malam Ibn Aljawzi ya ba wa malamai shawara kan yadda za su yi da tattalin arziƙinsu a dalilin wannan matsalar.

Kenan babu wani dalili da zai sa don kana musulmi da sunan gudun duniya ka dinga ƙasƙanta kanka (ya sha bamban da ƙanƙan da kai). Na taɓa karanta wani hadisi muttafaƙun alaihi, ba lalle na iya tuna kalmomin cikin hadisin yadda suka zo ba, amma ma’anarsa shi ne in kuka haɗu da wanda ba muslmi ba a lungu mai matsatsi, kada ka kauce masa, ka kara maƙure shi ma a jikin bango in da hali.

Duk wannan na nuna mana irin izzar da musulmai suke da ita, ko shakka babu bayan imani da salati, har da jarumta/jihadi da kuma yadda suka nemi arziƙi kuma suka yi amfani da shi wajen ɗaukaka Addinin Allah.

Da yawanmu mun san hadisin “masu dukiya sun tafi da lada” amma a maimakon mu ma mu mayar da hankali kan neman namu sai a ɓuge da zaginsu ko roƙonsu ko musu mummunan fata.

Tara dukiya ba shi ne arziƙi ba, wanda ba ya cire haƙƙin Allah a cikin dukiyarsa to da sauransa, kamar yadda kuma yawan nema ba shi yake nuna haɗama ba, kowa rabonsa yake ci, kuma kowa da manufarsa da burukansa na rayuwa. Idan sana’a ɗaya ta gaza wajen biya maka buƙatu ko taimakonka wajen cimma manufofinka sai ka ƙara wata kana mai neman taimakon Allah, idan sun zarge ka da haɗama ko rashin godiya ka jira lokacin da za su zo neman taimakonka.

Rufe wannan rubutun a wannan gaɓa ba zai ba da fa’ida cikakkiya ba, ku ɗan mini haƙuri na ƙara wasu yan saɗaru ya ku masu karatu.

Musulunci ya zo ne domin ya ba mu kariya daga abubuwan da za su cutar da mu ya kuma matsar da mu kusa da waɗanda za su amfane mu. A saboda haka ne manzon Allah mai tsira da aminci ya faɗa a wani hadisi cewa:

“Bawan dinare ya taɓe…”

Wannan hadisin ya nuna ma na cewa zama bawan kuɗi shi ne matsalar ba wai neman arziƙin ba. Kenan duk wata hanya ta halal da za ta kai ka ga samun arziƙi ba lefi dan ka bita dan kare mutuncinka. Kawai abun da za ka tsare shi ne manufarka ta neman arziƙin, da kiyaye dokokin mamallakinka kai da arziƙin wurin nema da kuma tasarrufi da shi.

Jikinka na da haƙƙi a kanka, iyalinka na da haƙƙi a kanka, ubangiji na da haƙƙi a kanka, don haka kowanne mai haƙƙi ka ba shi haƙƙinsa (hadisi ne). Kada neman lahira ya hana ka morar duniya, kamar yadda kuma asara ce babba neman kuɗi ya rufe ma ido daga jin ɗaɗin ita kanta duniyar, balle aje ga batun lahira.

Ka nemi duniya kamar ba za ka mutu gobe ba, ka nemi lahira kamar gobe za ka mutu, haka Mallam Bahaushe ya ce da ni a lokacin da yake ƙoƙarin fassara min wani bayani kan gudun duniya (in ka kai yamma kada ka ɗauka za ka wayi gari). Tsayawa a tsakanin tunanunnuka guda biyun shi ne kaɗai abun da zai saita mana rayuwa.

Akwai bayin Allahn da sun sadaukar da komai nasu don yi wa musulunci hidimar da a yanzu muke morarta, idan imaninka bai kai na su ba, gaskiya to ka haɗa dukka biyun zai fi maka rufin asiri da zaman lafiya, musamman in kana yi da niyyar bautar Allah.

Abu ma fi ban tsaro a wannan babin shi ne hadisin Amr bn Auf, da Ma’aiki mai tsira da aminci yake bayyana cewa ba talauci yake ji mana tsoro ba, babban abun tsoron shi ne a buɗe mana duniya da arziƙinta kamar yadda aka buɗewa waɗanda su ka gabace mu, sai mu yi ta gasa da rigegeniya a cikinta kamar yadda su ka yi, sai ta halaka mu kamar yadda ta halaka su.

“Zafin nema ba ya kawo samu” gaskiya ne, a matsayinka na mutum ƙuduri da aiki shi ne naka, sakamakon na mai dukka ne, sai yadda ya ga dama. Wannan kuma ba ya nufin ka ƙi nema, yana nufin kar ka ɗauka wayonka ne zai baka, domin babu wanda ya taɓa wuce arziƙinsa kamar yadda kuma babu wanda yasan inda arziƙinsa yake. Haka nan kuma koyaushe mu tuna mai Albarka ya fi mai yawa, kuma dai ma wadata ita ce wadatar zuci.

 

Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi yana faɗa a wani hadisin cewa:

“Wanda ya mayar da lahira ita ce damuwarsa, Allah zai gyara masa lamurransa, ya sanya masa arziƙinsa a zuciyarsa, kuma duniya za ta zo masa duk da yadda yake gudunta. Wanda kuma ya mayar da duniya damuwarsa, Allah zai wargaza lamurransa, ya sanya masa talaucinsa a gaban idonsa, kuma babu abun da zai samu na duniya sai abun da aka rubuta masa”.