Lokacin da ina makarantar sakandare masu ƙoƙari iri biyu ne, waɗanda ana yi a aji suke ganewa in sun dawo kuma su yi ta bita, da waɗanda ba sa iya ganewa tun a ajin amma akwai su da nacin karatu.

Da na shiga Jami’a ma dai haka na taras, har ma a nan na san kalmomin “guru by naci” da “guru gifted” wanda suke nufin wanda naci ne ya sa yake ganewa da kuma wanda an haife shi ne da wata baiwa. Wannan abun ya sa na ɗauka cewa a komai na rayuwa akwai waɗanda kaifin basirarsu ne yake taka rawa wajen kaiwa gaci, yayin da wasu kuma tsabaragen aiki tuƙuru ne.

Sai dai daga baya wata gaskiya da na  fahimta wacce kuma ta ɓuya ga mutane da dama ita ce, naci ya fi kaifin basira wajen cimma nasara, kuma shi ne abun da na ke so na bayyana muku a wannan rubutun.

Bari in fara da yanko wata magana daga Calvin Coolidge, inda yake cewa “Babu wani abu a duniyar nan da zai maye gurbin naci. Basira ba za ta iya ba; babu abun da ya fi mutane masu basira da ba su ci nasara ba zama ruwan dare. Baiwa ba za ta iya ba; “baiwa marar amfanarwa” kusan karin magana ne. Ilimi ba zai iya ba; duniya cike take da masu ilimi wofantattu. Dagewa da azama kaɗai ke da iko. Taken “ci-gaba-dai” ya warware kuma a koyaushe zai warware matsalolin jinsin ɗan’adam.”

A wani bincike da ta gudanar, Angela Dukworth ta bibiyi sirrin cin nasarar mutane a fannoni da dama na rayuwa, kama daga kan aikin soja, kasuwanci, ilimi da sauransu, a karshe abun da ta gano shi ne basira ta yi kaɗan ta kai mutum wannan matakin da masu nasarar suka kai, sai ya zama yana son abun, kuma ya yi aiki tuƙuru a kansa, irin aikin da zai sa shi ya ƙware, ya kuma jure. Ta kira wannan abun da sunan“Grit” a cikin littafinta mai wannan sunan.

Mutane da dama in da za a tare su a tambaye su tsakanin aiki tuƙuru da basira wanne ne yafi, za su ce aiki tukuru. Amma kamar yadda Angela ta bayyana, in da za a ga wani da ya yi fice a wani fanni sai a dinga masa kallon ɗan baiwa ne kawai, ba wani naci da ya yi, kenan ba har zuci aka aminta da cewa naci ya fi basira ba.

Na taɓa karanta wani labari na Michael Jackson shahararren mawakin nan, a ciki an bayyana cewa yana shafe awanni takwas kullum yana atisayen rawa da waƙa. Ka ga mu a wajenmu za mu ce masa ɗan baiwa ne shi, tunda ba mu san faɗin tashin da yake yi ba.

Ba ana so ace basira ba ta da tasiri ba ne, ƙwarai tana da shi, amma duk basirar da ba ta samu naci ya mara mata baya ba, ba ta yi wa mai ita amfani. Wasu suna ganin ma takan zama tsinuwa ga mai ita, domin ba za ta bar shi ya san muhimmancin aiki tuƙuru ba, balle ya dage.

Akwai wani binciken ma na masana da yake nuna duk wani da ya ke son cin nasara a rayuwa a kowanne irin fanni, yana buƙatar aiki tukuru na tsawon awanni dubu goma (10,000 hours), mafi ƙaranci shekara 7. Malcoms Gladwells ya kawo misalai na mutane mabambanta a cikin littafinsa“Outliers” don ya bayyana irin aiki tuƙurun da suka yi, da yadda suka nacewa abu guda tun yarintarsu, har sai da ta kai duniya ta ji sunansu kafin su haura shekara 30.

A gaskiyar magna basira ana kambabata fiye da misali, ana ganin ƴan baiwa su suke iya yin abu kaza, ko su ne abu kaza yake musu sauƙi, ko sune suke iya kai wa wani mataki na rayuwa. Amma kai ma mai karatu ba mamaki ba za ka rasa taɓa sanin wani da yake da basira ba tun yana yaro, amma ba ta masa amfani a yanzu da ya girma. Hakan kuwa yana da nasaba da rashin samun jajircewa daga gare shi, ko daga masu tarbiyyarsa ko masu ba shi horo.

Babu wani abu da nacin mutum ba zai iya kai shi gare shi ba, ko ba jima ko ba daɗe, sai dai in ba ya samun darasi daga faɗuwarsa ko kuma an rubuta cewa wannan abun ba rabosa ba ne. Bahaushe yace sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba. Yau da gobe ba ta bar komai ba. Duk abun da aka sa a gaba za a iya ganin haske matuƙar an jure an nace.

Malam mai Ta’alimu ya kawo abubuwa da dama da suke taimakon mutum wajen samun ilimi a cikin littafinsa. Shi kansa bai taƙaita a kan hazaƙa da ƙoƙari ba, sai da ya ƙara da naci da kuma daɗewa ana yi. A wurare da dama ya nuna muhimmancin naci da yi kullum, in ban manta ba har babi ya buɗe a kan wannan.

Aikin hannu kake kamar ɗinki, kafinta, zane, ƙira, kanikanci, kana buƙatar naci da yi yau da gobe. Marubuci ne kai, kana buƙatar naci, malami ne kai, ɗan makaranta ne kai, soja ne kai, ɗan kasuwa ne kai, babu wani fanni na rayuwa da naci da juriya suka bari. Wasan kwaikwayo, waƙa, wasan tamola da ma sauran wasanni, tsere, iyo, duk babu wanda iya baiwarsa take sa shi ya yi fice a fannin. Dole sai ya haɗa da naci da juriya da aiki tuƙuru.

Duk yadda mutum ya kai ga baiwa, yana zuwa wata gaɓa da baiwar tasa ba za ta matsar da shi ko’ina ba, matuƙar bai mata shimfiɗar aiki tuƙuru da naci ba. Duk inda mutum ya kai ga rashin basira, naci da aiki tuƙuru za su kai shi inda bai taɓa tsammani ba, domin zai zo wata gaɓa da wannan abun zai zama masa kamar shan ruwa, ko daga bacci ya tashi ba ya shakkar komai. Wannan shi ne yaro ɓata hankalin dare ka yi suna. Ina fatan mai karatu ya gamsu da cewa naci yana kan gaba a komai, in ba ka gamsu ba kuwa zan so na ji naka ra’ayin kan wannan batu.